MASU harkar finafinan Hausa za su yi taro a Kano gobe Lahadi domin yi wa babbar furodusa Hajiya Umma Ali addu’o’i, kwana bakwai bayan rasuwar ta.
Hajiya Umma, wadda ita ce shugabar farko ta ƙungiyar mata masu ɗaukar nauyin shirya finafinan Hausa (furodusoshi), ta rasu ne a ranar Lahadi, 31 ga Yuli, 2021 a Asibitin Premier da ke Kano.
Shekarun ta kimanin 63 a duniya.
Ta bar mijin ta, Alhaji Muhammad Ali, wanda tsohon ma’aikacin hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa ne, wato Kwastam, da kuma ‘ya’yan ta 10, maza shida mata huɗu, da jikoki 11.
Rasuwar ta ta girgiza ‘yan fim matuƙa domin kowa ya ɗauke kamar uwa ce gare shi.
‘Yan fim sun ƙudiri aniyar gudanar da gangami a ranar Lahadi, 8 ga Agusta, 2021 domin yi mata addu’o’in neman rahamar Ubangiji.
A sanarwar da jami’in yaɗa labarai na Majalisar Dattawan Kannywood (Kannywood Foundation), reshen Jihar Kano, Alhaji Auwalu Isma’il Marshal ya bayar, an ce buƙaci kowane ɗan fim da ya halarci wannan taro.
Marshal ya ce ƙungiyar “na gayyatar kowa da kowa wajen gudanar da addu’o’in neman gafara da afuwa da rahama daga Ubangiji Allah ga ‘yar’uwar mu kuma abokiyar sana’ar mu, Hajiya Umma Ali, wacce ta koma ga mahaliccin ta ranar Lahadi, 31/07/2021.
“Za a gudanar da wannan addu’o’in ranar Lahadi, 08/08/2021, a Social Welfare ta Gyaɗi-Gyaɗi, Court Road, da ƙarfe 3:00 na yamma. Allah ya bada ikon zuwa, amin.”
Ya ƙara da cewa a taron, za kuma a yi addu’o’i na musamman ga “sauran waɗanda mu ka rasa a wannan masana’anta.
“Haka kuma za a yi addu’a ga marasa lafiyar mu da ita kan ta masana’antar.”