• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Yan Kannywood sun yi tir da kalaman Ummah Shehu

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
August 24, 2021
in Labarai
0
‘Yan Kannywood sun yi tir da kalaman Ummah Shehu
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WASU daga cikin membobin masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood sun yi Allah-wadai da wasu kalamai da  jaruma Ummah Shehu ta yi a kan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.

Ƙungiyar Jaruman Hausa ta Nijeriya (Hausa Actors Guild of Nigeria), reshen Jihar Kano, da fitacciyar jaruma Fatima Isah Muhammad (Teema Makamashi) sun barranta kan su da kalaman da Ummah ta yi.

Idan kun tuna, Ummah Shehu ta zargi cewa wasu daga cikin jami’an hukumar su na neman mata, amma sai su je su na musguna wa mata marasa ɗaurin gindi irin su Sayyada Sadiya Haruna.

Tuni dai hukumar ta buƙaci Ummah ta je Kano ta kare kan ta kan wannan iƙirarin nata, sannan kotu ta .

A martanin da ya yi ga wannan taƙaddama, shugaban Ƙungiyar Jaruman Hausa, Malam Alhassan Aliyu Kwalle, ya faɗa a cikin wani bidiyo da ya saki cewa, “A madadi na  da manyan jarumai maza da mata da matsaƙaita, ƙanana masu tasowa, mu na amfani da wannan dama mu nuna alhini, wato mu na nuna takaicin mu, da barranta, ma’ana da ƙyamar wasu kalamai da wata jaruma mai suna Ummah Shehu ta gabatar ga Hukumar Hisbah.”

Kwalle ya ce, “Haƙiƙa wannan kalamai, kalamai ne wanda mu a tunanin mu da lissafin mu ba da Hukumar Hisbah ake ba, magana ce ake ta addini, saboda ita dai wannan hukuma ce wacce a kowace jahohi namu na Musulmai na Nijeriya aka kafa su domin umarni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna.

“Ka ga kuwa taɓa wannan hukuma abu ne wanda ya ke akwai ganganci da kuskure a ciki. 

“Saboda haka, mu na takaici, mu na kuma Allah wadarai da wannan furuci da wannan baiwar Allah ta yi.”

Kwalle ya ce ya na so mutane su gane cewa, “Akwai fa mutane da yawa wanda su na cikin wannan masana’anta su na gabatar da abubuwa a matsayin su na ‘yan wannan masana’anta, wanda mu kuma gaskiya ba ma tunanin cewa ‘yan’uwan mu ne ‘yan wannan masan’anta domin duk mutumin da bai san darajar ya bin ƙa’idoji wanda ƙungiyoyin mu irin na su MOPPAN, irin su Arewa da ƙungiyar mu ta jarumai kan ɗora mutane a kai, to magana ta gaskiya wannan mu ba ma ɗaukar mutum a matsayin ɗan wannan masana’anta ta Kannywood.”

Shugaban ya yi nuni da cewa Sadiya Haruna ba jarumar Kannywood ba ce, ita ma Umma Shehu ta na yin ‘yan abubuwan ta amma dai ba ta da cikakkiyar ƙa’idar zama cikakkiyar jaruma ba.

Ya ci gaba da cewa, “Mutane na gari ba za su iya fahimtar haka ba, amma mu na amfani da wannan damar wajen sanar da su cewa yanzu kamar ita kan ta Umma Shehu jaruma ce da ta ke gabatar da abubuwan ta amma magana ta gaskiya ba ta da ƙa’idoji na tabbatuwa a cikin wannan masana’anta tamu.”

Ummah Shehu

Kwalle ya ja hankalin jarumai da su dinga kiyaye bakin su, kuma ya gargaɗe su da ko me mutum zai yi, to ya dinga tuna addinin shi.

A nata martanin, ita ma Teema Makamashi ta yi Allah-wadai da kalaman na Ummah Shehu 

A saƙon bidiyo da ta saki, jarumar ta ce, “Na rantse da Allah Ummah Shehu ba ki isa ki jawo mana magana, ki jawo mana abin faɗa ba. 

“Har ma yaushe ki ka ji daɗin zama da Sadiyan da za ki tsaya ta fito ta dinga ba ta san darajar Annabin mu ba? Har ki zo ki na goya mata, ki na zagin uban wasu, mijin wasu, ki dinga ce musu su ma za ki zo ki nuna musu inda su ka je su ka yi zina da mutane?

“Wallahi ko idan ba ka iya bakin ka ba, idan ba ka iya harshen ka ba, sai ka sha wuya a rayuwa.

“Ba zai yiwu ki dinga jawo wa ‘yan Kannywood magana ba.

“Nan da ta zo ta na abu, na ga ba ki fito kin yi magana ba, sai da aka kama ta za ai mata hukunci daidai da abin da ta aikata za ki zo ki na zagin ‘yan Hisbah. ‘Yan Hisbah aikin Allah su ke yi.”

Ta kuma ce, “Wallahi babu wanda ya fi ƙarfin hukuma. Ko ni idan na yi ba daidai ba, za a hukunta ni daidai da laifin da na yi. Sai ki bi ta Kurmawa can, ba kuma beli babu tara, ki je. Sauran bayani ta yi miki bayani.

“Kuma wallahi ki kiyaye kan ki. Ba zai yiwu ki jawo wa ‘yan Kannywood zagi ba, ki zo don ‘yan Hisbah su na aikin Allah ki zo ki na zagin su ki na musu ƙazafi ba. Wallahi ke da su!”

Loading

Tags: Alhassan Kwallehausa actresshausa filmsHisbah CommissionHukumar HisbahKannywood womenTeema MakamashiUmmah Shehu
Previous Post

Ba a kan Ummi Rahab ne Zango ya fara yaudarar ‘yanmata ba – Ali Artwork

Next Post

Minista Sadiya ta ƙaddamar da shirin N-Power kashi na uku

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Minista Sadiya ta ƙaddamar da shirin N-Power kashi na uku

Minista Sadiya ta ƙaddamar da shirin N-Power kashi na uku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!