• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnati ba ta yarda wani ya yi harkar fim a Nijeriya ba tare da rajista ba – Umar Fage

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
June 22, 2023
in Labarai
0
Alhaji Umar G. Fage, Shugaban NFVCB shiyyar Arewa-maso-yamma

Alhaji Umar G. Fage, Shugaban NFVCB shiyyar Arewa-maso-yamma

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) ta shigo da tsarin wajabta yin rajista ga duk wani mai gudanar da harkar fim a duk in da ya ke a faɗin ƙasar nan. 

Shugaban hukumar mai kula da yankin Arewa-maso-yamma, Malam Umar G. Fage, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim a game da ƙoƙarin da su ke yi na gyara masana’antar fim a Nijeriya.

Tun da farko sai da ya fara da yin bayani kan yadda su ka yi nasara wajen yaƙi da fassarar finafinan Indiya da wasu daga cikin ‘yan kasuwar fim a Kano su ke yi, wanda a cewar sa hakan ya saɓa wa doka, don haka su ka ɗauki matakin dakatar da abin saboda haramtacciyar harka ce kuma har yanzu ta na nan a matsayin haramtacciya. 

Ya ce, “Tun a wancan lokacin mun yi rubutu kuma mun haɗa rahoto mun aika Abuja. A yanzu mu na jira mu samu sakamakon. Kuma duk da mutane kamar su na ganin abin ya yi tsauri, to ba haka ba ne, don akwai doka, sannan duk wani fim da za a nuna wa jama’a, to haƙƙi ne na Hukumar Tace Finafinai ta duba. To a cikin ƙa’idojin da za a duba na fassarar ko mayar da duk wani fim na waje akwai wata takarda wadda kai mai fassarar za ka mallaka kafin ka yi fassarar. To a kan wannan ƙa’idar mu ke.”

Dangane da sabon tsarin da su ka samar a yanzu kuwa, Malam Umar ya ce, “To duk da cewar ba sabo ba ne domin akwai shi a dokar Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa cewar duk wani da zai yi aiki na harkar fim to wajibi ne ya zama ya na da rajista da  wata ƙungiya, wato ‘guild’. Don haka ne a kwanakin baya mu ka yi zama da shugabannin ƙungiyar MOPPAN na ƙasa da ƙungiyar Arewa don tabbatar musu da saƙon da mu ka samu daga Abuja a kan cewa lallai akwai duba a ƙaramin sashi na 2 da kuma na 3 cewar duk wani wanda zai yi aiki sai ya na da rajista da wata ƙungiya, wato ‘guild’. Wannan kuma ya biyo bayan wata muhawara da ta taso bayan fitowar wani fim da aka yi a Legas.

“To, wasu abubuwa da mutane ba su sani ba shi ne an samu tsaiko wajen gabatar da shi wannan fim ɗin sakamakon ba a tace shi ba sun je su ka saki fim ɗin, saboda waɗanda su ka yi aikin fim ɗin ba su yi rajista da ƙungiyoyin su ba. Shi ya sa su ka ƙi kawo shi wannan hukumar ballantana har a sahale musu su sake shi. To wannan ya sa aka fitar da doka kuma ta fara aiki tun 22 ga Mayu na cewar duk wani da zai yi harkar fim – jarumi ne, darakta ne, mai ɗaukar hoto ne, da duk wani aiki da su ka shafi harkar fim – ya zama ya yi rajista da ƙungiyar sa. 

“Don haka kamar yadda na faɗa maka, da man ita dokar akwai ta. Don haka duk wanda zai yi fim dole ya zama ya na ɗaya daga cikin wata ƙungiya da ta ke da rajista da Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, don haka duk wanda ya yi gaban kan sa to doka ta tanaji hukunci a kan sa. Don haka ba ka da wani dalilin a yanzu don ganin ka iya daraktin ka je ka yi ba tare da ka na da rajista da ‘guild’ ba, don haka doka ce a sashi na 7 ƙaramin sashi na 2 da na 3. Don haka yin wannan rajista shi ne zai ba da damar samun tsafta a cikin harkar.

“Kuma ba wai mu na yin magana a kan Kano ko Kaduna ba, mu na magana ne a dukkan mataki na ƙasa. Don haka wannan dokar ta na yin aiki ne a jihohi 36 har da Abuja.”

Da mujallar Fim ta tambaye shi matsayin finafinan YouTube a hukumance, sai daraktan shiyyar ya ce: “Abin da ya kamata mutane su sani shi ne ita dokar Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa ta na iko ne a kan duk wani fim da za a nuna shi ga ‘yan Nijeriya, ya zama wajibi hukumar ta tace shi. Saboda haka mutanen da su ke ɗaukar fim su na sakawa a YouTube akwai rashin sani da su ke ganin cewa hukumar ba ta da hurumin tace su. Amma duk wani fim ko majigi da za a nuna shi a Nijeriya, to hukuma ta na da hurumin tace shi. Amma da yake kamar mu a nan Arewa da mutane su ke ɗaukar (harkar fim) wata harka ce da ta ke kara-zube, sun ɗauka babu doka. 

“Saboda haka ba daidai ba ne don mutane ba su sani ba, a ce ba za a aiwatar da doka a kan su ba. Saboda haka akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin finafinan da ake sakawa a onlayin da Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, amma mu a nan saboda rashin sani sai ka ji mutane su na cewa ai hukuma ba ta da hurumi a kan finafinan YouTube, bayan cewa babu wata ƙasa da ake saka fim a YouTube ba tare da an tace ba. Kuma wasu ƙasashen ma sun rufe YouTube a ƙasar su, ba a ganin sa. Amma mu a nan Nijeriya saboda an bai wa mutane dama sai kuma su ke zarmewa, su na wuce gona da iri, su na ganin babu doka. 

“Babu wata sana’a da za ka yi ta a Nijeriya babu doka a cikin ta.

“Don haka ina kira ga su masu harkar fim da cewa ita harkar fim idan ka ɗauke ta a matsayin sana’a, shi ne za ka ci gajiyar ta, amma idan ka ɗauke ta a matsayin wata hanya ta burgewa, to hakan ba daidai ba ne, domin harkar fim harka ce da ta ke kawo ɗimbin kuɗi, don haka bai kamata mutane su ɗauke ta da wasa ba.”

Loading

Previous Post

Ban mutu a matsayin marubuciya ba, inji Sadiya Garba Yakasai

Next Post

Sanusi: Magajin Sanusi da Kukuna

Related Posts

AFMAN ta taya Sarari murnar samun damar halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya a Toronto da fim ɗin ‘Kakanda’
Labarai

AFMAN ta taya Sarari murnar samun damar halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya a Toronto da fim ɗin ‘Kakanda’

June 16, 2025
Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima
Labarai

Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
Next Post
Khalifa Muhammadu Sanusi II

Sanusi: Magajin Sanusi da Kukuna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!