• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka: Daga Wali Ɗanmasani zuwa jiya

by DAGA FATUHU MUSTAPHA
June 21, 2023
in Addini
0
Surar yaƙin jihadin Islama (Hoto daga shafin History of Islamic Wars, a Facebook)

Surar yaƙin jihadin Islama (Hoto daga shafin History of Islamic Wars, a Facebook)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A TSAKANIN 1980 zuwa 1983, wani salon waƙa da labari ya karaɗe dukkan loko da saƙo-saƙo na ƙasar Hausa da aka fi sani da waƙar Yaƙin Tabuka. Wannan waƙa an ɗauki salon wata tsohuwar waƙa ne ta Shehu Muhammad al Kashnawi al Masani da aka fi sani da Wali Ɗanmasani da ya kira Waƙar Yaƙin Badara. Ba dai takamaiman yaushe aka yi waƙar, kuma jami’an yaɗa irin waɗannan kasakasai irin su Musa Nasaleh da Rabi’u BK da Malam Ƙalarawi duk ba su iya bayar da wani gamsasshen bayani kan wanda ya yi waƙar ba. 

Tun a wancan lokaci aka riƙa maganganu kan gaskiyar abin da waƙar ta ƙunsa. Wasu na ganin kawai shaci-faɗi ne, abin bai faru ba, wasu kuma su na ganin hakan ya faru. Ba na mantawa, an taɓa saka wa Malam Aminuddeen Abubakar waƙar, ya nuna farin cikin sa da ita, amma ya yi ƙarin haske da cewa ba haka abin ya faru ba, amma abu ne mai kyau domin a zaburar da mutane a kuma nuna masu irin gwagwarmayar da aka sha wurin kafa Musulunci. Wannan ƙarin haske na Malam Aminuddeen (Allah ya jikan sa) shi ne ya kawo ƙarshen ce-ce-ku-cen da aka yi a kan waƙar. 

To amma me waƙar ta ƙunsa? Wannan waƙa mai haɗe da labari ta ƙunshi gwagwarmayar da aka yi ne tsakanin dakarun rundunar Musulunci ƙarƙashin jagorancin mai gayya mai aiki, Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) da dakarun tsohuwar Daular Byzantine. Kuma an fita yaƙin ne a lokacin hijira na da shekara tara, wannan kuma shi ne yaƙi na ƙarshe da Manzon Allah ya fita a rayuwar sa. Ya fita da runduna mafi girma da Musulunci ya taɓa tarawa a zamanin sa, domin masana sun ce ya fita da sama da mutum 30,000. 

Wannan fita dai ita ce karo na farko da ya bar Sayyadi Aliyu a gida, inda ya umarce shi da ya zama wakilin sa a Madina, sannan kuma har ya je ya dawo bai gamu da rundunar Byzantine ba, wanda hakan ya nuna ba a gwabza yaƙi ba. Sai dai ya shafe kimanin sama da wata guda a wurin, ya na ƙoƙarin janyo hankulan shugabannin al’ummomin wurin da su amince su bai wa Musulunci haɗin kai. Da yawa masana na ganin Daular Byzantine ta karaya ne tun bayan da ta samu labarin irin fitar da Musulmi su ka yi, da kuma irin tarin rundunar da su ka fito da ita. 

Tambaya ta biyu ita ce shin abin da aka faɗa a waƙar haka ya ke ko kuwa ba haka ya ke ba? Shin in haka ya ke, to tunda ba a yi yaƙin ba, ya abin ya faru? A ina abin ya faru? Ya aka yi Sayyadi Ali (KarramalLahu wajahahu) ya samu kan sa a labarin? Bari mu amsa wannan tambayar domin mu warware matsalar. 

Da farko dai ya kamata a sani, akwai nason gaskiya a wannan waƙa tasa, sai dai abin da ya faɗa, kashi 10 cikin ɗari ne gaskiya, kashi 90 duk ƙari ne kawai, domin dai a nuna irin sadaukantar da kai na dakarun Musulunci. Domin ko shakka babu, an taɓa fita yaƙi da aka yi ɗauki-ba-daɗi da Sayyadi Ali a matsayin babban kwamandan dakarun Musulunci da wani babban kwamanda na Yahudawa da ake kira da Marhab bin Abi Zainab. Wannan suna Marhab shi ne kila bai ji sosai ba, sai ya kira shi da Ƙaura ɗan Marwana. Wani abin sha’awa game da yadda ya wassafa waƙi’ar shi ne yadda ya hausantar da abin, ya sanya kirari irin na Hausa, ya ɗauko muƙamai irin na dakarun ƙasar Hausa ya sanya wa wasu dakaru da ya yi amfani da su a yaƙin, musamman Ƙaura ɗan Marwan (Marhab bin Abu Zainab). Kowa ya san Ƙaura na nufin wani shahararren kwamandan yaƙi, kamar irin su Ƙaura Ama, Ƙaura Hasau na Maraɗi, da sauran su. 

Surar gwabzawar Musulmi da kafiri a fagen daga (Hoto daga History of Islamic Wars, a Facebook)

Wannan yaƙi an yi shi shekara ta 7 bayan hijira, kuma shi ne yaƙin da ya kulle wa Musulmai ƙofar talauci ya ɗaga tattalin arzikin Madina. Har ma Nana A’isha na cewa, “Musulmai ba su san yalwa da tarin arziki ba sai bayan da aka yi yaƙin Khaibar.” Wannan yaƙi shi ake kira da Yaƙin Khaibar! 

Khaibar wani babban gari ne mai ƙarfin arziki da Yahudawan da su ka baro Daular Rum su ka kafa kimanin kilomita 150 yamma da birnin Madina. Gari ne da ke da dausayi da dama a tare da shi, kuma ya haɓaka fiye da kowane gari a jazirar Larabawa saboda arzikin noma da su ke da shi. Kuma shi ne fito-na-fito na farko da ya auku a tsakanin Musulunci da Yahudawa. Wannan ya sanya nasarar da Musulunci ya samu a wannan yaƙi ta buɗe ƙofofin wadata da ƙaruwar arziki a tsakanin Musulmai. 

A wannan yaƙi Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) ya fita ne da soja 1,600, a yayin da su kuma Yahudawa su ke da soja 10,000 da kuma ‘yan haɗin gwiwar su, wato Bani Gattafan, su 4,000. Wato dai soja 14,000.  Baya ga wannan, Yahudawa sun fi Musulmi ƙarfin tattalin arziki nesa ba kusa ba, sannan kuma su na da ganuwa da babu irin ta duk faɗin jazirar Larabawa, wanda hakan ya sanya cin su da yaƙi sai mai ƙarfin imani. 

A haka rundunar Musulunci ta fita ta kuma gwabza yaƙi da ta Yahudawa, sai dai masana tarihi sun tabbatar da cewa a wannan fita ba a fita da Aliyu ɗan Abi Talib ba, saboda ya na fama da ciwon ido. To amma saboda ƙarfin mayaƙa da yawa ga kuma ƙarfin arziki, ya sanya cin su da yaƙi ya faskara. 

Masana sun ce akwai dalilin da ya sanya Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) bai fita da ƙatuwar runduna ba, ya yi haka ne saboda ya shammace su ya kai masu samame ba tare da sun ankara ba. Daga ɓangaren Yahudawa, sun raina rundunar da Musulmi su ka fito da ita, don haka su ka ƙi haɗe kan su wuri ɗaya, wanda haka ya bai wa Musulmi damar yi masu ɗauki ɗai-ɗai.

Inda aka shata daga shi ne wurin yaƙar babban garin su da ake kira Ƙamus, wanda shi ne mazaunar da manyan shugabannin su ke ciki. Da farko dai an tura Muhammad bin Maslama, wani gogaggen kwamandan yaƙi, to amma bai yi nasarar samun shiga garin ba. Bayan ya komo sai aka tura Sayyadi Abubakar, shi ma bai nasara ba. Aka tura Sayyadi Umar, shi ma Allah bai yi zai iya buɗe garin ba. Masana sun ce an shafe kwanaki 19 ana wannan ba-ta-kashi amma babu nasara, kuma dukkan ɓangarorin sun fara galabaita saboda rashin ruwa. Daga ɓangaren Musulmi kuma akwai ƙarancin abinci. Hakan ya sanya dole Musulmi su ka nemi wata hanya da za su kammala wannan yaƙi da su ka fara. 

A wannan lokacin ne aka nemi a samu wani sabon kwamnadan da ake ganin zai iya yin ta ta ƙare, wannan shi ne dalilin da ya sanya Manzon Allah ya zaɓo Sayyadi Ali da ya jagoranci rundunar, a yi ta ta ƙare. Kuma a wannan gumurzu ne aka ce sun yi karon batta da Ƙaura ɗan Marwana, wato Marhab bin Abi Zainab wanda aka ce uwar sa wata shahararriyar hatsabibiya ce da ta ƙware a ilimin tsafin nan na Kabbala. Kuma ita ce mai waƙar ya ke ambata a wannan faifai nasa. 

Ambatar su Sayyadi Abubakar da Umar (RadhiyalLahu Ta’ala Anhu) da ya yi, haka ya ke; sun shiga fagen yaƙi, amma sai dai ya yi ƙarin gishiri da ajino har ma da onga a waƙar. Haka kuma babu wata shaida ta cewa shi Sarkin ya na dara, abin da ya tabbata shi ne ya yi yunƙurin haɗa kai da sauran ƙabilun Yahudawa da ke Arebiya domin su yaƙi Musulunci, hakan ya sanya Musulmai su ka yi masu riga-malam-masallaci, ya yi masu ƙofar rago. 

An samu saɓani a kan waye ya yi daga da Ƙaura ɗan Marwana. Ibn Hisham ya dage a kan Muhammad Masalama ne ya kashe shi, amma sauran malaman tarihi da na hadisi duk sun ruwaito cewa Ali ɗan Abi Talib ne ya kashe shi. An ce a wannan daga sai da ya karya garkuwar Sayyadi Ali, sai wata ƙofa ya ɗauka ya yi garkuwa da ita. Sannan kuma Marhab ya yi nasarar sarar Sayyadi Ali a ka, ya zama mayaƙi na biyu da ya taɓa yi masa rauni tun bayan raunin da Amr ɗan Abi Wudd ya yi masa a yaƙin Hunain. In kuwa haka ne, to ko shakka babu wannan daga da Ali ɗan Abi Talib aka yi, ba da Muhammadu bin Maslama ba. 

To amma me ya sa Tabuka ta fi Khaybar shahara a tsakanin mutanen ƙasar Hausa?

Na farko dai saboda Musulunci bai taɓa haɗa runduna kamar wannan ba a zamanin Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam). Na biyu, Tabuka na nan har yanzu, amma Khaybar babu ita, tun bayan da Sayyadi Umar ya fasa su, ya rusa garin a zamanin mulkin sa. Na uku, sunan Tabuka ya fi kama da Hausa fiye da sunan Khaybar, saboda haka Bahaushe zai fi sabawa da ya kira sunan fiye da wancan na Larabci. Na huɗu, akwai rashin wadatar ilimin tarihi a tattare da wanda ya yi waƙar, da alama ba malami ba ne na Fiƙihu ko fannoni, kawai dai almajiri ne da ya tsinci labarin kuma abin ya ba shi sha’awa. Na biyar, irin waɗannan abubuwa ne da su ke faruwa a wurare da ilimin addini bai wadata ba. Za ka samu malaman turmi da ke yaɗa irin waɗannan labaran saboda kishin su da addini ba don su na da wani ƙwaƙƙwaran ilimi ba. 

Surar rundunar Musulunci a fagen daga (Hoto daga History of Islamic Wars, a Facebook)

Daga ƙarshe, abin da ya samu wannan waƙa shi ne dai ya samu waƙar Yaƙin Badar da aka ce Wali Ɗanmasani ne ya rubuta, domin ita ma mafi akasarin abin da aka ce an yi a ciki sun faru ne a Yaƙin Uhud ba Yaƙin Badar ba. Da wannan masana irin Malam Ibrahim Yaro Yahaya su ka musa cewa Ɗanmasani ne ya rubuta waccan waƙar, saboda sun yi nuni da cewa ilimin  Wali Ɗanmasani ya wuce a ce bai iya bambance Yaƙin Badar da Yaƙin Uhud. 

Wannan shi ne abin da na sani a game da Waƙar Yaƙin Tabuka.

* Malam Fatuhu marubuci ne mazaunin Abuja

Loading

Previous Post

Harkar rubutu ta na nan, kasuwar littattafai ce ta mutu – Zainab Lawan Briget

Next Post

Matan aure ‘yan Kannnywood sun kafa sabuwar ƙungiya

Related Posts

Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi
Addini

Baban mu Shehu Ɗahiru Bauchi ya cika shekara 98

August 2, 2022
Sheikh Ibrahim Khalil
Addini

Majalisar Malamai: Har yanzu Sheikh Ibrahim Khalil ne shugaba, inji gamayyar malaman Kano

October 12, 2021
Sheikh Ibrahim Khalil
Addini

Malamai sun bayyana tsige Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malaman Kano

October 11, 2021
Hukuncin ranar Idi
Addini

Hukuncin ranar Idi

May 12, 2021
Sama: Musulmi na sallah a Legas. A ƙasa: ƙwayoyin cutar 'Coronavirus'
Addini

Annoba, ibada da addini a arewacin Nijeriya

March 20, 2020
Ɗanfodiyo: Ƙabilanci ko Jihadi?
Addini

Ɗanfodiyo: Ƙabilanci ko Jihadi?

December 10, 2019
Next Post
Hatimin ƙungiyar

Matan aure 'yan Kannnywood sun kafa sabuwar ƙungiya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!