• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, June 5, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan da Yerima Shettima sun yi bikin sunan ɗan su

by DAGA ABBA MUHAMMAD
June 19, 2022
in Ranar Murna
0
Fati Ladan da Yerima Shettima su na rawa a wurin bikin sunan ɗan su

Fati Ladan da Yerima Shettima su na rawa a wurin bikin sunan ɗan su

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YAU Lahadi, 19 ga Yuni, 2022 tsohuwar fitacciyar jaruma Fati Ladan da mijin ta Shettima Yerima su ka shirya gagarumin taron sunan ɗan da su ka haifa a cikin watan azumin Ramadana.

An yi taron a gidan su da ke Yerima Close, daura da Jinya Close da ke Titin Kanta, a Kaduna.

Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta ba ku labarin cewa Fati ta haifi ɗa namiji a safiyar Litinin, 11 ga Afrilu, 2022 a wani asibitin kuɗi da ke Unguwar Rimi, Kaduna.

Haka kuma a ranar Litinin, 18 ga Afrilu aka raɗa wa ɗan suna Muhammad Shafi’u, amma za a riƙa kiran sa da Amir saboda sunan mahaifin baban Shettima aka raɗa masa.

Shettima na yi wa amaryar sa liƙi

A yau an fara bikin sunan da misalin ƙarfe 3:38 na rana, bayan fitowar mai jego da ƙawayen ta da kuma Shettima da tawagar sa.

Bayan an buɗe da addu’a, sai aka kira jaruman barkwanci, Yabanya da Yaɗo, su ka nishaɗantar da mahalarta taron da wasannin su masu ƙayatarwa.

Ba a ɗauki tsawon lokaci ba aka fara raba abin sha, sannan aka biyo baya da abinci kala-kala. Duk wanda ya halarci taron sunan ya ci ya sha, ya gyatse.

A haka an ci gaba da nishaɗantar da taron inda Hussaini Danko, Jamila Sadi, Auwal Fresh da sauran mawaƙa su ka ci karen su ba babbaka.

Mata mahalarta taron

Iyayenbjariri da sauran jama’a sun nuna farin cikin su a wannan rana, domin sun yi rawa sosai, kuma an yi masu kari.

Fitaccen jarumi Adam A. Zango shi ne ya nishaɗantar da taron har zuwa lokacin da aka tashi. Ya ɗauki kusan awa ɗaya ya na ɓarjewa da waƙoƙin sa.

Bikin ya ƙayatar, kuma ya samu halartar jama’a da dama daga sassa daban-daban na ƙasar nan, kasancewar dukkan su iyayen Muhammad Shafi’u masu jama’a ne.

Manyan mutane da dama sun halarci bikin sunan duk da yake wasun su ba su zauna ba. 

‘Yan fim da su ka halarta sun haɗa da Yakubu Lere, Adam A. Zango, Jamilu Adamu Kochila, Hussaini Danko, Abubakar Hunter, Abdullahi Abbas, Nasir Aminu, Ɗanladiyo Mai Atamfa, A.A. Rasheed Kabala, Sadiya Gyale, Fauziyya Maikyau, Fati Macijiya, Fati KK, Jamila Sadi, Ummulkhairi Mukhtar, Rahama Sirace, Raliya Muhammad da sauran su.

Yakubu Lere a wurin taron

A ƙarshe, Shettima ya gode wa dukkan waɗanda su ka halarci bikin, kuma ya yi wa addu’ar Allah ya maida koma gida lafiya.

An tashi daga bikin da misalin ƙarfe 6:45 na yamma.

Muhammad Shafi’u (Amir) shi ne ɗa na biyu da Fati ta haifa wa Yerima Shettima, wato har da Humaira. To Allah ya raya su baki ɗaya, amin.

Daga hagu: Sadiya Gyale, Fauziyya Maikyau da Fati Ladan
Yabanya da Yaɗo na nishaɗantar da mahalarta
Adam A. Zango (a tsakiya) tare da Hussaini Danko
Fati KK (a hagu) da Fati Macijiya
Shettima da Fati Ladan tare da ‘yar su Humaira

Loading

Tags: Adam A. ZangoBikiFati KKFati LadanFati MacijiyaHumairaHussaini DankoKadunaKannywoodMuhammad Shafi'u Amir.Sadiya GyalesunaYakubu LereYerima Shettima
Previous Post

Yadda Starlinks za su amfani Kannywood – Abdulkareem Muhammad

Next Post

Dalilin da ya sa INEC ta karɓi sunan Sanata Lawan wanda bai shiga takara ba, maimakon na Machina wanda ya lashe zaɓe – Kwamishinan Zaɓe

Related Posts

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu
Ranar Murna

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

April 25, 2025
Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 
Ranar Murna

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

April 20, 2025
Ahlan tare da 'yar sa Hassana, amaryar mako mai zuwa
Ranar Murna

Jarumi a Kannywood, Ahlan zai aurar da ‘yar sa Hassana

February 16, 2025
Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir
Ranar Murna

Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir

December 20, 2024
Mawaƙi Abdul Respect ya zama angon Hassana Abubakar
Ranar Murna

Mawaƙi Abdul Respect ya zama angon Hassana Abubakar

December 16, 2024
Next Post
Daga hagu: Ahmad Lawan da Bashir Machina

Dalilin da ya sa INEC ta karɓi sunan Sanata Lawan wanda bai shiga takara ba, maimakon na Machina wanda ya lashe zaɓe - Kwamishinan Zaɓe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!