GIDAN yanar TikTok ya cire bidiyoyi miliyan 2 da dubu ɗari huɗu ne da ‘yan Nijeriya suka wallafa a watanni uku na farko na shekarar 2024 saboda sun saɓa wa ƙa’idojin wallafa saƙo a manhajar.
Kamfanin, mallakar kamfanin ƙasar Chaina mai suna Bytedance, ya bayyana cewa Nijeriya tana cikin ƙasashe 50 na farko a duniya inda ake karya dokokin kamfanin a watanni 3 na farko na shekarar.
Gidan yanar ya bayyana haka a cikin rahoton sa kan ƙa’idojin wallafa wanda ya nuna cewa an soke jimillar bidiyoyi har miliyan 153 a faɗin duniya daga manhajar a ɗan tsakanin lokacin da ake magana.
Ya ce a ƙasar Amurka ne aka fi karya dokar manhajar, domin bidiyoyi miliyan 8.5 ne aka cire a lokacin.
Bidiyon da TikTok ke cirewa dai shi ne wanda ya saɓa wa ƙa’idojin tsare mutunci, kasancewa orijina, kauce wa keta mutunci, kauce wa tsiraici, kula da tsaro, kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da ta ɗabi’a, tsare mutunci, da sauran su.
TikTok suka ce a wannan tsakanin sun gano jimillar shafuka miliyan 211.5 ko dai na bogi ne ko kuma na yara ne ‘yan ƙasa da shekaru 13.
Suka ce shafukan bogi su ne suka fi yawa a cikin shafukan da manhajar ta goge. Ta goge jimillar shafuka miliyan 185.3 a manhajar.
Sannan an soke shafuka miliyan 20.5 da ake zargin na yara ‘yan ƙasa da shekaru 13, yayin da aka soke wasu shafukan har miliyan 5.6 a kan wasu dalilan waɗanda ba a bayyana ba.
![]()






