YAU saura kwana biyu shahararren mai ba da sutura kuma jarumi a Kannywood, wato Sadiqu Artist, ya zama angon Amina Aminu (Hajiya).
Kamar yadda yawancin ‘yan Kannywood su ke yi, shi ma angon da amaryar tasa sun yi hotunan kafin aure (pre-wedding pictures) da su ka ƙayatar da masoyan su da abokan sana’ar Artist.
Duk inda ka leƙa a soshiyal midiya, hotunan ake yaɗawa.

Mujallar Fim ta lura da cewa hotunan kafin auren Sadiqu da na mawaƙi
Adamu Mohammed Turaki (A. Wamba) da amaryar sa Hadiza Hassan Galadima, wanda a yi bikin auren su a Fabrairu, sun fi ɗaukar hankalin mutane a Kannywood a cikin wannan shekarar.
