JARUMA a cikin shirin ‘Kwana Casa’in’, Saratu Abubakar, wadda aka fi sani da Hajiya Ƙarama, ta bayyana cewa ɗaukakar da ta samu a harkar fim ta mayar da rayuwar ta a matsayin wata irin rayuwa ta daban da wadda ta saba.
Jarumar ta bayyana haka ne a lokacin tattaunawar ta da mujallar Fim a game da yadda ta samu kan ta bayan ta samu shahara a duniya.
Saratu ta ce, “Haƙiƙa, yanzu a yadda na ke rayuwa gaskiya sai a hankali, saboda babu yadda za a yi na fita ba tare da na rufe fuska ta ba, saboda ina fita da an gan ni wasu za su ce La!! Ga Hajiya Ƙarama ta ‘Kwana Casa’in’.
“To, gaskiya abin ya na ya jawo mani ba na zama cikin natsuwa a cikin mutane. Ni yanzu zan iya zuwa waje kuma can an jima ka neme ni ka rasa saboda ma kafin a tara mani jama’a na gudu.

“Ni da ma can a tsari na ba mai yawan shiga jama’a ba ce saboda ba na son hayaniya, don ko kasuwa na shiga, to hayaniyar kasuwa ta kan sa kai na ya yi ciwo. Sai ya zama na samu kai na a cikin harkoki na jama’a.
“Yanzu ka ga a baya da ba a san ni ba idan ina tare da mutane sai na saki jiki na yi ta hira da mutane, na shiga kasuwa babu ruwa na har waɗanda na ke sayen kaya a wajen su komai cikin sauƙi na ke yi a baya. Amma waccan rayuwar da na ke yi a baya ta zama tarihi.
“Ko a cikin satin nan da na shiga cikin kasuwa, na rufe fuska na saka baƙin tabarau, to akwai turaren da zan saya, sai na cire abin rufe fuska ta. Sai kawai wanda zan sayi kayan a wajen sa, ya ce, ‘Ashe jaruma ce ta shigo mana shago!’ Ai kuwa kafin wani ɗan lokaci jama’a su ka fara taruwa, dole sai sauri na yi na bar wajen saboda yadda aka rinƙa cewa Hajiya Ƙarama, sai mutane su ka cika wajen.
“To gaskiya haka na ke rayuwa a yanzu, saboda ita da man ɗaukaka ta gaji hakan, don haka yadda za ka yi mu’amala a baya, to idan ka samu ɗaukaka hakan ba za ta yiwu ba.”
Jarumar ta ci gaba da cewa: “A yanzu ko makaranta da na ke yi yanzu da yake ina yin karatu a BUK ina karantar harshen Ingilishi, to wallahi ni kaɗai na san abin da na ke gani, saboda kullum idan na shiga mutane za su yi ta kallo na, duk da mun saba da wasu amma daga na shigo aji hankalin kowa a kai na ya ke.
“To duk da haka ina alfahari da wannan baiwa da Allah ya ba ni. Kuma ina kira ga duk wanda ya samu kan sa a irin wannan yanayi to kada ya rinƙa girman kai ko wulaƙanta mutane, domin kuwa wata daraja ce da ba kowa Allah ya ke yi wa arzikin ta ba.”

Saratu Abubakar dai ‘yar asalin garin Gauraka a yankin Suleja ta Jihar Neja ce. Ta shigo harkar fim a cikin 2014, inda ta fara da fim ɗin ‘Hajiya Babba’, amma a yanzu an fi sanin ta da jarumar ‘Kwana Casa’in’, ko kuma fim mai dogon zango ɗin nan ‘Zo Mu Zauna’, wanda ake sakawa a YouTube.
Comments 1