• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Babu komai a Kannywood yanzu, shi ya sa kowa ya koma siyasa – Salisu Officer

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
December 5, 2022
in Labarai
0
Alhaji Salisu Muhammad Officer

Alhaji Salisu Muhammad Officer

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN bayyana cewa yanzu masana’antar shirya finafinai ta Kannywood ta koma babu komai cikin ta sai roƙo da tumasanci, wanda hakan ya sa kusan kowa ɗan cikin ta ya koma harkar siyasa.

Wannan kalamin ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin shugabannin masana’antar, Alhaji Salisu Muhammad Officer, a lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim.

Officer ya ce a yanzu da halin da masana’antar ta shiga yanayi ne da sai dai du’a’i.

Babban furodusan, wanda mazaunin Kano ne, ya ce: “Ita masana’antar Kannywood ta na nan a matsayin ta na masana’anta tun daga lokacin da aka kafa ta, amma idan ka duba yadda kasuwancin masana’antar ya ke da kuma yadda ake tafiyar da ita, to a yanzu za a iya cewa babu komai, saboda a yanzu idan ka duba ayyukan da ake fita wasu ‘yan kaɗan ne da ba su wuce guda biyar ko shida ba su ne waɗanda ake ɗorawa a YouTube da wanda ake haskawa a gidan talbijin, saɓanin yadda ake yi a baya lokacin da kasuwancin ya na tafiya da za ka furodusa ɗaya ya buga fim sama da dubu ɗari ya shigar da shi kasuwa.

“Sai ya zama abin yanzu ya koma YouTube da kuma gidan talbijin, to su kuma ba kamar yadda za ka yi ka kai kasuwa ka sayar ba.

“Sannan sai ya zama a yanzu ana yin abin ne babu ilimi, babu ƙwarewa.

“Kuma a yanzu idan ka ce ma sai ka yi fim ma, to su waye ‘yan masana’antar? Kowa ma yanzu ɗan fim ne, domin ga wasu yara can daga gidan iyayen su su na yin fim su ɗora a Facebook, Instagram, TikTok, kuma sun yi suna ba tare da sun shigo Kannywood ɗin ba, kuma duk abin da su ke yi ba ka isa ka ce ba fim ba ne, kuma ba za ka iya hana su ba, saboda ba su ce sun ‘yan Kannywood ba ne duk da fim su ke yi.

“Su kuma masu harkar fim ɗin, mun kasa samar wa kan mu mafita.”

Officer ya ƙara da cewa: “Su kuma shugabannin masana’antar sun ma kasa gane cewa a yanzu harkar fim ta mutu, babu ita, kawai wani ne ya zauna a ofis da sunan ‘shugaba’, wai ya na yi wa yara masu shiga harkar rajista, bayan babu ita!

“Kuma nawa ne da su ke yin fim ɗin da ba su san ma ana yin rajista ba, kawai a kan hanya aka haɗu da su aka saka su a fim? Kuma ba ka isa ka hana ba, saboda kowa harkar gaban sa ya ke yi, bai ma san ka ba a matsayin ‘shugaban masana’antar’, kawai kai ne ka zauna a ofis ka na jin kai shugaba ne!”

Da ya juya kan shiga harkar siyasa da ‘yan fim rankatakaf su ka yi kuwa, cewa ya yi: “To ai don babu abin da za a yi ne shi ya sa kowa ya shiga siyasar. Kuma sai zama a siyasar ma babu tsari, saboda an je an tare a waje guda.

“Duk da cewa ba laifi ba ne mutum ya yi ra’ayin da ya ke so, amma ya kamata ya zama mu na da manufar da za mu je wa duk wani ɗan siyasa mu sanar da shi a rubuce idan ya yi nasara ga abin da mu ke so a samar wa masana’antar finafinai ta Kannywood. To amma sai ya zama kowa buƙatar neman kuɗi ce ta kai shi, kuma kuɗin bai samu ba.

“Saboda haka, ya zama wajibi mu faɗa wa kan mu gaskiya cewa siyasar nan ta ɗan wani lokaci ce kuma za ta ƙare nan gaba kaɗan, don haka ko da za mu yi siyasar, to mu yi wadda za ta samar mana da cigaban masana’antar Kannywood bayan an gama zaɓe.”

Loading

Tags: KannywoodSalisu Muhammad Officershugabancisiyasasoshiyal midiyaZaɓen 2023
Previous Post

Jarumin Kannywood Adamsy Celebrity zai angwance da Ummakatty ran Asabar

Next Post

Sa’idu Isa Gwanja ya daidata wa masu harkar fassarar finafinan Indiya sahu

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Malam Sa'idu Isa Gwanja

Sa'idu Isa Gwanja ya daidata wa masu harkar fassarar finafinan Indiya sahu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!