WANI tarihi mai kyau da matuƙar muhimmanci ya na neman maimaita kan sa a Kano. Sarkin Kano na 32 a daular Hausawa, Muhammadu Kukuna Ɗan Alhaji, bayan ya zama Sarkin Kano, ya yi mulki shekara guda, sai Madawakin Kano na lokacin ya ƙulla maƙar- ƙashiyar cire shi daga sarauta, su ka naɗa Soyaki, shi kuma Kukuna ya yi gudun hijira zuwa ƙasar Zariya. Soyaki ya yi wata uku ya na sarauta sai manyan Kano su ka haɗu su ka yi shawara a kan sa. Gaba ɗayan manyan masu ƙarfin ikon su ka haɗu a ƙarƙashin Galadima Wari da Ɗan’iya Babba da Makama, su ka yi shawarar dawo da Sarkin Kano Muhammadu Kukuna gadon sarautar sa.
Wannan ya sa su ka ɗaura ɗamarar yaƙi da Sarkin Kano Soyaki, su ka fitar da shi daga Kano, Muhammadu Kukuna ya dawo karagar mulki, shi kuma Soyaki aka gina masa gida a Dukarawa inda ya rasu a can.
Wani abin al’ajabi da mamaki shi ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya ɗauko tarihin kakan sa, Muhammadu Sanusi na I, tare da gadon duk wani mataki da ya bi a loton sarautar sa a daular Fulani, ta fuskar sauke dukkan nauyin da ya rataya a kan Sarki da talakawan sa a ilimance da zamanance da sauran matakai na rayuwa.

Wani tarihi da zai ƙara maimaita kan sa shi ne a jerin sarakunan Hausawa ma Muhammadu Sanusi II ya ɗauko hanyar gadon Muhammadu Kukuna Ɗan Alhaji. Kamar yadda aka cire Kukuna ta hanyar maƙarƙashiya, shi ma haka ta faru ga Muhammadu Sanusi II, wanda aka cire shi daga sarauta kamar yadda aka yi wa Kukuna.
Haka kuma kamar yadda Kukuna ya samu mafaka a Zariya kafin ya dawo karagar mulkin sa, shi ma Sanusin a ƙasar Zariya ya ke karɓar gaisuwar mutanen sa da ya yi wa nisa, sannan kuma a ƙasar Zariya ya ke gabatar da sallar Idi.
Babban abin da zai ba ka mamaki shi ne kamar yadda masu faɗa a ji a Jihar Kano su ka ga cancantar dawowar Kukuna sarauta, haka ya ke a kan Muhammadu Sanusi. Shi ma mafi yawan masu faɗa a ji a Kano su na son su ga ranar da Sanusi zai dawo gadon sarautar sa. Hakika, wannan ba ƙaramin abin al’ajabi ba ne!
A sarauce, dukkan wanda ya zamto sarki ana duba ga sarakunan da su ka gabata a ga wa za a iya kwatanta shi da shi, ko ta fannin jarumta ko adalci ko talakawa da makamantan su. To, amma ga Khalifa Muhammadu Sanusi II shi jinkan al’amarin sa ya wuce dukkan yadda ake zato irin na kwatance, ya gama da ga shi a zahiri ya yi gado ga daular Fulani, wannan Hausawa ɓangaren ya kuma tsallaka ga daular gado inda ita ma ga shi zai ajiye muhimmin tarihin da ba a taɓa yin irin sa a tarihin ƙasar Hausa ba.
Haƙiƙa idan haka ta tabbata, to Sanusi ya zama abin kwatance ko da kuwa a Daular Larabawa, domin samun gwarzon sarki mai tagwayen tarihi irin wannan ya na da matuƙar wahala.
*Malam Rabiu Na’auwa marubuci ne mazaunin garin Daura, Jihar Katsina
I-mel: naauwa1@gmail.com