TSOHUWAR marubuciyar nan Sadiya Garba Yakasai (Maman Ummi) ta bayyana cewa ita ba ta mutu ba a fagen rubutu, domin kwanan nan ma za ta fito da sabon littafi.
Da yawa ana kallon tsofaffin marubutan Hausa kamar sun mutu a fagen, a yayin da ‘yan onlayin su ka maye gurbin su.
Hajiya Sadiya ta na daga cikin marubutan da su ka shafe tsawon lokaci rabon da su fitar da sabon littafi. Sai yanzu za ta fitar da littafi mai suna ‘Kuskure Ko Ganganci?’
A tattaunawar da ta yi da mujallar Fim, shararriyar marubuciyar ta bayyana cewa littafin zai shiga kasuwa nan da ‘yan kwanaki kaɗan.
Ta yi albishir da cewa littafin zai zo da wani salo da ba a saba gani ba. Ta ce: “Wannan littafin wani salon rubutu ne na zo da shi wanda ya yi daidai da wannan zamanin.
“Kuma masu ganin mu a matsayin tsofaffin marubuta, har gobe ni marubuciya ce kuma shi marubuci ba ya mutuwa sai in har numfashin sa ne ya ƙare. Don haka ni marubuciya ce da a ko da yaushe ina da damar da zan yi rubutu ko na bari, duk ya na daga tsarin Allah. Ba ni ce da kai na ba, sai yadda Allah ya ce shi, ya sa yanzun ma aka gan ni na dawo.”
Ta ci gaba da cewa, “A ko da yaushe marubuci ya na da sabon salo ko tsoho wataƙila irin wancan ne, ƙila kuma wani sabon salon ne, amma dai lokaci zai nuna.
“Na fi yarda shi rubutu baiwa ne, ba ruwan sa da babba ko yaro. Hasali ma ‘ya ta a yanzu marubuciya ce ita ma, irin marubutan onlayin ɗin nan. Ka ga ƙwarewar wasu kenan.”
Da mu ka tambaye ta inda za ta sayar ta sabon littafin nata, ganin a yanzu kasuwar littafin da aka saba da ita ta mutu, sai ta amsa da cewa: “Ba ni da tabbacin inda zan saki littafin. Na yi rubutu, ko ina zai iya karaɗewa.
Ko kasuwa ko ma a ina za a iya samun sa. A jira fitar sa.”
Da mujallar Fim ta nemi jin ƙarin bayani kan marubutan onlayin, sai ta ce, “To babu abin da zan ce illa na ce da yawan su su na ƙoƙari, saboda shi marubuci ba ya rasa abin da zai rubuta bai yi tasiri ba.
“Sai dai shawara ta su rinƙa sanin irin rubutun da za su yi. Su yi rubutun da za a yaba musu, ba wanda za a yi Allah-wadai ba.
“Kowa ya rinƙa rubutun da ya san ko maman sa ko baban sa ko miji ko ɗa zai ɗauka ya karanta ba tare da kin ji kunya ko yin nadama ba.”
Shin ko ita ma ta na karanta rubutun marubutan onlayin? Amsa: “Na ƙalilan na ke karantawa saboda yanzu ba kamar da ba. Da ba ni da nauyin kowa, yanzu kuwa sabgogi sun yi mini yawa; balle da rubutu ya koma na waya, gaskiya wuya ya ke ba ni, duba da ni kai na wannan da na ke rubutawa da ƙyar na ke yi saboda ban saba ba.
Na fi son in yi abi na a takarda, to amma zamani ya canza, sai a hankali.
“Kuma ina jinjina wa duk wani marubuci saboda rubutu ba abu ne mai sauƙi ba.”