FITACCIYAR jarumar Kannywood Hadiza Aliyu (Gabon) ta ce ita sam ba ta san mutumin nan da ya kai ta kotu bisa zargin ta yaudare shi ta ƙi auren sa ba.
Gabon ta faɗi haka ne a yau a gaban alƙali a kotun Musulunci da ke Magajin Gari, Kaduna, lokacin da ta fara zuwa domin ta kare kan ta kan tuhumar da mai ƙarar ya ke mata.
Idan kun tuna, a makon jiya mujallar Fim ta ba ku labarin yadda wani Bazamfare mai suna Alhaji Bala Musa, wanda ma’aikacin gwamnati ne ɗan shekara 48, ya yi ƙarar ‘yar wasan, ya na iƙirarin cewa sun yi soyayya tare da alƙawarin aure, har ya kashe kuɗi N396,000 a kan ta, amma ta juya masa baya ta ƙi auren sa.
Gabon dai ba ta je kotun ba a zaman da aka yi a makon jiya, amma ta aika da uziri ta hanyar lauyan ta, Barista Mubarak Sani Jibril, tare da alƙawarin za ta zo a yau.

A yau ɗin, Gabon ta bayyana a kotu, bayan an karanta mata tuhumar da ake yi mata, sai jarumar ta faɗa wa Alƙali Malam Rilwanu Kyaudai cewa ba ta taɓa sanin wannan mutumin ba ballantana har a ce sun yi soyayya da shi.
A cewar ta, ba ta taɓa gani ko haɗuwa da mutumin ba, kuma ba ta san abin da ya faru ba kamar yadda shi ya ke iƙirari.
Ta ce sun haɗu ne a shafin ta na Facebook, amma ita ba ta ma san shi ba, don haka ta bar wa kotu ta yanke hukuncin da ya dace.
Shi kuwa lauyan mai ƙara, wato Barista Naira Murtala, cewa ya yi Bala da Gabon sun fara haɗuwa ne a Facebook inda daga nan soyayya ta ƙullu a tsakanin su, kuma ta yi alƙawarin za ta aure shi. Ya ce tun daga nan ya shiga ɓarin kuɗi a kan ta.
Ya ce: “Ta ce ba ta san shi ba, amma mun faɗa wa kotu cewa za mu kawo shaidu a kan hakan.”
Daga nan sai Barista Mubarak Sani Jibril ya miƙe ya roƙi kotu da ta ba shi belin jarumar, kuma lauyan mai ƙara ya amince da hakan tunda tuhuma ce mai beli.
Alƙali Malam Rilwanu Kyaudai ya amince ya ba Gabon beli a bisa sharaɗin ta kawo mutum biyu yardaddu, mazauna Jihar Kaduna, waɗanda za su tsaya mata.
Daga nan ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 28 ga Yuni, 2022.
A kotun dai Gabon ta rufe fuskar ta da mayafi a lokacin shiga kotun da kuma bayan zaman shari’ar domin kada a ɗau hoton ta