NA kan sha jin maganganu ko ra’ayi a kan abin da ake kira tsarin iyali ko tazarar haihuwa waɗanda su ke nuna hakan shisshigi ne ko shiga hurumin Allah. A kan nuna wa mutum cewa tunda Allah ne mai ba da haihuwa da hanawa, mutum bai kamata ya ɗau mataki na yin wani tsari ba, kawai ya bar haihuwar ta faru ba da wani tsari ba.
Masu ra’ayin sukar tsari a haihuwa su na cewa Allah ne mai arzutawa, saboda haka ba daidai ba ne mutum ya ce zai yi tsari a haihuwa. Su na kuma nuna cewa wata hanya ce ta Yahudanci da aka shiryo ta don rage yawan Musulmi ko al’ummomin ƙasashe masu tasowa. Amna kuma su ma Yahudawan ba sa haihuwa da yawa, ka ga kenan ba don hana waɗansu haihuwa su su haihu su ka fito da tsarin iyali ba.
Allah da ya halicci ɗan’adam ya bambanta shi da sauran halittu ta ba shi kaifin basira da hankali. Wannan ya saka ɗan’adam ya ke yin tsari a rayuwar sa a komai wanda da ba ya tsari da rayuwar sa, za ta zama kamar ta dabbobi.
Na farko, ɗan’adam ana haihuwar sa huntu tsirara, ba da sutura ba. Abu na farko da ya bambanta mutum da dabba shi ne saka sutura. Mutane su na saka auduga su yi abin da ake sutura da shi tun zamani mai tsawo. Da mutum ba zai yi tsari a nan ba, zai yi yawo ne tsirara.
Mutum ya gano dabarar gina gida ya shiga saboda kare kan sa daga zafin rana, ruwan sama da dabbobi masu cutarwa. In da bai yi tsari ba, sai ya kwana a daji kamar dabbobi.
Ɗan’adam ya gano dabarar noma abin da zai ci maimakon yawo ya na cin tsirrai kamar yadda dabbobi su ke yi. Ya gano ya share gona, ya yi shuka, ya yi huɗa, ya zuba mata taki don ya samu amfani mai kyau.
Mutum ya gano dabarar ƙirƙirar abubuwan da za su sauwaƙa masa tafiya kamar hawa dabbobi da ƙera na’urori kamar keke, motoci, jiragen sama da na ruwa. Haka kuma mutum ya gano dabarar yin magunguna da yin aiki don warkar da cututtuka. Ba ya zama kawai ya bar cuta ta warke da kan ta.
Duk waɗannan tsare-tsare da mutum ya yi don sauwaƙa wa kan sa rayuwa da samun abinci mai kyau da wurin zama da sauwaƙe kan sa tafiya da lafiya, a wajen haihuwa ne kawai ya ke ganin zai haihu ba wani tsari saboda in ya yi tsari ya yi shisshigi! Ka ga hankali ba zai ɗau wannan tunanin ba.
Ita dabarar tsarin iyali babban amfanin ta shi ne inganta lafiyar mace da ta ke haihuwa da ‘ya’yan da ta ke haifa. Wannan ta na ba da dama ga wanda ba shi da ƙarfin tafiyar da rayuwar yara da yawa ya haifi yaran da zai iya kula da su.
Abin da masu adawa da wannan tsarin ba sa lura da shi shi ne a asibitin da ake tsarin iyali kuma ana taimaka wa waɗanda ba su haihu ba ko haihuwa ta tsaya su na son su ƙara haihuwa su samu haihuwar. Ka ga in da kawai so ake a rage yawan jama’a, da likitocin murna za su yi su ga waɗanda ba su haihu ba kuma ba wani taimako da za a yi masu tunda kawai hana haihuwa ake son yi. Irin wannan taimakon da ake bayarwa ya haɗa da dabaru na likita da yawa kuma a kan dace da samun haihuwar.
Sai ka ji masu tunanin haihuwa gaba-gaɗi su na cewa ai ɓarayin gwamnati su su ka sace kuɗin al’umma, su ya kamata a hana sata ba wai taƙaita haihuwa ba. Na ɗauka wanda ya san cewa ƙasar nan ana fama da matsalin tattalin arziki, wanda zai yi wahala talaka ya iya maganin su, ya kamata ya taimaki kan sa wajen haihuwa daidai ƙarfin arzikin sa. Ni ban damu don mutum ya ce zai haifi ‘ya’ya ashirin a wannan zamani ko fiye da haka ba. Ba wanda ya hana shi. Amma ya sani cin su da shan su da tufatar da su aikin sa ne, ba haƙƙin maƙwabta ko ‘yan’uwa ba.
Ba martaba a ga mata su na yawo da ‘ya’ya a goye da waɗansu a janye su na cewa a taimaka masu da abinci saboda mazajen su ba su da ƙarfi. Ba martaba a ji yara su na shiga gidan rediyo su na cewa a taimaka masu da kuɗin makaranta saboda iyayen su ba su da ƙarfi.
* Dakta Abdullahi Ɗahiru likita ne a Birnin Kano. Ya yi wannan shrhin ne a Facebook