• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Umar Bankaura ya buƙaci addu’ar jama’a saboda matsanancin rashin lafiya da ya ke fama da shi

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 20, 2022
in Labarai
1
Alhaji Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura) ... kafin ya kwanta ciwo

Alhaji Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura) ... kafin ya kwanta ciwo

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHON ɗan wasan kwaikwayon nan Alhaji Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura) ya bayyana cewa ya na buƙatar addu’a daga al’ummar Annabi saboda yanayin rashin lafiyar da ya ke ciki, wanda ya kai har an kwantar da shi tsawon lokaci a wani asibiti a Kano.

Bankaura, wanda a yanzu ake kira Yakubu Ka-Fi-Gwamna saboda rol ɗin sa a diramar ‘Kwana Casa’in’ ta gidan talbijin na Arewa24, ya na daga cikin daɗaɗɗun ‘yan wasan kwaikwayo da Arewa ke ji da su, domin ya fara dirama ne tun kafin a assasa masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.

Lokacin da wakilin mujallar Fim ya samu labarin rashin lafiyar, ya garzaya gidan sa da ke unguwar Hotoro Tsamiyar Boka a ranar Litinin, 19 ga Satumba, 2022

Daga can aka tura shi wani asibitin kuɗi mai suna Pinnacle Special Hospital da ke unguwar Hausawa kusa da Masallacin Murtala inda ya same shi a kwance magashiyan.

Wakilin mu ya ruwaito cewa da ƙyar ya gane ɗan wasan saboda yadda rashin lafiyar ya ci ƙarfin sa, ya zama kamar ba shi ba.

Daga kwance a gadon sa na jinya, Bankaura ya faɗa wa wannan mujallar cewa: “Ka zo lokacin da ba zan samu damar da zan iya doguwar magana da kai ba saboda yadda na ke a yanzu, amma na gode da zuwan ka waje na.”

Duk da haka, ya ɗan yi bayanin cewa: “Na samu lokaci mai tsawo ba ni da lafiya, domin tun a watan Ƙaramar Sallah na ke cikin rashin lafiyar.

“Kuma dai ka ga a yadda ka same ni. Kuma ina fatan ku ci gaba da yi mani addu’a; Allah shi ya san yadda zai yi da bayin sa.”

Haƙiƙa duk wanda ya san Bankaura, idan ya gan shi sai ya tausaya masa, domin ya na cikin yanayi na buƙatar taimako.

Allah ya ba shi lafiya, ya sa cutar ta zama kaffara a gare shi, amin.

Loading

Tags: Arewa 24asibitiBankauraciwodiramaHotoro Tsamiyar BokoMasallacin Murtalarashin lafiyaUmar Yahaya Malumfashi
Previous Post

Siyasa ba gaba ba ce, inji darakta Sadiq Mafiya

Next Post

Kotu ta hana beli ga matasan da ake zargi da yin zamba da ɓatanci da sunan Iman Sani Danja

Related Posts

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa
Labarai

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa

July 28, 2025
Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala
Labarai

Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala

July 28, 2025
Labarai

KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu

July 25, 2025
Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Next Post
Hajiya Mansurah Isah da Khadijatul Iman Sani Danja

Kotu ta hana beli ga matasan da ake zargi da yin zamba da ɓatanci da sunan Iman Sani Danja

Comments 1

  1. Ibrahim Sajo says:
    3 years ago

    Wace gudunmawa yan uwanshi yan film suka Bashi? Ko kuwa yanzu be da sauran amfani a wajen su saboda haka zasu kyaleshi ba tare da sun taimake shi ba? Allah ya ganar damu ya sa mu fi qarfin zuciyar mu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!