ALLAHU Akbar! A daren Asabar, 30 ga Satumba, 2023 Allah ya ɗauki ran Malama Sabira, matar furodusa kuma ɗan kasuwa a Kannywood mazaunin Kaduna, Alhaji Rabi’u Koli.
Sabira Ishaq Koli ta rasu da misalin ƙarfe 11:00 na dare a wani asibitin kuɗi mai su na Manal da ke Kawo, Kaduna, sakamakon jinyar kwanaki bakwai da ta yi.

Marigayiyar, mai kimanin shekara 43 a duniya, ta rasu ta bar mijin ta da kuma ‘ya‘ya shida.
An yi jana’izar ta da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Lahadi a gidan mijin ta da ke Layin Darma a unguwar Rafin Guza, Kaduna.
Idan kun tuna, watanni huɗu da su ka gabata mujallar Fim ta ba ku labari cewa Alhaji Muhammad Rabi’u Koli ya aurar da ‘yar sa ta farko, wato Hafsat (Ummi), a ranar Juma’a, 26 ga Mayu, 2023.
To Ummi ita ce babbar ɗiyar marigayiya Sabira, wadda Allah ya yi za ta ga auren ta kafin ta koma ga Mahaliccin ta.
Allah ya yi mata rahama, ya albarkaci dukkan abin da ta bari, amin, amin.