ƊAN takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa Kannywood kyautar naira miliyan 50 a matsayin gudunmawar sa ga cigaban masana’antar.
Tinubu ya ba da kuɗin ne a lokacin da ya halarci wani taro na musamman da ‘yan fim su ka shirya masa a daren ranar Lahadi a fadar Gwamnatin Jihar Kano.
Tun da farko da ya ke jawabin manufar shirya taron, furodusa Abdul Amart Maikwashewa, ya ce: “Wannan taro na matasa ‘yan fim ne masu goyon bayan tafiyar Tinubu su ka shirya a ƙarƙashin Gidauniyar Kannywood domin su nuna irin ƙarfin goyon bayan da ya ke da shi a cikin ‘yan fim.
“Don haka a shirye su ke su ba shi dukkan goyon baya don ganin ya kai ga nasara.”

Shi ma a nasa jawabin, shugaban ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya bayyana Kannywood da wata babbar masana’antar da ta ke kawo kuɗin shiga da kuma samar da aikin yi ga matasa, don haka ya yi kira ga Tinubu da ya duba yadda masana’antar ta ke idan an kai ga nasara.
A nasa jawabin, jarumi kuma tsohon shugaban MOPPAN, Alhaji Sani Mu’azu, ya yi kira ga ɗan takarar da ya zuba ‘yan fim a cikin yaƙin neman zaɓen sa saboda karɓuwar su ga jama’a da kuma masoya masu yawa da su ke da su.
A lokacin da ya ke mayar da jawabi, shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na ƙasa, Gwamna Samuel Lalong na Jihar Filato, ya tabbatar wa da ‘yan fim ɗin cewa da man su na cikin kwamitin, kuma za a ƙara wasu.

Haka kuma ya tabbatar da gudunmawar naira miliyan 50 ga Kannywood da Tinubu ya ba su domin inganta masana’antar.
Taron ya samu halartar dukkan ƙungiyoyin da ke cikin masana’antar.