
ƘUNGIYAR daraktoci a Kannywood, wato ‘Professional Film Directors Association (PROFDA), za ta yi taron addu’a ga abokin aikin su, marigayi Aminu S. Bono, wanda ya rasu makon da ya gabata.
A cikin takardar gayyatar taron addu’ar wadda kakakin ƙungiyar, Hassan Giggs, ya fitar a daren jiya, ta nuna za a yi taron a gobe Litinin.
Taron zai gudana ne a Social Welfare da ke Court Road, Kano da misalin ƙarfe 3:00 na rana.
Ƙungiyar na gayyatar dukkan ‘yan Kannywood zuwa wurin addu’ar.
