MAWAƘIN nan Sanusi Ɗahiru, wanda aka fi sani da Sanusi Pambeguwa, ya yi bayani kan yadda ya gamu da ibtila’in rasuwar ‘ya’yan sa biyu a wani haɗari maras daɗin ji.
Mutuwar Khaleed da Tasi’u, yara ‘yan shekara biyar da haihuwa, ta faru ne jiya Lahadi, 3 ga Oktoba, 2021, a cikin motar sa da ya yi fakin a ƙofar gidan sa da ke garin Pambeguwa, a Ƙaramar Hukumar Kubau cikin Jihar Kaduna.
A lokacin da ya ke yi wa mujallar Fim bayani dalla-dalla game da yadda wannan abin baƙin ciki ya faru, Sanusi Pambeguwa ya ce, “Na dawo daga Zariya da misalin ƙarfe 11:30, mun yi taro a daren Asabar, na dawo gida Lahadi, na yi fakin mota ta a ƙofar gida. Yayan su sai ya zo ya karɓi biredin da ayaba da na sawo masu.
“Da su ka shiga gida sai su ka gan ni. Ni kuma da ma taron da mu ka yi na dare ne, bacci ya kama ni sosai, ban samu damar kwanciya da wuri ba. Ina zuwa, da na aje kaya sai na kwanta bacci.
“Bayan an raba masu biredin, sai su ka fita waje. Sai ɗayan yaro na ya buɗe ƙofar motar, kamar yadda wani bawan Allah maƙwabcin mu na kusa da mu ya ke faɗa, yaron ya zo shagon mu ya na faɗa wa ɗan’uwan sa cewa, ‘Baban mu ya bar mota a buɗe, zo mu je mu shiga.’
“Allah cikin ikon sa, ina tunanin bayan sun shiga motar ne sai su ka danna wannan kilif ɗin, sai motar ta rufe baki ɗaya, kuma ban sauke gilashin motar ba.
“Ni kuma saboda gajiya, ina kwanciya bacci ya ɗauke ni, ban tashi ba sai wurin ƙarfe 3:30 na yamma.
“Bayan na tashi, na yi wanka na fita kasuwa. Da ma kuma ban sa a rai na zan sake fita da motar ba.
“Daga baya, mata na su ka kira ni su ka ce mani ba a ga yara ba. Sai na ce masu ai yara za su ɓata ba, wataƙila sun bi ‘yan’uwan su zuwa makaranta ne.
“Can daga baya, sai babban yaro na ya leƙa cikin motar, sai ya gan su, sai ya ke cewa ai ga su can a cikin mota su na bacci.
“Allah da ikon sa, ana buɗe motar sai aka gan su sun rasu. Kuma an gano su a cikin motar ne da misalin ƙarfe 4:30 zuwa 5:00 na yamma.
“Dukkan su ‘ya’ya na ne. Tsakanin su kwana bakwai; ranar sunan Khaleed aka haifi Tasi’u. Shekarun su huɗu zuwa biyar, ba su cika biyar ɗin ba. Mata na biyu, ‘ya’ya na goma.”
A binciken da mujallar Fim ta yi, ta gano cewa irin wannan haɗarin na yara su shiga mota ba a sani ba har su mutu ya na yawan faruwa a ƙasar nan.
Kwanan baya a Tudun Wada, Kaduna, ‘ya’yan wani mutum su ka shiga motar maƙwabcin su, su ka kasa fitowa, sai daga baya aka ga gawarwakin su a ciki bayan an sha cigiya.
A Kano a wata shekara kuma wani Inyamiri ɗan kasuwa ya bar motar sa ƙirar Baswaja a ƙofar gida, yaron maƙwabcin sa ya buɗe ya shiga, ya mutu a ciki ba a sani ba.
An yi ta neman yaron tsawon kwana biyu kafin a ji wani wari ya na fita daga cikin motar. Ana buɗewa, aka gan shi a kumbure a ciki.
Matasan unguwa sun so su kashe Inyamirin a bisa zargin wai matsafi ne, amma uban yaron da dattawan unguwa, waɗanda Hausawa ne, su ka hana domin Inyamirin mutumin kirki ne, har dai ‘yan sanda su ka zo su ka fitar da shi daga unguwar.
Ba kawai mota ba, wakilin mu ya gano cewa akwai abubuwa da dama da ke zama sanadiyyar rasa ran yara ƙanana. Misali, akwai wata yarinya da ta taɓa shiga cikin dif-firiza, aka neme ta sama da ƙasa ba a gan ta ba, kuma an ga takalman ta a bakin firiza ɗin amma babu wanda ya kawo a ran sa cewa ta na ciki. Sai daga baya da aka buɗe firizar aka gan ta a ciki har ta yi ƙanƙara.
Allah ya jiƙan Khaleed da Tasi’u da sauran shahidai irin su, ya sa masu ceton iyaye ne. Allah ya ba iyayen su haƙurin rashin su, amin.