SHUGABAN ƙungiyar masu shirya finafinai ta Kadawood kuma sanannen jarumi, Malam Nura MC Khan, ya ƙalubalanci Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano a game da hana shirya fim na daba da ta yi.
Nura MC, wanda mazaunin Kaduna ne, ya yi magana ne a ranar Laraba da ta gabata, jim kaɗan bayan da mujallar Fim ta buga labarin cewa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta haramta yin fim da harkar ‘yan daudu a jihar.
Ya ce, “Sai dai Alhaji Abba El-Mustapha ya manta cewa a YouTube ake kallon waɗannan finafinan da su ke tasiri a zukatan mutane, musamman matasa wanda su ka rasa mafaɗa a jihar.
“A nawa hangen, kusan an riga an makara in dai maganar daba ce a Jihar Kano ce. Ba wai kawai a fim ba ne su ke koya, kusan gadon sa aka yi in dai faɗan daba ne a Kano.
“Za mu iya tunawa tun ina ƙarami na ke jin ‘yan daban Yadakwari da menene ma sunan ɗayan? Na manta. To kun ga kuwa kusan ya zama jinin Kanawa.
“Idan El-Mustapha ya yarda da cewa a finafinai ne ake koyar da harkar daba, to babu ƙwarewa a wannan ɓangaren. Kuma with time mutane za su fara fito da matsaloli ɗaya bayan ɗaya su na danganta shi da fim, cewa ai a fim ake koyarwa.
“Wannan hanyar da hukumar ta ɗauka ba mai ɓullewa ba ce, domin wani aiki ne su ka ɗauko wa kan su wanda gaskiya, iya wannan kawai idan ya ɗauka har ya gama tenuwar sa ba zai iya samun cikakken nasara a kai ba.”
Haka kuma ya ƙara da cewa, “Kada su manta, akwai inda ake shirya finafinai wanda ba wai Kano ba ne kawai, shin ya za a yi da su?
“Ina da mafita wanda zan iya haska wa Hukumar Tace Finafinai, wataƙila ta yi tasiri. Amma hana nuna fim na daba, ba zai hana harkar daba a Kano ba.
“Ina goyon bayan hana nuna daudanci cikin finafinai, hakan kuma zai iya tasiri sosa ai ƙarƙashin hukumar.”
Idan kun tuna, a ranar Laraba ta makon jiya ne Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta ba da sanarwar cewa ta soke shirya fim a kan harkar daba da kuma ‘yan daudu.
Jami’in yaɗa labarai na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne wanda ya ba sanarwar haka a wani saƙon manema labarai da ya fitar.
Ya ce, “Biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da al’umma ke yi a kan shirya finafinan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a Jihar Kano, Shugaban Hukumar Tace finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya ba da umarnin dakatarwa tare da hana dukkan finafinan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a faɗin Jihar Kano.”
Wannan hanin ya jawo ka-ce-na-ce a cikin jama’a, wasu na cewa ya yi daidai a yayin da wasu kuma ke cewa ai harkar daba da ta addabi jihar ba laifin ‘yan fim ba ne.