• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sukar da aka riƙa yi wa ‘yan zaman shahada ce aka kwaso aka yaɓa wa ‘yan Kannywood – Zulai Bebeji

by DAGA IBRAHIM HAMISU
December 27, 2022
in Taurari
1
Hajiya Zulaihatu Aliyu Abdullahi Bebeji

Hajiya Zulaihatu Aliyu Abdullahi Bebeji

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HAJIYA Zulai Bebeji ƙwararriyar ‘yar wasa ce wadda ta yi fice a Kannywood inda ta ke fitowa a finafinai a matsayin uwa tagari. A tattaunawar da ta yi  mujallar Fim kwanan baya, ta bayyana yadda aka yi ta shigo Kannywood da irin nasarorin da ta samu da ƙalubalen da ta ci karo da shi da kuma yadda ta ke zaune da kowa lafiya a fagen harkar fim har aka raɗa mata sunan ‘uwa tagari’. Ga hirar:

FIM: Wace ce Hajiya Zulai?

ZULAI BEBEJI: Suna na Zulaihatu Aliyu Abdullahi Bebeji ko Hajiya Zulai Bebeji ko Hajiya Zulai Uwa Tagari. Ana yi min laƙabi  da Attajira.

FIM: Ki na daga cikin tsofaffin hannu da ki ka ga jiya ki ka ga yau a wannan masana’ata ta Kannywood. Waɗanne irin nasarori ki ka samu?

ZULAI BEBEJI: Alhamdu lillah, na samu nasarori da yawa a harkar fim. Alfarma da ake yi mana sanadin fuskar mu ita ma nasara ce. Yanzu haka yarinya ta ta na ‘School of Hygiene’, gaba ɗaya al’amarin makarantar ta alfarmar fim ce. Kuma akwai ‘yan fim da yawa waɗanda ni ne silar shigowar su Kannywood. Yanzu haka a wannan lokeshin ɗin akwai yaron da sanadiyya ta an sanya shi a wannan fim ɗin kuma wuri mai kyau. Wasu ma sai mun haɗu sai su same ni su ce ai su ne waɗanda na yi magana aka sanya su a fim. Kuma akwai kamfanoni kamar ‘Khairiyya Fim Production’ da kamfanin Ali Rabi’u Ali Daddy da GSharif25 sun ba ni matsayin uwa da na ke  zama da yara mu na ba su horo na musamman a kan fim. Don haka babu abin da za mu ce wa Allah sai godiya.

FIM: Waɗanne irin ƙalubale ki ke fuskanta kawo yanzu a wannan masana’anta?

ZULAI BEBEJI: Ƙalubale musamman a wannan ƙasa tamu ta Kano, wato ka san ƙasa ce ta malamai da al’umma daban-dadan, to har yau za ka ga fim bai shiga jikin jama’a ba. Sai ka ga wani ya na yi maka kallon don kawai ka na fim, wani lokacin har rai ya kan ɓaci. Ni na kan ce mu ma ‘ya’ya ne, mu ma masu usuli ne, ba daga sama aka jefo mu ba, kuma ba daga wata uwa duniya aka jefo mu ba, kuma duk bawa ba zai wuce ƙaddarar sa ba. Don haka idan akwai ƙalubale, ba zai wuce wannan ba. 

Cewar Hajiya Zulai Bebeji: “Mu ma ‘ya’ya ne, ba daga sama aka jefo mu ba”

FIM: Wasu na cewa  masana’atar Kannywood  wuri ne na sheƙe aya da rashin tarbiyya, musamman mata. Me za ki ce a kan haka?

ZULAI BEBEJI: A cikin kowace mu’amala ta rayuwa akwai mai kyau akwai mara kyau, kuma ko wane tsuntsu kukan gidan su ya ke yi. Idan ka ga mutum ba shi da tarbiyya a cikin mu, to da ma haka ya zo, da kayan sa ya zo, kuma ɗan ɗan tarbiyya duk inda ya shiga, ba zai cire rigar gidan su ya jefar ba. Saboda haka ba fim ba ne. Da kafin fim ‘yan zaman shahada na Saudiyyya ne su ake ɗora wa balai’n duniya; ‘yar zaman shahada ko a Ka’aba ta ke kwana ‘yar iska ce, yanzu kuwa fim ya karɓe wannan!

FIM: Wanene ubangidan ki a Kannywood?

ZULAI BEBEJI: Ba da alfahari ba, ni gaskiya ba ni da wani  ubangida. Da ƙafa ta na shigo harkar fim. Kamar yadda na gaya maka, ni mace ce mai karance-karance, don haka ni jagora ta a harkar Hausa film mujallar Fim ce, domin na sayi mujallar Fim naira bakwai a Bata. Haka na ke sayo ta na ke karantawa, ina karantawa. To da na samu wani ɗan ɓacin rai a rayuwa ta ta aure, to kawai sai na ce ni fim zan yi. Har wata ‘yar’uwa ta ta ke cewa, ah gaskiya za ta nema min tsari a kan Allah ya kiyaye ya tsare ni da shiga fim. Na ce, “Saboda me za ki ce haka? Su waɗanda su ke yi ba ‘ya’ya ba ne? Ai su ma ‘ya’ya ne, haifar su aka yi!” To, haka dai kamar da bakin mala’iku, ga shi da rabon zan yi ɗin. Don haka ni babban ubangida na bai wuce mujallar Fim ba, domin da ita na samu adireshoshi na kamfanonin fim. Duk da yake na je kamfanoni  daban-daban mun zauna da su amma ban fara fim ba sai ta hannun marigayi Tjjani Ibrahim, don ya sanya ni a fim ɗin ‘Ƙudira’. To ka ga idan ina da wani ubangida ba zai wuce marigayi Tijjani Ibrahim ba. Haka na ke aiki na a masana’atar. Amma a ce ko a mutu ko a yi rai a ce wai wane ne ubangida na, wanda duk wani abu idan ya taso ya sa a nemo ni, gaskiyar magana ba ni da shi.

FIM: Menene fatan ki na ƙarshe ga masoya da abokan aikin ki na Kannywood?

ZULAI BEBEJI: Mu na yi masu fatan alheri. Allah ya bar ƙauna. Abokan aiki kuwa ina yi masu fatan samun nasara, da fatan Allah ya ƙara ƙwarin gwiwa.

Hajiya Zulai ta ce ta hannun marigayi Tjjani Ibrahim ta fara yin fim
“Babban ubangida na bai wuce mujallar Fim ba,” inji Hajiya Zulai Bebeji

Loading

Tags: Ali Rabi'u AliƙalubaleMujallar Fimnasarorishiga KannywoodtarihiTijjani IbrahimUwa TagariZulai Bebeji
Previous Post

‘Yan Kannywood sun yi juyayin cika shekara 20 da rasuwar darakta Tijjani Ibrahim

Next Post

‘Yan siyasa ne ke tafka maguɗin zaɓe ba hukumar zaɓe ba – INEC

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
Onyeka Pauline Ugochi

'Yan siyasa ne ke tafka maguɗin zaɓe ba hukumar zaɓe ba - INEC

Comments 1

  1. isiyaku lawal says:
    2 years ago

    Comment:Allah kara taimko hajia xulai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!