SHUGABA Bola Ahmed Tinubu ya sauya membobin hukumar gudanarwa ta kamfanin mai na ƙasa, wato NNPC Limited, inda ya cire shugaban gudanarwar hukumar, Cif Pius Akinyelure, da babban jami’in gudanarwa, Malam Mele Kolo Kyari.
Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai, Mista Bayo Onanuga, ya fitar da sanarwa a yau inda ya ce Tinubu ya kuma sallami dukkan sauran membobin hukumar gudanarwar waɗanda aka naɗa tare da Akinyelure da Kyari a cikin Nuwamba 2023.
Hukumar ta ƙunshi mutum 11, waɗanda suka haɗa da Injiniya Bashir Bayo Ojulari a matsayin Babban Shugaban Gudanarwa, da Ahmadu Musa Kida a matsayin Ciyaman na hukumar gudanarwa maras cikakken iko.
Haka kuma Tinubu ya naɗa Adedapo Segun a matsayin babban jami’in kula da harkokin kuɗi na kamfanin.
Membobin Sabuwar Hukumar Gudanarwar NNPC:
Sababbin membobin kwamitin gudanarwa sun fito daga sassa daban-daban na Nijeriya:
• Bello Rabi’u (Arewa Maso Yamma)
• Yusuf Usman (Arewa Maso Gabas)
• Babs Omotowa (Arewa ta Tsakiya)
• Austin Avuru (Kudu Maso Kudu)
• David Ige (Kudu Maso Yamma)
• Henry Obih (Kudu Maso Gabas)
Baya ga haka, Babbar Sakatare a Ma’aikatar Kuɗi, Missis Lydia Shehu Jafiya, za ta wakilci Ma’aikatar Kuɗi, yayin da Aminu Sa’id Ahmed zai wakilci Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur.
Dalilin Sauyin Hukumar Gudanarwar:
Shugaba Tinubu ya aiwatar da wannan sauyi ne bisa ƙa’idar Sashe na 59, sashi na biyu na Dokar Masana’antar Fetur (Petroleum Industry Act) ta 2021, domin:
• Inganta ayyukan NNPC
• Ƙarfafa amincewar masu saka hannun jari
• Haɓaka tattalin arziki da inganta amfani da iskar gas
Sabuwar hukumar za ta gudanar da bincike kan kadarorin NNPC tare da haɗin gwiwa da wasu kamfanonin mai domin tabbatar da cewar ana samun riba mai yawa daga dukiyar ƙasa.
Tun daga 2023 ne gwamnatin Tinubu ta jawo sababbin jarin dala biliyan 17 a harkar mai da iskar gas. Sabon tsarin zai ƙara jawo jarin dala biliyan 30 kafin 2027 da dala biliyan 60 kafin 2030.
Haka nan gwamnati na da burin ƙara haƙo mai zuwa ganga miliyan 2 a kowace rana kafin 2027, sannan ya ƙaru zuwa ganga miliyan 3 a kowace rana kafin 2030.
Taƙaitaccen Bayani Kan Sababbin Jagororin NNPC:
Ahmadu Musa Kida (Sabon Shugaban Hukumar NNPC)
• Ya fito daga Jihar Borno
• Ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya
• Ya ƙware a fannin injiniyan mai kuma ya yi aiki da kamfanin Total Exploration and Production
• Shi ne tsohon shugaban ƙungiyar ƙwallon kwando ta Nijeriya (NBBF)
Bashir Bayo Ojulari (Sabon Babban Shugaba na NNPC Limited):
• Ya fito daga Jihar Kwara
• Ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a fannin injiniyan ƙere-ƙere (Mechanical Engineering)
• Ya riƙe manyan muƙamai a Shell Petroleum Development Company of Nigeria (SPDC)
• Ya kasance manajan daraktan kamfanin Shell Nigeria Exploration and Production Company (SNEPCO)
Shugaba Tinubu ya gode wa tsofaffin membobin hukumar NNPC bisa ƙoƙarin su wajen farfaɗo da matatun mai na Fatakwal da Warri, sannan ya yi musu fatan alheri a rayuwa.