• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda Starlinks za su amfani Kannywood – Abdulkareem Muhammad

by DAGA ABBA MUHAMMAD
June 19, 2022
in Labarai
0
Alhaji Abdulkareem Muhammad

Alhaji Abdulkareem Muhammad

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BABBAN furodusa a Kannywood kuma shugaban kamfanin shirya finafinai na ‘Moving Image’ da ke Kano, Alhaji Abdulkareem Muhammad, ya bayyana cewa majalisar shirya finafinai cikin harsunan gado da ke Inugu mai suna ‘Starlinks Movie Africa’ za ta iya amfanar masana’antar Kannywood ta hanyoyi da dama.

Alhaji Abdulkareem, wanda kuma shi ne shugaban masu shirya biki da kasuwar baje-kolin finafinan da ake shiryawa cikin harsunan gado na Afrika a Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF), ya bayyana haka ne yayin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim kwana kaɗan bayan an naɗa shi a matsayin uba kuma ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na majalisar.

Sanarwar naɗin nasa ta fito daga shugaban ‘Starlinks Movie Africa’, wato Ambassador Vitus Ekpechi Prince, inda ya ce da Turanci: “Special Announcement. Good morning distinguished creative colleagues. This is to inform the General Assembly that Comrade Abdulkareem Mohammed, a veteran filmmaker and Managing Director, Moving Image Limited, Kano, the founder/CEO, Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival (KILAF), has been appointed the Patron/Board of Trustees member of Starlinks Movie Africa. Congratulations, sir.”

Lokacin da mujallar Fim ta taya shi murnar wannan naɗi da aka yi masa, furodusan kuma darakta ya amsa da cewa: “Ina matuƙar godiya ga mujallar Fim, wadda ta zama zakaran gwajin dafi na mujallun fim na Kannywood. Ku ma ina maku murna da jinjina maku saboda yadda ku ka jajirce a kan wannan aiki naku mai mahimmanci da kambama masana’antar Kannywood. Allah ya ƙara maku ƙarfin gwiwa da nasara.”

Da wakilin mu ya nemi ƙarin haske kan ainihin abin da ‘Starlinks Movie Africa’ ke yi da kuma yadda za su amfani Kannywood, sai furodusan ya ce, “Starlinks Movie Africa’ wani sabon dandamali ne wanda aka kafa shi domin bunƙasa harkokin yin fim a nahiyar Afrika. Ya na da ofishin sa a garin Inugu kuma ya na ƙarƙashin shugabancin wani matashi mai suna Ambassador Vitus Ekpechi Prince. 

“Dandamalin na da manufar bunƙasa harsunan Afirika da al’adun ta da shirye-shiryen finafinan ta. A bisani ma dai har sun buɗe kafar YouTube domin cimma waɗannan manufofin. Su na da zummar bijiro da kafofin taimaka wa waɗanda ke sha’awar shiga masana’antar fim da nishaɗantarwa a duk faɗin nahiyar Afrika. Kuma su na son fito da filin baje-kolin finafinai da bada lambobin yabo, watau ‘film festival and awards’, a duk faɗin Afrika.

“A gani na, manufofin nan da su ka ayyana, za su iya amfanar masana’antar Kannywood domin kuwa ita ma a nahiyar Afrika ta ke. A gaskiya ma, Kannywood ce ta cancanci jagorar irin wannan ƙudiri saboda masana’antar ta na kan gaba a wannan nahiyar tamu.”

Mashirya fim da dama sun taya Abdulkareem murnar wannan naɗi da aka yi masa. Majalisar Dattawan Kannywood, wato ‘Kannywood Foundation’, ta taya shi farin ciki a cikin sanarwar da ta bayar ta hannun Alhaji Kabiru Maikaba, inda ta bayyana cewa, “Wannan abin farin ciki ne, abin alfahari gare mu da duk wani ɗan Kannywood. ‘Yan wannan majalisa na taya shi da duk ‘yan wannan masana’anta murna. Kuma mu nai masa fatan Allah yai masa jagora, Allah ya sa ya kasance sanadiyyar kyautatuwar al’amurra a wannan masana’anta, ya kuma kasance dalilin kyautatuwar danƙon zumunci tsakanin wannan masana’anta da wannan babban kamfani.”

Mujallar Fim ta tambayi Alhaji Abdulkareem abin da zai ce  kan taya shi murna da ake ta yi kan wannan naɗi. Sai ya amsa da cewa, “To, babu abin cewa fiye da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da kuma duk waɗanda su ka taya ni murna. Wannan naɗi ya ƙara mani ƙarfin gwiwa ƙwarai da gaske saboda ya hasko mani wani sabon shafin rayuwa ainun. 

“Ban taɓa tsammani cewa wasu da ke Enugu sun saka ni a ma’auni ba tare da sani na ba, har su ka ga cancanta ta ta wannan naɗi. 

“Kuma kafa ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF) da na yi shekaru huɗu da su ka gabata na ɗaya daga cikin abubuwan da su ka duba domin su ga cancanta ta, kuma su ka nuna mani cewa hakan ne ma ya sa su ka samu ƙarfin gwiwar yin abin da su ke yi. 

“Saboda haka, babu abin cewa fiye da godiya ga Allah da duk waɗanda su ka taya ni murna duk da cewa nasarar tamu ce baki ɗaya.

“Godiya ta musamman ga mujallar Fim da ta ga dacewar tattaunawa da ni game da wannan naɗi. Allah ya ƙara mana zumunci da ƙaunar juna.”

Loading

Tags: Abdulkareem MuhammadfilmsKabiru MaikabaKannywoodKannywood FoundationKano Indigenous Languages of Africa Film MarketKILAFMoving Image LimitedStarlinks Movie Africa
Previous Post

Hotunan bikin Lilin Baba da Ummi Rahab (2)

Next Post

Tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan da Yerima Shettima sun yi bikin sunan ɗan su

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Fati Ladan da Yerima Shettima su na rawa a wurin bikin sunan ɗan su

Tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan da Yerima Shettima sun yi bikin sunan ɗan su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!