WANI mutum mai suna Bala Musa ya maka fitacciyar jarumar Kannywood Hadiza Gabon a kotun shari’ar Musulunci a Kaduna bisa zargin ta yaudare shi ta ci masa kuɗi a kan za ta aure shi.
Mutumin, ɗan shekara 48, ya maka jarumar a kotun ne bisa laifin yaudarar ma’aikacin gwamnati.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an fara zaman sauraron ƙarar ne tun a ranar 23 ga Mayu, 2022 amma ita Hadizar ba ta je kotun ba.
A zaman da aka yi a yau Litinin, 6 ga Yuni, 2022, mai ƙarar ya bayyana wa kotu cewa sun kwashe tsawon lokaci su na soyayya da jarumar, har ta kai ga sun yi alƙawarin yin aure a tsakanin su kuma ta aminta da haka.
Bala Musa ya ƙara da cewa, ”Haka jarumar ta yi ta sa ni ina yi mata hidima a duk lokacin da ta ke da buƙata ba tare da tunanin abin da zai je ya dawo ba, domin kuwa na gama yarda da za mu yi aure, wanda zuwa yanzu na kashe wa jarumar zunzurutun kuɗi kimanin naira 396,000.”
A cewar sa, ”Haka kuma jarumar ta kauce wa haɗuwar mu a garin Gusau da ke Jihar Zamfara, inda a nan na ke da zama, bayan na gama dukkan wani shiri da ya kamata.”
To sai dai a nata ɓangaren, Hadiza Gabon ta musanta zargin, ta ce tun da fari ba ta ma tabbatar da sahihaccin sammacin da aka kai mata ba, shi ya sa ba ta bayyana a gaban kotun ba.
Lauyan ta, Mubarak Kabiru, wanda ya wakilce ta, ya ce, ”Duba da irin shaharar wadda na ke karewa, ta na haɗuwa da mutane daban-daban masu wata manufa ta daban. Ita mace ce mai tsantseni da kula domin samun kariya da tsaro.”
Lauyan ya roƙi kotun da ta ba shi lokaci domin ya gabatar da wadda ake ƙara a gaban kotun.
Mai Shari’a Malam Rilwanu Kyaudai ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 13 ga Yuni, 2022.