• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Soyayyar mu da Fadila Ummi Lollipop ta har abada ce – Mala

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 11, 2020
in Mawaƙa
0
Abdulhameed Usman (Mala) tare da masoyiyar sa, marigayiya Fadila Muhammad (Ummi Lollipop)

Abdulhameed Usman (Mala) tare da masoyiyar sa, marigayiya Fadila Muhammad (Ummi Lollipop)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ABDULHAMEED Usman, wanda a fagen waƙa aka fi sani da suna Mala, ya na ɗaya daga cikin matasan mawaƙan siyasa da na soyayya waɗanda tauraron su ke haskawa sosai a wannan zamani. Mala mawaƙi ne da bai da hayaniya, ga shi da sauƙin kai da ladabi da biyayya ga kowa da kowa. 

 Mawaƙin ɗan asalin garin Bama ne a Jihar Barno, amma mazaunin garin Kaduna ne. Ya amsa wa ABBA MUHAMMAD na mujallar Fim  tambayoyin da ya yi masa a game da tarihin rayuwar sa da yadda ya shiga harkar waƙa da nasarori da ƙalubalen da ya ci karo da su, da kuma uwa-uba yadda soyayyar su ta kasance da fitacciyar jarumar nan da ta rasu kwanan nan, wato Fadila Muhammad (Ummi Lollipop). Idan kun tuna, mutuwar Fadila ta girgiza jama’a, ‘yan fim da waɗanda ba ‘yan fim ba, musamman ganin cewa ko auren fari ba ta yi ba. Shin wace irin kaɗuwa Mala ya yi a matsayin sa na matashin da ya fi kowa kusanci da ita har su na shirin yin aure? Ga yadda tattaunawar ta kasance:

FIM: Ka faɗa wa masu karatu sunan ka da tarihin rayuwar ka a taƙaice.

 MALA: Assalamu alaikum jama’ar ƙasa baki ɗaya. Da farko dai suna na Abdulhameed Usman. An haife ni a Ƙaramar Hukumar Bama, Jihar Barno. Na yi makarantar firamare na, na yi karatun addini duk a Bama. Daga nan kuma na koma Potiskum na ci gaba da karatun sakandare na. A nan na yi jarabawa amma ban samu tsallakewa ba, sai da na dawo Kaduna, sai na shiga Rimi College, inda a nan na ƙarasa karatu na.

FIM: Menene asalin yaren ka?

 MALA: Ni Bafillace ne. Mahaifiya ta Bahaushiya ce, amma ta na da dangi Barebari. Wannan ya sa na iya Fillanci, Barbanci, yaren Shuwa Arab, ga shi kuma ina jin Hausa.

FIM: Ka na waƙa da waɗannan yarukan gaba ɗaya?

MALA: Alhamdu lillahi, ina waƙar siyasa da soyayya da Barbanci, haka ina yi da Fillanci, sannan uwa-uba Hausa.

FIM: Ya aka yi ka tsinci kan ka a harkar waƙa?

 MALA: Waƙoƙin soyayya ne su ka ja ra’ayi na har na fara waƙa. Kuma da waƙar soyayya na fara. Domin ina yawan jin waƙoƙi, kawai sai na ji ya kamata ni ma na yi. Haka kuma ina yawan kallon finafinan marigayi Ibro, shi ma ya ƙara sa mani sha’awar in fara waƙoƙin Hausa. 

 Wata rana na je wurin Ibro a Gombe, ya ce mani zai kai ni situdiyon abokan sa na yi waƙa, amma Allah bai yi ba; da wannan maganar ya kai shekara goma sha shida.

FIM: Wace shekara ka fara waƙa, kuma da wacce ka fara?

 MALA: Yanzu dai na kai shekara goma sha shida da fara waƙa. Na kuma fara waƙa ne da wata waƙar soyayya inda na waƙe wata masoyiya ta, da na je Gombe, Barhama ya kai ni situdiyon su Isah Gombe. Oga Jiyo shi ya yi mani kiɗa a lokacin da na fara waƙa.

FIM: Koya maka waƙar aka yi ko kuma da kan ka ka fara?

 MALA: Allah shi ke yin komai. A lokacin ina da wani aboki, kullum na kan rubuta baiti ɗaya, sai in kai wa abokin nawa ya aje mani, har na yi tsawon kwana bakwai. A haka har na haɗa baiti bakwai na waƙar. Sunan waƙar ‘Hassanaye’. Yarinyar ‘yar Biu ce, sunan ta Hassana.

FIM: Waƙoƙin da ka yi za su kai nawa?

MALA: Gaskiya ba zan iya cewa ga yawan waƙoƙin da na yi ba, saboda ina da situdiyo ne nawa na kai na. Amma a yanzu aƙalla za a iya samun waƙoƙi na da su ka kai dubu biyu.

FIM: Ka taɓa zama a ƙarƙashin wani ne kafin ka buɗe naka situdiyon? Kuma wanene ubangidan ka? 

MALA: Gaskiya ina da iyayen gida da dama. Akwai maigida na wanda idan na rubuta waƙa shi ke duba min, Alhaji Yusuf Kebbi, shi ke duba min waƙoƙi na. Amma wanda na zauna a ƙarƙashin sa shi ne Alhaji Aminu Dumbulum. Bayan shi ba ni da wani ubangida. Amma dai duk da haka ban tsaya wuri ɗaya ba; duk inda na san zan ƙaru ina kai ziyara wurin don ƙarin ilimi a kan harkar. 

FIM: Wace waƙar ka ce ta yi fice?

MALA: A ɓangaren waƙar soyayya, akwai wata waƙa da Hajiya Fatima Lamaj ta sa ni na yi mai suna ‘Zarah’, gaskiya wannan waƙar alhamdu lillahi ta samu karɓuwa sosai, domin ta shiga ko’ina, kuma mutane su na kira na daga ko’ina saboda wannan waƙar su na ba ni aiki. Ɓangaren waƙoƙin siyasa kuma ga su nan babu adadi. Na yi wa Kwankwaso waƙoƙi ban san iya adadin su ba, daga baya na juya ina yi wa Ganduje waƙa. Da na ga tafiyar ba za ta yi mani daɗi ba, sai na sake dawowa ƙarƙashin Kwankwaso. Kwanan nan na yi wa Kwankwaso waƙa, an ba ni kujerar Umara har guda biyu. A yanzu da wannan waƙar aka san ni, domin a kullum na kan amsa waya sama da ɗari biyu a rana saboda waƙar. Sunan waƙar ‘Yanzu Ma Mu Ka Fara Madugu’.

FIM: A kwanakin baya ubangidan naka, Aminu Dumbulum, ya bar tafiyar Kwankwaso, ya koma tafiyar Ganduje. Kai kenan ba ka bi sahun ubangidan naka ba?

MALA: Ko a gida ɗaya ana samun  uba ya ce ga ra’ayin sa, ɗa ya ce ga ra’ayin sa, uwa ma ta ce ga ra’ayin ta. Amma ina zaune da shi lafiya, sai dai a kan wannan waƙar mun samu matsala da shi ba kaɗan ba don har sai da ta kai ga mun raba jiha da shi! Daga baya an sasanta mu, mu ka ci gaba da mu’amala. Tunda dai ubangida na ne, ban raina shi ba; ubangidan ka, ubangidan ka ne duk matsayin da Allah ya ba ka.

FIM: Waɗanne nasarori ka samu a harkar waƙa? 

MAKA: Alhamdu lillah! Na samu nasarori da dama. Na farko, da waƙa na taɓa yin aure, da waƙa na gina gida, da waƙa na samu mota, da waƙa na sayi Keke Napep sun kai guda huɗu. Na biyu, a yanzu haka da waƙa za ni Umara, in kuma kai mahaifiya ta. Kuma yanzu haka da waƙa zan ƙara aure. Duk abin da na samu ba ta wata hanya ba ne sai ta hanyar waƙa. 

FIM: Ɓangaren ƙalubale kuma fa?MALA: Ai a wannan harkar in har mutum ya ce bai samu ƙalubale ba, gaskiya bai kai ba. A cikin ƙalubalen da na fuskanta, na sha zuwa situdiyo a kore ni, in na je wani situdiyon ma su kore ni, saboda ana tunanin ba zan kai wannan matsayin ba.

FIM: Menene dangantakar ka da marigayiya Fadila Muhammad (Ummi Lollipop)?

MALA: Alhamdu lillah! Asalin ɗaukaka ta, Fadila ita ce sanadi. Allah ya jiƙan ta, ya gafarta mata. Har ga Allah babu wata mace da ta nuna min ƙauna a duniya sama da Fadila. Fadila ta na son cigaba na, Fadila ta haɗa ni da mutane don in samu arziƙi. Kuma a kowane irin hali Fadila ta na haƙuri da ni, ko da kuma ɓata mata rai na yi. Wasu lokutan ma ni na ke ƙaƙalo abin da zai sa mu samu matsala, amma a haka za ta yi haƙuri da ni. Ga shi Allah ya ɗaukaka ta sama da ni, amma ita burin ta ta ga na ɗaukaka sama da ita. Ta sha faɗa min cewa ta na yi min addu’a in samu ɗaukaka sama da ita. Ɗaukaka na Allah ne. Amma alhamdu lillahi, addu’ar da ta yi Allah ya amsa, domin ina gani wallahi. Ni ma ina yi mata addu’a Allah ya gafarta mata.

FIM: Ya ka tsinci kan ka a lokacin da ka samu labarin rasuwar ta?

MALA: A gaskiya ban taɓa jin mutuwar da ta girgiza ni ba irin mutuwar Fadila. Lokacin da mahaifi na ya rasu na kaɗu, amma rasuwar Fadila ta kaɗa ni sosai, saboda irin shaƙuwar da mu ka yi. Kullum mu na tare. A tarayyar da mu ke yi, ta na son ƙaruwa ta, ina son ƙaruwar ta. Har na kai matsayin da saurayi zai ce ya na son ta, za ta kalle shi ta ce masa ita ni ta ke so.

FIM: Kafin rasuwar ta ko akwai maganar aure a tsakanin ku? 

MALA: Gaskiya akwai maganar aure. Don shekara kusan biyu a baya, mun yi maganar aure da ita, a ranar na faɗa mata cewa ta fi ƙarfi na don ita babbar jaruma ce, ban kai ƙarfin da zan iya auren ta ba, don ta fi ƙarfi na a ɓangaren aure duk da dai an ce namiji shi ke gaba da mace. Amma akwai mace da ka gan ta ba ka isa ka je ka tunkare ta da maganar aure ba, saboda ka san yanayin da ta ke, kai kuma ka san yanayin aljihun ka. Na ce mata gaskiya ba zan iya auren ta ba saboda ta fi ƙarfi na. Nan ta ke ran ta ya ɓaci, ta ce mani in je in sauke ta a gida. Na je na sauke ta; da ma motar ta na ke hawa a lokacin. Motar ta ta ba ni don in ci gaba da harkoki na, don ta ce ni mawaƙi ne dole akwai inda zan rinƙa zuwa, dole sai da mota. Duk inda mu ka je can na ke barin ta in tafi harkoki na da motar, in ta gama abin da za ta yi sai ta hau Keke Napep ta koma gida.  

Na samu ƙalubale a wurin mutanen mu, inda su ke cewa ya za a yi ina ƙaramin mawaƙi ina soyayya da babbar jaruma? 

Abdulhameed Usman (Mala): “Duk abin da na samu ba ta wata hanya ba ne sai ta hanyar waƙa”

FIM: Za ka iya tuna maganar ku ta ƙarshe da ita? 

MALA: Maganar mu ta ƙarshe da ita, ta kira ni za ta zo wuri na a situdiyo, sai na ce mata ba na situdiyo. Wannan shi ne maganar mu ta ƙarshe.

FIM: Bayan rasuwar Fadila, akwai wata magana da ka yi da iyayen ta?

 MALA: Gaskiya akwai. A ranar da ta rasu Aunty Dije ta kira ni. Ni ne mutum na farko da na fara zuwa kan gawar ta. 

 Fadila ta na yi wa iyayen ta biyayya kamar yadda ya kamata ‘ya ta yi wa iyayen ta, domin duk inda za mu je, in mu na hanya baban ta ya kira ta za ta ce mani, “Mala, juya motar nan, Baba na ya kira ni.”  

Ni saurayin Fadila ne, zan iya shaidar ta har a gaban Allah. Mun yi magana da baban ta bayan mun dawo maƙabarta, har ya ke ce mani ji ya ke yi shi kamar zai rasu domin Fadila ita ce gatan sa. Jin haka ya sa na fashe da kuka, na ce masa, “Baba, in Allah ya yarda ina tare da ku har abadan abidina!” Na ce masa kuma ko da yake Fadila ba ta tare da su, zan kasance tamkar ɗan da su ka haifa, za mu ci gaba da mu’amala da su.  

Da ma a cikin watan azumi akwai kalmar da ta faɗa min, ta ce, “Ni da kai hanta da jini!” Sai ta ƙara da cewa, “Ga ni ga Malan Waƙa, hanta da jini, ba ma rabuwa!” Sai na ce, “Me zai raba mu ni da ke?” Sai ta ce, “Sai mutuwa.” Amma a wannan lokacin na ce mata, “Masha Allah!” Amma ban gane haka ba sai da Allah ya yi mata rasuwa. 

 Don haka ni a wuri na mutuwa ba za ta raba ni da Fadila ba. Ko da ba ta raye zan je gaban kabarin ta in yi mata addu’a, kuma zan iya haihuwar ‘ya mace in saka mata suna Fadila, don ba zan taɓa mantawa da ita ba. Ita ce a zuciya ta har yau har gobe. 

FIM: Ka taɓa yin album?

 MALA: Gaskiya ban taɓa yin album ba.

FIM: Ka na da burin yi ko da nan gaba?

 MALA: Gaskiya ina da buri. Kuma nan ba da jimawa ba zan yi, in-sha Allahu. 

FIM: Mecece shawarar ka ga mawaƙa? 

MALA: Shawara ta ga mawaƙa, zan iya cewa a yadda mu ke tare sana’ar mu ɗaya, jinin mu ɗaya, kan mu ɗaya,  ya kamata mu ƙara haɗa kan mu. Kuma mu rinƙa ba na ƙasa da mu dama da ƙwarin gwiwa don su ma su samu ɗaukaka. Sannan mu ci gaba da yi wa juna addu’a, musamman idan mu ka rasa ɗaya daga cikin mu. 

FIM: Me za ka ce wa masoyan ka?

MALA: Abin da zan ce wa masoya na shi ne na gode. Kuma su ci gaba da taya mu da addu’a don harkar mu ta ƙara samun ɗaukaka da cigaba. Kuma ina son masoya na da su rinƙa haƙuri da junan su. Sannan akwai lokacin da za a kira ni a waya ban ɗauka ba, don Allah a yi haƙuri a yi min uzuri, aiki ne. 

Loading

Previous Post

‘Yan biyu za mu aura, inji Tagwayen Asali

Next Post

Shirin Yaƙi Da Yunwa na nan tafe

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Next Post
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Shirin Yaƙi Da Yunwa na nan tafe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!