DA alama dai salon tafiyar siyasar 2023 daban ne a masana’antar finafinai ta Kannywood, musamman ma dai yadda ake ganin su ma mata sun shiga sahun ‘yan kwamitin tallar yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu.
A ziyarar da ya ke yi ta ganawa da jama’a a Kano ya buɗe ofishin yaƙin neman zaɓen sa da ‘yan fim su ke jagoranta a ƙarƙashin furodusa Abdul Amart Maikwashewa.
Wani abu da ya ɗauki hankalin jama’a a wajen shi ne yadda jarumai mata su ka yi shigar Yarabawa, su na yi wa Tinubu maraba.

Fitattun jarumai mata da aka gani sun haɗa da Mansurah Isah, Rahama MK, Maryam CTV, Safiya Adamu (Kishiya), Fati Nijar, Safiya Ahmad, Teema Makamashi, Ummi Gombe, da sauran su.
Ana ganin wannan wata sabuwar tafiya ce matan su ka samar ta siyasa domin tafiyar da siyasar su ta daban, ba tare da sun shiga cikin tawagar maza ba.