• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, May 31, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tinubu ya yaba wa Sule Lamiɗo a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa

by ABUBAKAR IBRAHIM
May 13, 2025
in Nijeriya
0
Tinubu ya yaba wa Sule Lamiɗo a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar da jawabi a taron ƙaddamar da littafin tarihin Alhaji Sule Lamiɗo a Abuja a yau

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, murna bisa ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa mai suna ‘Being True to Myself’, wanda aka yi a yau.

Shugaban Ƙasa ya bayyana littafin a matsayin muhimmin ƙari ga tarihin siyasar Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasar a wajen taron da aka gudanar a Cibiyar Taro ta NAF da ke Abuja, ya bayyana Lamiɗo a matsayin ɗan siyasa jarumi kuma mai aƙida wanda tafiyar rayuwar sa ta yi daidai da cigaban dimokiraɗiyyar Nijeriya.

Idris ya ce: “Wannan ba kawai ƙaddamar da littafi ba ne, amma bikin rayuwa da jarumtaka, daidaito, da jajircewa ga tsarin dimokiraɗiyya suka bayyana.

“Ko da yake Alhaji Sule Lamiɗo babban jigo ne a jam’iyyar adawa kuma sau da dama mai suka ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), har yanzu yana daga cikin manyan ginshiƙai na cigaban siyasar Nijeriya.”

Ministan ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya yarda da siyasar da ke bai wa kowa dama, inda ake maraba da ra’ayoyi mabambanta, kuma suna da muhimmanci ga tattaunawa kan makomar ƙasa.

“Kowane ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da dangantakar sa da jam’iyya ba, yana da gurbin zama a teburin tattaunawa kan makomar ƙasa.”

Idris ya jinjina wa ƙoƙarin da Lamiɗo ya yi na fiye da shekaru goma wajen rubuta littafin, yana mai cewa ya taka rawar gani wajen adana tarihi, kuma ya buƙaci sauran tsofaffin ‘yan siyasa da su bi irin wannan hanya.

Minista Idris tare da sauran shugabanni a lokacin da ake buga taken Nijeriya a taron

Ya kuma ce taken littafin, wato ‘Being True to Myself,’ ya dace da halayen Lamiɗo.

Ya ce: “Ya dace da halin Sule Lamiɗo da kuma sunan da yake da shi na ɗan siyasa mai aƙida da nuna ra’ayi kai-tsaye.

“Zan shawarci ɗalibai, malamai, ‘yan jarida, da sauran ‘yan siyasa da su karanta littafin don za su ga littafin yana da amfani a gare su na tsawon shekaru.”

Idris ya ƙara da cewa shi ma Shugaba Tinubu, kamar Lamiɗo, ya jajirce kan gaskiya, adalci, zaman lafiya da cigaban ƙasa.

Idris yana gai da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a taron

Ya ce: “Ɗimbin ilimi da ƙwarewar marubucin, tabbas, wata baiwa ce da ya kamata duniya ta amfana da ita, kuma abin farin ciki ne ganin ya ɗauki mataki ya wallafa littafi.”

Yayin da Nijeriya take shirin cika shekaru 26 da dimokiraɗiyya, ministan ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa – duk da yake masu tsauri ne – sun fara haifar da sakamako mai kyau a fannin tattalin arziki.

Shugabanni a taron

Ya ce: “Shin muna cewa mun kai inda ya kamata mu kai, kuma babu sauran aikin da ya rage? A’a, ko kaɗan. Abin da muke cewa mai sauƙi ne: cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna ƙarfin hali da hangen nesa na musamman wajen ɗora Nijeriya a kan hanyar cigaba da bunƙasa na gaskiya.

“Kuma, bayan wata farawa mai ɗan wahala saboda tsauraran sauye-sauyen da ba za a guje masu ba, yanzu muna shiga wani sabon zamani na samun sakamakon alheri da aka yi niyya.”

Game da matsalar tsaro, ministan ya tabbatar da cewa Shugaban Ƙasa yana aiki tuƙuru wajen kare rayuka da ƙasa daga barazanar ‘yan ta’adda.

“Don haka muna son jaddada buƙatar a yaba da sadaukarwar da sojojin Nijeriya suke yi a wannan fanni,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa sababbin dokokin haraji da Shugaban Ƙasa ya gabatar suna nufin haɓaka kuɗaɗen shiga ga gwamnatoci a matakai daban-daban ba tare da ƙara wa talakawa nauyi ba.

Shugabanni riƙe da littafin a taron

“Shugaban Ƙasa yana maraba da suka mai ma’ana a kowane lokaci, cikin ruhin ’yancin faɗar albarkacin baki da dimokiraɗiyya, amma ba zai taɓa bari a karkatar da shi daga aikata abin da ya dace da Nijeriya ba.”

Manyan baƙi daga bangarori daban-daban na siyasa sun halarci taron don girmama tsohon gwamnan da kuma yin nazari kan gudunmawar da ya bayar wajen gina dimokiraɗiyya a Nijeriya.

Tarin littafin tarihin Sule Lamiɗo a taron

Loading

Tags: littafin tarihin rayuwaMohammed IdrisShugaba Bola Ahmed TinubuSule Lamiɗo
Previous Post

Minista Idris ya ƙaddamar da yekuwar wayar da kan ɗalibai kan kafofin sadarwa

Next Post

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

Related Posts

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Minista Idris ya ƙaddamar da yekuwar wayar da kan ɗalibai kan kafofin sadarwa
Nijeriya

Minista Idris ya ƙaddamar da yekuwar wayar da kan ɗalibai kan kafofin sadarwa

May 10, 2025
Next Post
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!