KWANAN nan aka riƙa yaɗa hotunan fitaccen jarumi, mai fitowa a matsayin uba a finafinan Hausa, wato Alhaji Balarabe Jaji, tare da faɗin cewa wai ya yi haɗarin mota tare da ‘ya’yan sa sun rasu. Hakan ya sa mujallar Fim ta bazama don gano gaskiyar lamarin.
Wakolin mu ya yi dacenganawa da Balarabe Jaji, ya yi masa zancen da ake yaɗawa. Shi kuma ya yi bayani kan gaskiyar abin da ya faru.
Alhaji Balarabe Jaji ya ce: “Magana ta gaskiya, haɗari ne ‘ya’ya na su ka yi tare da ƙane na a kan hanyar su ta komawa Jaji daga Kaduna, inda su ka je taron saukar karatun Alƙur’ani. Mun rasa yara huɗu, shida na Asibitin Barau Dikko a karairaye.
“Waɗanda su ka rasu ɗin akwai Maryam, Binta, Sa’adatu, sai Sulaiman.
“Wannan iftila’i ya auku ne a ranar Asabar, 26 ga Fabrairu, 2022 da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.”
Da wakilin mu ya tambayi Alhaji Balarabe abin da zai ce gane da wannan iftila’i da ya same shi sai ya amsa da cewa, “Duk abin da ka ga Allah ya tsara, haka ya ke zuwa, don Allah ba ya kuskure. Tun daga lokacin da ya fara halitta, ya tsara zai faru, kuma ga ta yadda abin zai faru, kuma inda zai faru. Kowane ɗan’adam ya na da adadin sa. Duk yadda abu ya zo, a karɓe shi yadda ya zo, kuma a karɓe shi cikin imani, domin ba mu da wani tsimi kuma ba mu da wata dabara.
“Saboda haka daga Allah mu ka zo, kuma ga Allah za mu koma. Don haka mu na fatan dukkan mumini mai imani ya samu kyakkyawar cikawa da imani.
“Yara dai mu na kyautata masu zaton cikawa da imani, domin su na kan hanyar su ne sun je sun yi zumunci da ‘yar’uwar su, ta samu damar kammala karatun Alƙur’ani su ka je su ka cimma wannan addu’a, aka yi addu’a tare da su, wurin dawowa su ka haɗu da wannan iftila’in.
“Saboda haka waɗanda Allah ya yi masu cikawa, Allah ya sa sun yi cikawa na imani. Kuma a cikin su, kamar Sulaiman shi sati huɗu kenan da ya kammala hajamar Alƙur’ani, ya yi sauka a Islamiyyar su da ke nan Jaji. Ka ga kuma ya ziyarci ‘yar’uwar sa ita ma a saukar ta.
“Mu na addu’ar Allah ya ba mu haƙuri. Kuma jaruman mu da ma’aikatan mu na ‘yan fim, waɗanda su ka jajanta min da waɗanda su ka ziyarce ni Allah ya saka masu da alkhairi.
“Sannan ina jan hankali da duk lokacin da mutum zai yi ‘posting’ a kan wani abu a soshiyal midiya, ina roƙon al’umma da Allah da su daure su riƙa bincike kafin su yi. Haka masu karatu, su riƙa karanta abin da aka yi ‘posting’ kafin su yanke hukunci.
“Haka ku ma ‘yan jarida, don Allah ku riƙa bincike kafin ku bada labari, saboda ku bada labari na gaskiya. Ba daidai ba ne abin da ba a yi bincike ba a je a shiga yaɗawa. Ka san kalma ɗaya za ta iya fusata Ubangiya ya azabtar da bawa. Domin ɗan wani abu kaɗan da ka ke ganin ba komai ba ne zai iya wadatar da Allah (s.w.t.) ya ce gafara da shi.
“Na yi mamakin yadda nan take wasu su ka ɗora a soshiyal midiya cewa ni na je na yi haɗari, kuma har yara huɗu sun rasu tare da ni. Gaskiya wannan abu ya sa ni damuwa. Mu na cikin alhinin abin da ya faru, amma mu na ta shan wayoyi daga ko’ina, gida da wajen ƙasar nan cewa na rasu. Ka ga wannan ba daidai bane. Don haka kafin mutum ya bada labari, ya yi bincike. Wannan shi ne.
“Don Allah ku miƙa mana godiya ga mutanen masana’antar mu maza da mata, yara da manya, waɗansu sun taso da kan su sun zo min ta’aziyya, waɗansu sun kira, wasu sun yi addu’o’i daban-daban a wurare daban-daban.
“Saboda haka babu abin da za mu ce sai dai mu yi fatan Allah ya sa mu cika da imani.”