• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar jarumar Kannywood Ladidi Fagge: Ban san ana yaɗa mugun labari game da ni a soshiyal midiya ba

by .
September 23, 2022
in Labarai
1
Hajiya Ladidi Fagge

Hajiya Ladidi Fagge

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jarumar masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, Hajiya Ladidi Fagge, ta bayyana cewa labarin da ake bazawa cewa ta rasu ba gaskiya ba ne.

An jima ana baza labari a soshiyal midiya cewa jarumar ba ta da lafiya, ta na kwance cikin wani mawuyacin hali, har ana haɗawa da wani hoto inda ta rame matuƙa.

Akwai ma masu cewa wai ta rasu.

Ganin yadda labarin ya yaɗu kamar wutar daji ya sa mujallar Fim a jiya Alhamis ta nemi jin ta bakin ta, inda ta ce ita ba ta ma san ana yaɗa wannan labarin ba saboda ba ta samu zama ba da har za ta hau intanet ta ga abin da ake rubutawa.

Dangane da ko ta yi rashin lafiya kuwa, Hajiya Ladidi ta faɗa wa wakilin mu a Kano cewa: “Tabbas, a baya na yi rashin lafiya, amma ba yanzu ba ne, tun a watannin baya ne. Kuma na samu sauƙi na ci gaba da harkoki na, don a yanzu ma da na ke magana da kai anjima kaɗan zan tafi aikin fim ɗin ‘Alaqa’ a unguwar Maidile.”

Ladidi Fagge ta ce tun a watannin baya ne ta yi rashin lafiya amma tuni ta wattsake ta ci gaba da harkokin ta

Ta ci gaba da cewa, “Ko a kwanakin baya gidan Rediyon Arewa sun kira su ka ce wai sun samu labarin ba ni da lafiya ina neman taimako na kuɗi da na addu’a. Sai na ce ni dai ban faɗa wa kowa ina neman taimako ba, amma dai idan wani ne ya ga dacewar hakan ya ce zai ba ni wani abu na taimako to hakan ba zai zama abin da zan ce ba na so ba; kuma maganar ina buƙatar a taya ni da addu’a, to ai ba sai mutum ya na kwance zai buƙaci addu’a ba. Ina buƙatar addu’a a wajen masoya na a yanzu da kuma kowane lokaci.”

Jarumar ta yi fatan alheri ga dukkan masoyan ta saboda damuwar da su ka nuna a game da labarin da su ka gani ana yaɗawa.

Loading

Tags: Alaqafake newsKannywoodKanolabaran ƙaryaLadidi Faggerashin lafiyaRediyon Arewasoshiyal midiya
Previous Post

Yanzu waƙa ce ke riƙe da Kannywood, ba fim ba – Darakta Aminu S. Bono

Next Post

Sana’ar waƙa ta yi mani komai, inji Ummi Kano

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Ummi Kano

Sana'ar waƙa ta yi mani komai, inji Ummi Kano

Comments 1

  1. Pingback: Ina Nan Raye ban mutu ba kuma Lafiyata Kalau – Mikiya.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!