MAWAƘIYAR nan ta Kannywood wadda ta yi fice a waƙoƙin siyasa, Ummi Kano, ta bayyana waƙa a matsayin wata babbar sana’a da ta yi mata komai a rayuwar ta, domin ta zama sanadiyyar samun arziƙin ta.
Ummu ta bayyana haka ne a lokacin da mujallar Fim ta tattauna da ita a kan yadda a ke damawa da ita a harkar waƙoƙin siyasa.
Mun fara da jin tarihin ta daga bakin ta, inda ta ce: “Ni ‘yar asalin garin Kano ce. A nan aka haife ni. A yanzu ina da shekaru 28.
“Na yi makarantar firamare ta Ja’oji kuma na fara sakandare ta Salanta, ban gama ba aka cire ni aka yi mani aure.”
Dangane da yadda aka yi ta shiga harkar waƙa, Ummi ta ce: “Ni da man tun ina ƙarama na fara sha’awar yin waƙa. To, bayan mun rabu da miji na ne, da na dawo, sai kuma na fara waƙar da ta yabon Annabi, wadda maigida na a harkar waƙa, Tijjani Gandu, shi ne ya ke rubuta mani.
“Daga baya dai na fara waƙoƙin soyayya, ina yin su sosai, har kuma na shiga waƙoƙin siyasa waɗanda a yanzu aka fi sani na da su.”

Da mu ka tambaye ta yawan waƙoƙin da ta yi, sai ta ce, “A gaskiya, waƙoƙin da na yi su na da yawa a na ɓangaren soyayya da na yabon Annabi da kuma na siyasa. Duk da cewa ban yi album ba, kawai dai ina yin waƙar ne, sai daga baya na zo ina sakawa a YouTube. Kuma ka ga waƙoƙin siyasa ba ajiyewa mu ke yi ba, idan mu ka yi wa mutum ne za mu kai masa. Shi ya sa ba zan iya sanin yawan waƙoƙin da na yi ba.”
Mawaƙiyar ta bayyana cewa ta samu nasarori a wannan sana’a.
“To gaskiya na samu nasarori sosai,” inji ta, “domin ita harkar waƙa babu abin da ba ta yi mani ba na rufin asiri, domin na samu alaƙa da mutane, na samu mota da sauran abubuwa na rufin asiri. Don haka ni a yanzu babu abin da zan ce da harkar waƙa sai godiya ga Allah. Kuma ina fatan Allah ya ƙara mana rufin asiri da ɗaukaka a harkar waƙoƙin da mu ke yi.”
Ummi ta yi kira ga mawaƙa da su haɗa kan su domin ta haka ne za a samu cigaban da ake buƙata.
Comments 1