• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, August 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Yan sanda na binciken yadda jarumi ya harbe mai shirya fim da bindiga a lokeshin

by DAGA IRO MAMMAN
October 25, 2021
in Labarai
0
Lokeshin ɗin shirya fim ɗin 'Rust' inda aka yi kisan

Lokeshin ɗin shirya fim ɗin 'Rust' inda aka yi kisan

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

‘YAN sanda a garin Santa Fe na jihar New Mexico ta ƙasar Amurka su na gudanar da bincike kan yadda wani jarumi ya bindige wata ma’aikaciyar shirya finafinai da darakta a wajen ɗaukar wani fim.

Wani rahoto da mujallar Fim ta fassaro daga jaridar New York Times ya bayyana cewa haɗarin ya faru ne a wani yanki mai yawan gonakin auduga da tsaunuka inda a kan shirya finafinan gumurzu (Westerns) tun cikin shekarun 1950s.

Jarumi Alec Baldwin su na ɗaukar wani fim a wani gidan gona a yammacin ranar Alhamis da ta gabata inda ya ke taka rol ɗin mugu, sai ya buƙaci yin amfani da bindiga a cikin wasan.

Sai wani mai tallafa wa darakta ya ɗauko ɗaya daga cikin bindigogi uku waɗanda mai kula da makamai a lokeshin ɗin ya jera kan wata amalanke, ya miƙa wa Baldwin, tare da faɗa masa cewa babu ɗuri a bindigar. 

Ɗan sanda mai binciken lamarin, Joel Cano, ya bayyana cewa an faɗa wa jarumin cewa lallai babu albarushi a cikin bindigar.

Jarumi Alec Baldwin … an faɗa masa babu albarushi a bindigar kafin ya harba ta

Sa’ilin da Baldwin ya harba bindigar, inji jami’an ‘yan sanda, sai kawai aka ji ta tashi, kuma nan take ta kashe wata ma’aikaciyar shirin fim ɗin (cinematographer) tare da ji wa daraktan fim ɗin rauni.

Al’amarin ya tada muhawara kan dacewar aje bindigogi masu ɗuri a lokeshin ɗin shirya finafinai.

An bayyana cewa mai tallafa wa daraktan “bai san cewa bindigar na da ɗuri ba” lokacin da ya miƙa ta ga jarumi Baldwin.

Takardar ƙarar da ‘yan sanda su ka rubuta kan binciken farko kan al’amarin ba ta faɗi irin albarushin da ke cikin bindigar ba.

Da ya harba, sai ya samu daraktar tsarin hoto ta shirin (director of photography) a ƙirji, wato Halyna Hutchins, ‘yar shekara 42. An garzaya da ita asibitin Jami’ar New Mexico da ke garin Albuquerque, inda ta ce ga garin ku. Shi kuma daraktan shirin, Joel Souza, ɗan shekara 48, albarushin ya same shi a kafaɗa ne, ya ji masa ciwo; aka kai shi Cibiyar Magani ta Christus St. Vincent da ke Santa Fe, inda daga baya aka sallame shi.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a Tuwita a ranar Juma’a, Baldwin, ɗan shekara 63, ya ce, “Babu kalmomin da zan iya amfani da su in bayyana tsananin kaɗuwa ta da baƙin ciki na dangane da wannan haɗari abin baƙin ciki da ya ɗauki ran Halyna Hutchins, macen aure, uwa kuma abokiyar aikin mu wadda mu ke ƙauna.

“Ina bada cikakken haɗin kai ga binciken da ‘yan sanda ke yi don warware zare da abawar yadda wannan abin takaici ya auku, kuma ina magana da mijin ta, ina ba shi goyon baya shi da iyalin shi. Zuciya ta na tausaya wa mijin ta da ɗan su da kuma dukkan waɗanda su ka san Halyna tare da ƙaunar ta.”

Labarin fim ɗin ‘Rust’ wanda su Baldwin ke shiryawa ya shafi yadda aka yi kisa bisa haɗari ne da abin da ya biyo bayan kisan. 

Sai ga shi lokeshin ɗin fim ɗin a gonar Bonanza Creek Ranch da ke yankin Santa Fe County — ya zama wurin kisa na gaske, da kuma binciken gaske.

Jami’in yaɗa labarai na ofishin ‘yan sandan garin, Juan Rios, ya faɗa ran Juma’a da yamma cewa ana ci gaba da bincike mai zurfi kuma masu bincike sun shiga lokeshin ɗin shirin a ranar tare da ci gaba da tattaunawa da waɗanda abin ya faru a kan idon su.

Loading

Tags: Alec BaldwinAmurkabindigafilm locationgun violenceHalyna HutchinsharbiHollywoodkisalokeshinRust movie
Previous Post

Cewar Rarara: Zan tsaya takarar Majalisar Tarayya a 2023

Next Post

Jami’ar Jihar Sokoto ta shirya gasar rubuta ‘waƙa kwaikwaye’

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Tsohuwar matar Adam Zango, Maimuna Musa, ta tabbatar da dalilin rabuwar auren su
Labarai

Tsohuwar matar Adam Zango, Maimuna Musa, ta tabbatar da dalilin rabuwar auren su

August 2, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
Next Post
Ƙofar Jami'ar Jihar Sokoto

Jami'ar Jihar Sokoto ta shirya gasar rubuta 'waƙa kwaikwaye'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!