• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 22, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: Atiku ya mai da hankali kan kamfen, ya rabu da su Wike ‘yan bulkara – Rundunar Yaƙin Atiku

by DAGA WAKILIN MU
November 9, 2022
in Nijeriya
0
Atiku Abubakar

Atiku Abubakar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN bayyana cewa tuni ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi watsi da gaganiyar neman sulhu da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas da sauran magoya bayan sa su ke yi.

Wata majiya daga cikin Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku ta shaida wa jaridar Vanguard cewa yanzu Atiku ya mayar da hankali ne kan yaƙin neman zaɓe, kuma hakan ya yi tasiri sosai, idan aka yi la’akari da irin karɓuwar da ya ke ƙara samu a faɗin ƙasar nan.

Ta ce: “Jirgin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar na 2023 ya rigaya ya tashi, don haka duk wani tuggu da ƙulle-ƙullen da su Wike za su yi, ba zai haka jirgin kaiwa zango ba.

“Ƙoƙarin da su ka yi da wanda su ke yi domin hana jirgin tashi, bai yi nasara ba. Domin idan ka duba za ka ga a kowane yanki na ƙasar nan Atiku na ci gaba da ƙara samun karɓuwa.

“Wike da sauran gwamnonin da ke goyon bayan sa duk su na da ‘yancin goyon bayan wanda su ka ga dama. Amma fa ba gaskiya ba ce da su ke nuna kan su cewa za su iya hana al’ummar jihohin su zaɓen PDP.” 

Majiyar ta ƙara da cewa: “Maganar cewa su Wike da sauran su na ganin sai wanda su ke so za a zaɓa a jihohin su, wannan duk hauragiya ce kawai. Ka na nufin ka ce Gwamna Seyi Makinde na Oyo na da kwarjinin cewa sai wanda ya ke so za a zaɓa a Oyo? Haba! Shi fa ba Bola Ige ba ne ko Awomolo, to wane kwarjinin hana ‘yan PDP su zaɓi Atiku ya ke da shi?”

Majiyar ta ce tuni rundunar kamfen ta yi gaba, ba za ta taɓa kowawa kan su Wike ba.

“Amma idan mu ka ci karo da su kan hanya, su ka tsayar da jirgin su ka ce a ɗauke su, za mu tsaya su shiga.”

Kwanan nan wasu jiga-jigan PDP da su ka haɗa har da ɗan takarar sanatan Delta ta Tsakiya, Ned Nwoko, sun yi kira ga PDP ta kori Wike, su na cewa ko da shi ko babu shi PDP za ta iya cin zaɓe.

Haka shi ma Gwamna Samuel Ortom na Binuwai, da dama sun ja hankalin sa cewa ya kamata ya yi karatun ta-natsu, ya goyi bayan Atiku domin kawo ƙarshen rikice-rikicen makiyaya da manoma a jihar sa.

Loading

Tags: Atiku AbubakarNed NwokoNyesome WikeSamuel Ortomyaƙin neman zaɓeZaɓen 2023
Previous Post

Shin Nabraska ya yi baki biyu ne kan rigimar Ganduje da Rarara?

Next Post

Zaɓen 2023: Ba za mu take umarnin kotu ba – INEC

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya na gabatar da jawabi ga manyan alƙalan

Zaɓen 2023: Ba za mu take umarnin kotu ba - INEC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!