• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Waƙar gyaran Kano ta Aƙilu Aliyu

by DAGA FATUHU MUSTAPHA
April 29, 2020
in Marubuta
0
Dakta Akilu Aliyu (a hagu) da Dakta Muhammadu Uba Adamu

Dakta Akilu Aliyu (a hagu) da Dakta Muhammadu Uba Adamu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
WANNAN waƙa, mai taken ‘Zan Je Ziyarar Shugaba Dattijo Kantoma Uba’, an rubuta ta ne a cikin 1975, kuma Malam Aƙilu Aliyu yi ta ne domin wani hangen nesa da ya ga Kantoman Kano na lokaci ya yi, wato Dakta Muhammadu Uba Adamu (1935-2020). 
 
A hirar da na yi da shi Dakta Muhammadu Uba Adamu a gidan sa cikin watan Afrilu, 2020, ya bayyana mani cewa a cikin 1974 ne su ka yi tunanin kawo gyara a tsarin zamantakewar birnin Kano. A saboda haka su ka kawo wani tsari, wanda hakan ya haifar da gina manyan tituna a Birnin Kano, da yin kwalbatoci da kuma wajajen zuba shara. 
 
A lokacin ne aka yi manyan titunan da ake amfani da su har yanzu a Kano, aka kuma yi kwalbatoci a gefunan su, da kuma wajejen zuba shara. 
 
Jin daɗin wannan aiki ne ya sanya Dakta Aƙilu Aliyu ya yi wannan waƙa. Ga dai waƙar:
 
 
 
ZAN JE ZIYARAR SHUGABA DATTIJO KANTOMA UBA
 
Ta Aƙilu Aliyu
 
Ba zan shiru na kawaita ba,
In ba da na ce Rabbu ba.
 
Sarki guda ɗaya wahidi,
Ba zan taƙaita kiran sa ba.
 
Bayan faɗar Allah da gaida,
Manzo Muhammadu Mujtaba.
 
Me zai biyo bayan su ne,
Na abin nufi da ya ke gaba?
 
Haka ne akwai wani ɗan batu,
Da ba zan ƙi tunkarar sa ba.
 
Ga dai bayani ɗan kaɗan,
A taƙaice ba dungun sa ba.
 
Niyyar ziyara ce da ni,
Zancen ta yau zan bayyana.
 
Mai tambaya ya so ya ji,
Domin ya amfana gaba.
 
Manufar ziyarar wacce nai,
Maganar ta tun farko gaba.
 
Ya zuwa ina wai za ni kai
Mai tambaya bai aibu ba.
 
Zan bayyana masa ne ya ji
Ba zan yi ƙwauro gun sa ba.
 
Zan ɗau ziyara ne ni kai
Ta Kano gari ba ƙauye ba.
 
Wajen masoyi na abin
Ƙamna sahihin shugaba.
 
Shi ne Muhammadu Adamu,
Kantoma mai laƙabi Uba.
 
Dattijo ɗin nan adali,
Mai tausayin jama’a Uba.
 
Bangon tama ƙi faɗuwa,
Sha kabra garnaƙaƙi Uba.
 
Matsayin ka ɗin nan kai can-
Canta da shi Malam Uba.
 
Ilimi zalaƙa ke gare
ka da kwarjini na ƙwarai Uba.
 
Ga hattara ga hankali,
Kantoma ga hangen gaba.
 
Illimin makamar zamani
Da sanin shari’a tun gaba.
 
Ka san su ka kuma dandaƙe
Ba yau kawai ka tsire su ba.
 
Birnin Kano da wajen ta duk
Ta samu babban cigaba.
 
A wajen nizafa in ka du-
Ba ƙauyuka ba a bar su ba.
 
Balle cikin birnin fa,
Ba wai ba ne ba inke ba.
 
Kwatami cakal yau babu shi,
Shara butsa ba mu gan ta ba.
 
Sarari a hanya ya daɗu,
Albarkacin himmar Uba.
 
Duk tarkace an kauda su,
Daga ko’ina ba a bar shi ba.
 
Sababi da wane mun ka sami,
Wannan gimgimemen cigaba.
 
Mun samu kakkaifan mutum
Mai ƙoƙari ba kasa ba.
 
Gwarzon maza namijin tsaye
Inuwa ba a bisne ki ba.
 
Kantoma Muhammadu Adamu
Dattijo mai laƙabi Uba.
 
Bompai da Rimin Dada sun
Maka godiya Malam Uba.
 
Sabon Gari da Tudun Wada,
Sun gode mai daraja Uba.
 
Tarauni su da Giginyu sun
Yi yabo ga mai daraja Uba.
 
Gandu, Sharaɗa da Ɗorayi
Da Salanta, Calawa gaba.
 
Jama’ar da ke Fanshekara,
Duk sun yi sambarka Uba.
 
Waika da Jajira, Gobira
Wa, sun yi godiya Malam Uba.
 
Kurna, Fagge da Gwagwarwa,
Sun maka godiya Malam Uba.
 
Na sauka Fanisau mutan
Gama sun game da yabon Uba.
 
Ungogo, Kunya su na faɗar
Madalla-madalla Uba.
 
Wannan sadauki adali
Dattijo bai yashe mu ba.
 
Kub! Dai yawa kuwa lara bugu
Ɗaya ta mace ba ta tashi ba.
 
Ya watsa rundunar
Sauro a yau ba mu ji shi ba.
 
Ba na nufin guda da ɗai
Ban ɗaura niyyar yin ta ba.
 
Amma dalili ya saka, ni
Na yi ta ban shirye ta ba.
 
Domin saboda farin ciki
Daɗin zaman mu da kai Uba.
 
Zai sa ni ƙwalla ‘yar kaɗan,
Wataƙil ba kwa zarge ni ba.
 
Sirri na ƙoƙon zuciya
Fuska ba ta rasa jin sa ba.
 
Yururui! A yau na ranɗama
Ko dai da ban sabe ta.
 
Amma akwai magana daban,
Da ba zan iya ban yi taɓa.
 
Domin ta nai mini ƙaiƙayi,
Na zo ka sosa wajen Uba.
 
Najasa da ke yi barkatai
Haka nan butsa! An zuzzuba.
 
Ba kariya ko ‘yar kaɗan
Daga baya har ya zuwa gaba.
 
Ka ga sangamemen saurayi,
Ba ma su yara ƙanana ba.
 
Ya yaye al’aura a fi
Li bada jin kunyar sa ba.
 
Wannan abin bisa gaskiya
Ban samu jin daɗin sa ba.
 
Domin akwai illa gama
Baƙi ba za su yabe mu ba.
 
Har ma su kan zarge mu ne,
Ba wai ba ne, ba inke ba.
 
Ni na ji san da su ke faɗe,
Kuma na gwada na jarraba.
 
Ka san ni kan fita ne waje,
Zancen ga ban ƙage shi ba.
 
Wannan ta ja mini damuwa,
Na tafo ka maganta Uba.
 
Ai ya kamata ka tsawata,
Kuma kar a ƙara nan gaba.
 
Na san ka ba ka rurumi,
Kuma ba ka lalaci Uba.
 
Me maida kai ka ke mai kula,
Ga abin da duk ka saka gaba.
 
Tsuguna da tashi ba a yin ta,
A ofishin Malam Uba.
 
Ba la shiri da munafuki,
Ce-ce-ku-ce ba ka ji shi ba.
 
Kowa shigo da maganganu,
Mara sa shiri a gaban Uba.
 
Kuɗar sa zai kuwa ɗanɗana,
Daɗin karon bai ji shi ba.
 
Su kwaramniya da rigingimu,
Da hayaniya an zuzzuba.
 
Duk dai a ƙarata dole ne,
A yi gaskiya a gaban Uba.
 
Domin kurum shi kayi shi ji
Kowa abin da ya rattaba.
 
Su na daban yau zan faɗa
A gare ka yau Malam Uba.
 
Kere ka na fasa kan maƙi
Bin gaskiya ba ka san shi ba.
 
In kun tuna na ce da ku,
Guɗa ba na riƙa yin ta ba.
 
Amma fa har haka dan ku ji
Daɗi ba zai inganta ba.
 
In ban da an ware shi an
Yafa shi an more shi ba.
 
Kash! Nan wajen zan dakata
In sa alama sai gaba.
 
Ni ne Aƙilu Aliyu na
Gaishe ka mai daraja Uba.
 
Kantoma huta lafiya,
Sai lokaci wani nan gaba.
 
In Rabbana ya ƙaddara,
Mana saduwa ban mata ba.
 
Ba na yawaita maganganu,
Sai addu’a zan kattaba.
 
Ya Rabbi ya Sarki Gwani
Allah ka ja zamanin Uba.
 
Amin saboda abin biya,
Da yabo Muhammadu mujtaba.
 
Tamat bi AunilLahi mun,
Biɗi taimako nasa tun gaba.

Loading

Previous Post

Dakta Muhammadu Uba Adamu (Kantoma), 1935-2020

Next Post

Sheikh Ahmad Tijjani Tukur Yola: Ba rabo da gwani ba, kan a maida kamar sa!

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Sheikh Alhaji Ahmad Tijjani Tukur Yola ya na gabatar da waƙen yabon Manzon Allah (s.a.w.) a wajen wani taro a Kano

Sheikh Ahmad Tijjani Tukur Yola: Ba rabo da gwani ba, kan a maida kamar sa!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!