• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Wasan Sallah: Yadda mai doki ya koma kutiri

by DAGA ABBA MUHAMMAD
May 3, 2022
in Tsokaci
0
Adam A. Zango ya na wasan Sallah a ƙasar Kwatdebuwa (Cote d'Ivoire)

Adam A. Zango ya na wasan Sallah a ƙasar Kwatdebuwa (Cote d'Ivoire)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ALHAMDU lillah! A cikin hukuncin Allah da yardar sa an kammala azumin watan Ramalana lafiya, an yi Sallah lafiya. Allah ya karɓa mana dukkan ibadun mu, ya sa mu na daga cikin ‘yantattun bayin sa, amin.

A shekarun baya, ƙungiyoyin masu shirya finafinai su kan shirya bukukuwan Sallah (wato gala) kusan a kowace jiha, musamman a Kano da Kaduna. Sai dai a bana an yi Sallar lami a Jihar Kaduna, babu wata ƙungiya da ta yi yunƙurin shirya rugunɗumin Sallah duk da cewa dukkan ƙungiyoyin sun yi sababbin shugabanni.

Idan aka yi duba a shekarun baya, an yi fama da matsalolin tsaro da su ka sa gwamnati ta dakatar da kowane irin taro, hatta tarurrukan biki. Ba a Jihar Kaduna kaɗai ba, har da sauran jihohi. Haka kuma a 2020 zuwa 2021 an yi fama da dokar hana tarurruka saboda cutar korona, sai daga baya ne aka sakar wa kowa mara.

Idan ka ɗebe Kano, Kaduna ce jiha ta biyu wajen yawan ‘yan fim, kuma ta fi duk sauran jihohin shirya bikin Sallah shekaru 15 zuwa 17 da su ka gabata. Har daga Kano ‘yan fim na shigowa su shirya waɗannan bukukuwan a nan.

Su ma gidajen rediyo da talbijin irin su KSMC, FRCN, Nagarta da DITV duk su na shirya irin wannan rugunɗumi. Akwai kuma wasu ‘yan fim, irin Wassh Waziri Hong, da otal-otal irin su Hamdala waɗanda su ma su ke shirya galar Sallah. Amma duk sun daina. In dai ana maganar wasan Sallah a Kaduna, za a iya cewa a yau mai doki ya koma kutiri!

To, a ina matsalar ta ke? Ƙungiyoyin fim na Jihar Kaduna sun yi ƙaurin suna wurin maida hankali idan aka kaɗa gangar siyasar ƙungiyoyin. Da kuma an yi zaɓe, shi kenan ba za ka ƙara jin wani abu daga gare su ba har sai bayan shekara biyu, lokacin da za a fara neman takara.

Wannan ya sa shugabannin baya su ke faɗin cewa a lokacin su an fi haɗin kai. Waɗannan wasanni da ake shiryawa su na haɗa ka ‘yan fim matuƙa, domin a irin wannan wurin ne za ka haɗu da wanda ku ka daɗe ba ku ga juna ba. Wasu ma daga wasu jihohin su ke zuwa. Sannan za a yi zumunci da tattauna batutuwa na cigaban masana’antar. 

Wasan Adam A. Zango a Kwatdebuwa (Cote d’Ivoire)

Amma a yanzu wannan duk ya zama tarihi a jihar. Ka na ɗan fim sai dai ka tafi wata jihar galar Sallah ko da ko ba a gayyace ka ba, don in ka zauna a Kaduna sai dai ka yi ta yawo a gari babu wurin zuwa.

Yau ga shi a Kano wata sabuwar ƙungiya ta shirya rugunɗumin Sallah har na tsawon kwana bakwai. Wasu jaruman sun tafi wasu ƙasashe irin su Kwatdebuwa (Cote d’Ivoire), Nijar da sauran su, wasu kuma sun tafi wasu jihohin irin su Gombe, Neja da sauran su. 

To wai ina sababbin shugabannin da aka zaɓa tun daga Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai (MOPPAN) reshen Jihar Kaduna da sauran ‘guilds’ na furodusoshi, jarumai, daraktoci da sauran su? Dukkan su a yayin yaƙin neman kujerun da su ka yi sun ɗauki alƙawarin samar da haɗin kan waɗanda su ke jagoranta. Amma tun bayan da aka zaɓe su har zuwa bayan rantsar da su, ban da maganar shirya bukukuwan Sallah, ta kowane ɓangare ba su motsi.

A jiya na haɗu da ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a Kannywood, kuma fitaccen darakta kuma ɗan jarida. A tare da shi akwai ɗaya daga cikin maitaimakin sabbin shugaban ɗaya daga cikin ƙungiyoyin Jihar Kaduna. Sai mu ke maganar batun wasan Sallah a Kaduna. Ya ce mani, “Yanzu haka da mu ka fito mun rasa wurin zuwa ne, tunda yanzu an daina wasan Sallah a Kaduna.”

Ya ƙara da cewa, “Ai wannan ma labari ne. Ya kamata ka yi rubutu a kan wannan, tunda ga ɗaya daga cikin shugabannin ma har yanzu ba su yi wani motsi ba. Amma a baya sai ihu su ke yi a kan a canza shugabanni.”

Nan take maitaimakin shugaban ya fara maganar cewa kada a yi masu haka, za su yi aiki, yanzu su ka fara. Ya na magana har da zufa. 

Sai daraktan ya ce, “Ai in ba haka ake yi maku ba, babu abin da za ku yi har lokacin saukar ku ya yi. Mu na ji mu na gani Kanawa sun ƙwace mana wasan Sallah!”

Wannan ne ya ƙara jan hankali na na yin wannan rubutu. Mu na jira ga hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar shirya finafinai ta Jihar Kaduna da su yi dukkan ƙoƙarin su don ganin sun dawo da martabar masana’antar ta kowane ɓangare. 

Wasanin Sallah da ake shiryawa, mutane da dama na amfana da shi. Sannan kuma ya na ƙara kusanta jarumai da masoyan su.

Loading

Tags: Eid el-Fitrgalaguildshaɗin kaiKadunaKanoKwatdebuwaMOPPANNijarwasan Sallah
Previous Post

Cewar Gidan Dabino: MOPPAN reshen Kano za ta yi fim zakaran gwajin dafi wanda zai shiga duniya

Next Post

Sarkin Bichi zai naɗa Fatima Lamaj Jakadiyar Matasan Nijeriya

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post

Sarkin Bichi zai naɗa Fatima Lamaj Jakadiyar Matasan Nijeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!