TA dai tabbata an cire sunan mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) a cikin ayarin kwamitin kamfen ɗin ɗan takarar zama shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Da ma a cikin sabuwar waƙar sa mai taken ‘Lema Ta Sha Ƙwaya’, akwai baitin da ya ke cewa, “Ka ce a cire suna na wannan na ji, / Da ma ban ce a saka ni ba inda ka ji, / Duk wani taro da ka ke don ni to na ji, / Mu harkar Tinubu ba sai da takarda ba.”
Tun bayan da ya saki waƙar ake ta ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, masoyan sa kuma na ɗaukar daidai wannan baitin su na yin gajeren bidiyo su na wallafawa a shafukan su.
A wani ɓangaren, kuma wasu daga cikin abokan sana’ar sa su na ta murna da jin maganar. Amma kuma ce-ce-ku-ce bai yi ƙamari ba sai da aka fitar da sabon jerin sunayen ‘yan kwamitin babu sunan Rarara ɗin a ciki, sai sunan Abdul Amart, shi ɗin a matsayin memba ba tare da muƙami ba.
A cikin ayarin sunayen na farko da aka fitar, wanda mujallar Fim ta ba da labarin, Rarara ne jami’in gudanarwa (admin officer), sai dai kuma a wannan karon da aka cire shi sai aka mayar da muƙamin sa zuwa kudu, aka ba wata mai suna Eberechukwu Chidera Eberechi daga Jihar Inugu.
Wasu daga cikin ‘yan Kannywood murna su ke ta yi don a cire Rarara a cikin ayarin, ba su duba illar da aka samu na rasa muƙamin sa da aka mai da Kudu ba. Wasun su kuma su na murnar ne domin an cire shi an saka Abdul Amart.
An ɗauki tsawon lokaci a Kannywood ana ce-ce-ku-ce kan cewa da Rarara da Abdul Amart ba su shiri. An samu rarrabuwar kai a masana’antar tun bayan kafa ƙungiyar YBN Network Group da kuma ƙungiyar 13×13 Movement, inda kowa ya ɗauki ɓangaren sa.
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa an cire Rarara ne saboda a yanzu ba ya goyon bayan jam’iyyar APC a Jihar Kano.
Tun bayan bayyanar sabon jerin sunayen, Rarara bai ce uffan ba. Hasali ma ya na Gombe tare da jama’ar sa na ƙungiyar 13×13 Movement su na ɗaukar sababbin waƙoƙin sa irin su waƙar ‘Jagaba Shi Ne Gaba’, ‘Lema Ta Sha Ƙwaya’, waƙar gwamnan Gombe, da wasu waƙoƙin haɗaka da su shi da sauran mutanen sa, ya bar masu surutu su na yi.
Rarara dai ya bar APC a Jihar Kano ne bayan da ya miƙa buƙatar sa ta a ba wasu daga cikin abokan sana’ar sa takara, saboda su ma a ba su dama, don da su mawaƙan ake amfani wurin cin zaɓe. Waɗanda ya ke so a tsayar su ne Aminu Ala, Abale da Naziru Ɗanhajiya.
Sai dai kuma sun ƙi amincewa da buƙatar tasa, inda shi kuma ya koma goyon bayan ɗan takarar zama gwamnan Kano, Malam Sha’aban Ibrahim Sharaɗa na jam’iyyar ADP. A nan ne kuma abokan sana’ar sa irin su Ala, Daddy Hikima, Ɗanhajiya da sauran su su ka samu damar yin takara a jam’iyyar.
Ganin hakan ta faru ya sa shi kuma Abdul Amart ya samu damar kutsawa wurin su Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ɗan takarar zama gwamnan Kano na APC, wato Dakta Yusuf Gawuna.
A halin yanzu Rarara ba ya cikin kwamitin kamfen na Tinubu, amma kuma akwai wasu na kusa da shi na ƙut da ƙut a cikin membobi, irin su Yusuf Haruna (Baban Chinedu) da A’isha Ahmad Idris (Ayshatulhumaira).
A wannan karon dai akwai irin su Ado Isa Gwanja, Sadiq Sani Sadiq, Sadiq Mafiya da sauran su.
Tun farko an ba Sani Idris Kauru (Moɗa) matsayin dattijo (elder) na Kaduna; Jadda Garko, mataimakin darakta (co-deputy director), Nuhu Abdullahi, mataimakin jami’in walwala (assitant welfare officer) na Kano, shi kuma Isma’il Na’abba Afakallahu mataimakin darakta (deputy director) na Kano.
![]()






