A YAU Laraba, 20 ga Disamba, 2023 tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Fati Ladan, da mijin ta, Alhaji Yerima Shettima, su ka cika shekara 10 cur da aure.
Domin yi wa Allah godiya da ya nuna masu wannan lokaci, an yi saukar Alƙur’ani yau da safe a gidan su da ke Yarima Close a cikin rukunin gidajen Jinya Close da ke Titin Kanta a cikin garin Kaduna.

An fara gudanar da addu’o’i ga ma’auratan da kuma ƙasa baki ɗaya. Daga nan alarammomi su ka fara karatu bisa umarnin jagoran su.
An kammala saukar Alƙur’anin da misalin ƙarfe 10:40, sannan aka ƙara yin addu’o’in ƙarin zaman lafiya ga Fati da Yerima.
Bayan an gama, sai aka fito da abinci da abin sha, aka yi walima.
Da misalin ƙarfe 2:30 na rana, an yi ƙasaitacciyar walima ta ‘yan’uwa, ƙawaye, abokai da abokan arziki. Duk da cewa ba kowa aka gayyata ba, amma taron ya samu halartar ɗimbin mutane daga wurare daban-daban. An ci, an sha an gyatse.

Bayan kammala ciye-ciye da tanɗe-tanɗe, sai ma’auratan su ka yanka kek don nuna farin cikin su da Allah ya nuna masu wannan rana.
Yerima da Fati sun ba junan su kek ɗin da su ka yanka a baki.
‘Yan’uwa da abokan arziki sun taya su murna tare da yi masu addu’ar ƙara danƙon so da ƙauna.
An tashi daga taron da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.
Idan ba ku manta ba, a makon da ya gabata mujallar Fim ta kawo maku hirar da Fatin ta yi da manema labarai, inda ta ce Allah ya kashe ta a ɗakin mijin ta.
‘Yan Kannywood su ka halarci walimar sun haɗa da Abbas Sadiq, Jamilu Adamu Kochila, Zaharaddin Mando, Al-Amin Abdullahi Albani da Wasila Isma’il.
Allah ya ƙara masu zaman lafiya da danƙon soyayya.


