• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sheikh Ahmad Tijjani Tukur Yola: Ba rabo da gwani ba, kan a maida kamar sa!

by DAGA AYSHA BILKISU UMAR
April 29, 2020
in Marubuta
0
Sheikh Alhaji Ahmad Tijjani Tukur Yola ya na gabatar da waƙen yabon Manzon Allah (s.a.w.) a wajen wani taro a Kano

Sheikh Alhaji Ahmad Tijjani Tukur Yola ya na gabatar da waƙen yabon Manzon Allah (s.a.w.) a wajen wani taro a Kano

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
AN haifi marigayi Sheikh Alhaji Ahmad Tijjani Tukur Yola a watan Janairu, 1935, a unguwar Satatima cikin birnin Kano. Ya fara karatun allo tun ya na yaro har ya sauke Alƴur’ani a cikin 1948, wato ya na ɗan shekara 13. 
 
Daga nan sai ya fara karatun ilimin addini da na harshen Larabci a wajen mahaifin sa, Malam Tukur Yola. 
 
Bai bar karatu gare shi ba har sai da mahaifin nasa ya koma ƙauye da aiki. Daga nan sai ya juya wajen malaman gari don cigaba da neman ilimin sa.
 
Ya yi karatu wurin malamai da dama kafin ya shiga makarantar Shari’a ta Shahuci a shekarar 1955.
 
Bayan ya gama wannan makarantar sai ya tafi makarantar firamare ta Gwarzo, inda ya shekara biyu ya na koyo. 
 
A cikin 1960 ya fara aikin koyarwa, har zuwa 1966, lokacin da ya shiga makarantar koyon harshen Larabci don ƙaro ilimi. Bayan ya gama a cikin 1969, ya sami takardar shaidar ilimin addinin Musulunci mai zurfi, sai ya koma kan aikin sa na koyarwa. 
 
Bai daɗe ba kuma ya koma Kwalejin Abdullahi Bayero ta Jami’ar Ahmadu Bello don neman digiri, wanda ya kammala a shekarar 1976. Ya cigaba da aikin sa na koyarwa. 
 
Sheikh Tijjani Tukur Yola babban marubuci ne adibi, malami masanin addinin Musulunci, wanda ya ƙare rayuwar sa a ilmantar da al’umma ta fannoni da dama. Haka za, ya yi wa harshen Hausa gagarumin aikin da duniyar nazarin harshen Hausa ba za ta taɓa mantawa da shi ba. 
 
Daga cikin rubuce-rubucen sa na Hausa akwai waƙoƙi masu yawa da su ke ƙunshe da ɗimbin hikimomi da fasaha, gami da zalaƙar sarrafa harshe, da saƙwanni masu ma’ana cikin salo mai ban sha’awa.
 
Ya fara rubuta waƙa a cikin 1950 bisa sha’awar sa ta rubuce-rubucen waƙoƙi. Ya rubuta waƙoƙi da dama a kan addini da wa’azi, da siyasa da zamantakewar al’uma da sauran su. Kaɗan daga cikin waƙoƙin sa sun haɗa da:
 
1. “Ɗan’adam Kayan Allah”
 
2. “Duniya Ba Ki Da Gaskiya”
 
3. “Kanari”
 
4. “Cida”
 
5. “Hawainiya”
 
6. “Garkuwa”
 
7. “Allantaka”
 
8. “Mudi Da Siyasa”
 
9. “Uwa Ta Maganin Wahala Ta”
 
10. “Kar Ka Shigo”
 
11. “Mawaƙin Gaskiya”
 
12. “Ilimi Arziki Ne”
 
13. “Hausa Gwana”
 
14. “‘Yar Sarki”
 
15. “Burin Zuciya”
 
16. “Burtalin Dila”
 
17. “Hanyar Waliyyai”
 
Marigayi Sheikh Ahmad Tijjani Tukur Yola ya rasu a garin Kano a ranar Talata, 28 ga Afrilu, 2020 wanda yai daidai da ranar 5 ga Ramadan, 1441.
 
Allah ya jiƙan sa, ya gafarta masa  ya sa can ta fi nan, amin. 
 
Aysha Bilkisu Umar
28/4/20

Loading

Previous Post

Waƙar gyaran Kano ta Aƙilu Aliyu

Next Post

Kansa ta kashe jaruman Indiya, Irrfan Khan da Rishi Kapoor

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Irrfan Khan (a hagu) da Rishi Kapoor

Kansa ta kashe jaruman Indiya, Irrfan Khan da Rishi Kapoor

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!