TSOHON Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Alhaji Abubakar Malami, SAN, ya miƙa saƙon jaje ga jarumi Adam A. Zango kan haɗarin mota da ya yi kwanan nan.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Zango ya yi haɗarin ne a hanyar sa ta zuwa Kano daga Kaduna, inda har wata mace matashiya da ke cikin motar ta rasa ran ta.
Yanzu haka jarumin yana kwance yana jinya a wani asibitin kuɗi a Kano.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka ya fitar a yau, Malami ya ce: “Cikin matuƙar damuwa, na samu labari maras daɗi na haɗarin motar da ya ritsa da sanannen jarumin Kannywood kuma mawaƙi, Adam A. Zango, kwanan nan, wanda ya auku a hanyar Kaduna zuwa Kano.
“Lokacin da nake gudanar da aikin Hajji a ƙasar Saudi Arebiya ne aka ba ni labarin haɗarin, to da na dawo sai na ga ya dace in aiko da saƙon jaje da kuma kyakkyawar addu’a a gare ka ta samun cikakken sauƙi cikin sauri.

“Gudunmawar ka a fagen ayyukan fasaha a masana’antar nishaɗantarwa ta Nijeriya, musamman ma a Kannywood, abin matuƙar a gode a yi alfahari ne.
“Ina addu’ar Ubangiji Allah (SWT) ya ba ka lafiya da kuzari da kuma ƙarin kariya.
“Ina tabbatar maka da cewa a wannan mawuyacin lokacin, muna tare da kai tare da bada cikakken goyon baya a gare ka da iyalan ka. Kana cikin tunanin mu da addu’ar mu.”