
ALHAJI Abdulkareem Mohammed shi ne shugaban shirya Biki Da Baje-kolin Finafinan Harsunan Gadon Afrika na Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF). A bana ma an shirya bikin kuma an yi an kammala lafiya, kamar yadda mu ka kawo maku rahotanni a kai cikin ‘yan kwanakin nan.
Mujallar Fim ta tattauna da Alhaji Abdulkareem kan yadda bikin na bana ya gudana, kamar haka:
FIM: An kammala taron KILAF 2023 kamar yadda aka saba yi a duk shekara. Ko yaya taron ya kasance?
ABDULKAREEM MOHAMMED: To, alhamdu lillahi. Wato shi wannan taron kalankuwa da mu ke shiryawa a kowace shekara kuma wanda mu ka yi karo na shida kenan aka kammala a ranar Asabar, 26 ga Nuwamba da biki da aka yi na bada kyaututtuka na gasa da aka yi na finafinan harsunan Afrika, mun yi shi ne na tsawon kwanaki biyar, wanda ranar farko, 21 ga Nuwamba, mu ka buɗe taro da kai wa fadar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ziyara tare kuma da shirya liyafar cin abinci ta maraba da baƙi da mu ka yi da daddare a Bristol Hotel.
To, bisa gayyata da mu ka miƙa wa gwamnan Jihar Kano ya kasance ya shugabancin wannan taron, amma saboda an san yanayin da shi gwamna ya ke ciki kan taƙaddamar kotu, hakan ya sa bai samu damar halarta ba. Kuma mun gayyaci manyan mutane da su ke Kano na cewa su halarci wannan liyafa ta cin abincin maraba da baƙin namu kuma mun samu halartar mutane aƙalla 140 da su ka halarta.

A rana ta biyu kuma mu ka buɗe bita da mu ke yi a kowace shekara, wanda a wannan shekara mun yi wa bitar laƙabi da “Ya za a yi a Warware Katutu Na Mulkin Mallaka Da Ya Ke Zukatan ‘Yan Afrika?” Kuma an gabatar da maƙaloli wajen guda goma sha huɗu daga mutanen da su ka fito daga ƙasashe wajen biyar. Kuma mun yi wannan bita ne da haɗin gwiwa da Tsangayar Sadarwa ta Jami’ar Bayero kuma a harabar wannan makaranta ne mu ka gudanar da taron wanda mu ka yi na kwana biyu.
Sannan a cikin waɗannan kwanakin sai aka fara wata horaswa da aka yi a kan yadda ake ilimintar da jarumai na yadda za su inganta harkar wasan kwaikwayon su. To, nan mun gayyato masana da su ka haɗa da Sani Mu’azu Galadiman Jos da sauran masu ilimi a harkar. Kuma mun samu halartar mutane daga wurare daban-daban, har daga gidan talbijin na ƙasa, NTA, da su ka shiga wannan horaswa.
A lokacin da ake wannan horaswa kuma an yi baje-koli na kayayyakin al’adu na gargajiya namu, sannan an baje-kolin abincin mu na gargajiya inda duk wani wanda ya zo taron ya yi rajista ake ba shi abincin domin ya ɗanɗana irin abincin da mu ke da shi a nan. Sannan kuma ban da abincin hatta su zoɓo da duk wata harka ta sha ko ci mun tabbatar da abincin mu ne na gargajiya mu ka bayar, don haka mu ka samar da su zogale, rama, lansir, dambu; duk irin waɗannan abubuwa saboda mu nuna masu cewa mu na da abincin mu na gargajiya.
To bayan wannan kwanaki uku da aka yi ana waɗannan shirye-shirye na koyarwa, da baje-kolin kayan gargajiya.
An shirya wasan garaya da hawan bori wanda aka yi ranar Alhamis a Gidan Ɗanhausa, wanda shi ma wani ɓangare ne na al’adun Hausa da yake neman ya ɓace, aka shirya domin nuna wa baƙin mu al’ada.

Sannan kuma ranar Juma’a aka shirya taron cin abinci da bayyana finafinan da su ka fito a matakin shiga gasar, wanda aka yi da daddare a otal ɗin Tahir, kuma manyan mutane da dama sun halarta.
Sai kuma ranar Asabar da rana aka ɗauki baƙin mu aka zagaya da su wuraren tarihi da yawon shaƙatawa da su ke cikin birnin Kano. Kuma bayan an gama aka tafi gidan shugaban ƙungiyar ACF, reshen Jihar Kano, Dakta Gwani Umar Faruk, wanda ya haɗa mana liyafar cin abincin rana a gidan sa wanda shi ma na gargajiya ne aka ci.
Sai kuma bayan nan da daddare aka shiga wajen taro na otal ɗin Bristol inda aka gudanar da bikin bada kyaututtuka ga waɗanda su ka ci gasa daban-daban. Sannan mu ka naɗa Dakta Gwani Umar Faruk ya kasance shi ne Garkuwan wannan KILAF 2023.
To, waɗannan su ne abubuwan da mu ka gudanar a taron mu na wannan shekarar.

FIM: Taron da aka yi na ƙarshe na karrama waɗanda su ka ci gasar shi ne mafi girma saboda shi ne wanda ya ɗauki mutane da yawa da su ka zo daga wurare da dama. Ko yaya ka kalli wannan taron?
ABDULKAREEM MOHAMMED: To, alhamdu lillahi, wannan ya yi armashi sosai, saboda mun samu shigowar finafinai wajen 56 daga ƙasashe 21 na duniya. Sannan kuma mun bayar da lamba ta yabo ga finafinai ta fannoni 16 na harkar shirya fim. Sannan kuma mun ware guda uku da mu ka bai wa fitattu na wannan nahiya tamu ta Afrika da su ka bayar da gudunmawa a fannoni daban-daban, musamman ma a harkar.
FIM: Idan ka duba tsawon shekaru shida da aka yi ana wannan taro, ko waɗanne irin nasarori aka samu?
ABDULKAREEM MOHAMMED:To nasara ta farko dai ita ce da ya zama wannan taron ya fara karɓuwa har ya zama na nahiyar Afrika, tun da har ta kai ƙasashe 21 sun shiga wannan taron. To, ka ga nasara ta farko kenan.
Sannan kuma shigo da finafinan, abin da na ke gani ya ƙara wa mutane ƙarfin gwiwar inganta aikin su ta yadda za su shigo da finafinai masu kyau gasar ta yadda sai ka na ganin abin da ka yi mai kyau ne sannan za ka shiga wannan gasar. Saboda haka mun saka wa masu wannan harka ɗan ba na cewar su riƙa yin abu mai inganci saboda su shigo gasar don su samu nasara. Sannan kawo mutane, don ina ganin bita da mu ka yi a Jami’ar Bayero, ina ganin babu wani taro da ake yi na harkar fim da ya ke kawo masu harkar fim da kuma waɗanda su ke koyar da harkar fim na jami’o’in mu waje guda a ce sun samu fahimtar juna. Saboda mun samu halartar farfesoshi da kuma daktoci da su ke koyar da harkar kuma sun zo sun koyar da maƙaloli. Kuma a cikin waɗanda su ka koyar mu ke fitar da wasu takardu mu buga su mu wallafa su zuwa littafi. Wannan ba ƙaramin abu ba ne, saboda zai inganta harkar. Don mu ɗin nan nahiyar Afrika akwai malaman da su ke koya mana da su ka yi jawabi kuma za mu karanta mu samu biyan buƙatar da mu ke nema. Maimakon mu yi ta kawo littattafai daga ƙasashen Turai waɗanda su ke nuna mana abubuwan da su su ke yi, sai ya zama a yanzu mu mu ke wallafa littattafan da su ke koya mana yadda ake yin harkar nan da duk wani abu da mu ke buƙata, don haka wannan ba ƙaramin abu ba ne a cikin nasarar da mu ka samu.
Sannan shigowar kamar Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation da ta ke Kaduna, sun shigo wannan lamari su na ganin cewa tunda harkar fim matasa ne su ke yin ta. Kuma su su na da sha’awar inda za su inganta rayuwa ta matasa, sai su ka ga ta yaya za su shigo a yi wannan tafiya da su. Kuma mun nuna masu cewa ya kamata a ce duk wani horo da za a yi a cikin wannan dandamali a ce sun shiga ciki sun bai wa matasan mu gurbin yadda za su ce sun ɗauki ɗawainiyar su su zo su koyi wani abu.

Ita ma haka Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) sun buɗe mana ƙofa kuma sun nuna mana sha’awar su na cewa in dai har za a sake yi nan gaba za su iya duba inda za su kawo mutane waɗanda su ke ‘yan Arewa, su ba su dama a koyar da su a irin wannan dandamali da mu ke samarwa a cikin wannan tafiya ta KILAF. To ka ga waɗannan abubuwa ne manya.
Sannan alal misali kamfanoni kamar Bankin Manoma sun shigo wannan harkar, mun nuna masu cewa mu na son mu yaɗa harkokin cin abinci kamar irin cin abincin da mu ke yi wanda shi ne su ka ba mu gudunmawa. Ka ga wannan ba ƙaramin abu ba ne ba.
Sannan akwai wani kamfani su ma da su ke harkar noma da su ka shigo wannan waje su ka bayar da abinci kyauta. Ka ga wannan ma cigaba ne saboda zai inganta harkar su, sannan kuma zai bai wa mutane damar su ɗanɗana kayan su. Ka ga sun samu kasuwa.
Akwai kuma Bankin Masana’antu da su ka nuna sha’awa. Sun zo sun duba yadda mu ke abin kuma sun gamsu da cewa abin da mu ka yi ya na da fa’ida. Su na da zummar su ma su shigo su ga yadda za su tallafa wa harkar.
To ina ganin waɗannan gudunmawa idan aka same su daga waɗannan ɓangarorin zai ma inganta abin fiye da yadda mu ke yi.

FIM: A duk shekara daga lokacin da aka gama taron ake fara shirin na gaba. Ko wannan ma haka ne?
ABDULKAREEM MOHAMMED: Wannan haka ne. Ko a yanzu ma haka ne, saboda in ka lura da abubuwan da mu ka tsara babu yadda za a ce ba a shirya masa ba a samu a yi wannan taron. Domin abubuwan da mu ka yi ba ƙaramin abu ba ne ba. Don gabatar da abu tsawon kwana biyar ana wannan ana wancan idan har ba a shirya masa ba ai babu yadda za a yi ya yiwu. Saboda haka a yanzu mun saka ɗan ba na yin taro na gaba na KILAF 2024 in-sha Allahu.
Kuma ina son mutane su gane, musamman waɗanda mu ke yin harkar fim a nan ƙasar Hausa, kamar har yanzu ba su farga da cewa KILAF ko mutum ya so ko bai so ba, KILAF wallahi wakiltar sa ta ke yi. Saboda idan harshen Hausa ya zama shi ne ya ke karɓar baƙuncin harsuna na Afirka, a ce ka na cin abinci a harkar fim, amma a ce an yi babu kai, wallahi to kash! ɗin ka, don rashin sanin ciwon kai ne. Saboda haka ina kira ga waɗanda su ke yin wannan harkar ta fim idan mutum ya na ganin cewar wannan KILAF kassara tafiyar ta zai yi don bai shigo ta ba, wallahi ƙarya ya ke yi, don ta fi ƙarfin mutum. Abin da za mu yi dole mu yi la’akari da cewa wannan abu namu ne ko mun ƙi ko mun so, saboda zummar cewa harshen Hausa zai shugabanci harsunan Afrika a yi wannan kalankuwa. To idan babu Bahaushe a ciki, wannan shi ya so.
FIM: To madalla, mun gode.
ABDULKAREEM MOHAMMED:To ni ma na gode sosai.
