A WANNAN watan na Disamba ne babban darakta Tijjani Ibrahim ya cika shekara 20 cif rasuwa, wato ya rasu a cikin 2002. Hakan ya sa wasu daga ‘yan Kannywood da su ka yi rayuwa da shi ko suka zauna a ƙarƙashin sa su ka wallafa alhinin su dangane da rashin sa tsawon 20 da bayanai a kan irin gudunmawar da ya bayar a masana’antar.
Alhaji Ibrahim Mohammed Mandawari, jarumi kuma Mai’unguwar Mandawari, Kano, ya wallafa jawabi kamar haka: “Allahu Akbar kbar, Allah ya jiƙan Daraktan Daraktoci Tijjani Ibrahim Bala. Ya na daga cikin waɗanda su ka bayar da gudunmawa mai tarin yawa wajen samar da masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, musamman a ɓangaren ‘directing’.
“Ya fara aiki da gidan television na CTV 67 (yanzu ARTV Kano) a matsayin ‘cameraman’ kafin ya zama ‘producer/director’, sannan ya yi kwasa-kwasai a ‘film and television’ a TV College da National Film Institute da kuma Ohio University da ke United States of America.
“Damo sarkin haƙuri, Tijjani ya horar da daraktoci da dama a wannan masana’anta kuma ya kafa kamfanin Fasaha Films inda ya dinga samar da finafinai masu tasiri a wancan zamani.
“Allah ya jiƙan sa, ya gafarta masa.”
Shi ma ɗaya daga cikin manyan yaran Tijjani Ibrahim, Mika’iku Isa bin Hassan (Gidigo), a tattaunawar sa da mujallar Fim, ya bayyana cewa: “Maganar gaskiya, Tijjani Ibrahim mutum ne da ba za a taɓa mantawa da shi ba a wannan masana’antar ta Kannywood, domin duk wani cigaban da ake gani a yanzu, kusan shi ne silar kawo shi, domin shi ne farko da ya sauya masana’antar daga fim na talbijin zuwa ‘home video’, kuma shi ya samar da tsarin aikin darakta da furodusa da jarumi, kowa ya san matsayin sa. Don haka duk wani darakta ko furodusa da jarumi da ya yi lokaci da shi har yanzu ya na alfahari da cewar Tijjani Ibrahim uban lgidan sa ne.
“Don haka mu na fatan Allah ya ƙara rahama a gare shi, ya kyautata makwancin sa.”
Darakta Hafizu Bello, wanda shi ma ya na ɗaya daga cikin manyan yaran marigayin, ya bayyana mana cewa: “Babu wani abu da zan ce sai dai Allah ya jiƙan sa, domin kuwa gudunmawar da ya bayar ce a masana’antar Kannywood mu ke rayuwa da ita har yanzu. Don haka, komai tsawon lokaci, in dai za a faɗi tarihin masana’antar Kannywood, to ba zai cika ba sai an haɗa da ayyukan darakta Tijjani Ibrahim. Mu na fatan Allah ya yi masa rahama.”
Saleem Tijjani Ibrahim, babban ɗan marigayin wanda ya gaje shi a industiri, shi ne ya fara nuna wa jama’a cewa baban sa ya cika shekara ashirin da rasuwa. A rubutun da ya yi a Turanci da Hausa a soshiyal midiya, Saleem ya ce: “20 years without you! You will always be remembered in thoughts and prayers. Allah ya kyauta makwanci Abba!”
Mutane da dama sun yi magana kan wannan addu’ar, ciki har da ‘yan fim da su ka haɗa da Maijidda Abbas, wadda ta ce: “Allahu Akbar! Allah ya jaddada rahama, ya kai haske kabarin shi. Oga mun yi babban rashi, mu na ta kewar ka oga. Allah ya haɗa fuskokin mu gobe kiyama.”
Shi ma Saraki Tijjani cewa ya yi: “Ubangiji Allah ya jaddada masa rahama, ya sa Aljannar Firdausi ta zamo makomar dukkan Musulmi don limamin mala’iku Annabi Muhammadu s.a.w.”