• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: Za mu ɗauki ma’aikata miliyan 1.4 domin horar da su yadda za su yi amfani da na’urar BVAS, inji INEC

by DAGA WAKILIN MU
January 3, 2023
in Nijeriya
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ta fara shirye-shiryen ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi domin fara horas da su yadda za su yi aiki da na’urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe, wato BVAS.

Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Barista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels TV a ƙarshen makon jiya.

Okoye ya ce akwai buƙatar bayar da horon ƙwarewa wajen yin amfani da na’urar, ta yadda a lokacin zaɓe ba za a riƙa samun jinkiri ba, wanda hakan ka iya sa masu jefa ƙuri’a yin ƙorafi da tsarin tantance su ta hanyar amfani da na’urar.

Ya ƙara da cewa za a wadatar da BVAS a dukkan rumfunan zaɓe 176,846 da ke faɗin ƙasar nan.

A wani bincike kuma, hukumar ta tabbatar har yanzu akwai aƙalla mutum miliyan 1.7 da ba su karɓi katin shaidar rajistar zaɓe ba, wato PVC, a Jihar Legas.

Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa ranar Asabar, mutum 5,816,528 ne su ka karɓi shaidar rajistar zaɓe a jihar.

Tuni dai hukumar zaɓen ta fara kokawa da yadda karɓar katin shaidar rajistar zaɓe ke tafiyar hawainiya a wasu jihohin, ganin yadda jama’a ba su bayar da himma sosai wajen tururuwar zuwa karɓar katin, wanda sai da shi ne mutum zai iya jefa ƙuri’a a zaɓubbukan a Nijeriya.

Hakan ya sa cikin makon jiya INEC ta je Jihar Cross River, inda ta riƙa wayar wa jama’a da kai cewa su hanzarta su je su karɓi katin shaidar rajistar zaɓen su.

Hukumar ta yi wannan kiran ne a wurin gagarumin taron kalankuwar ‘Calabar Carnival’.

A Jihar Akwa Ibom ma hukumar ta koka ganin yadda jama’a ba su yin tururuwar zuwa karɓar katin shaidar rajistar zaɓe.

A Gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT) kuwa, rahotanni sun nuna cewa har yanzu akwai katin shaidar rajistar zaɓen da ba a karɓa ba, tun daga 2011 zuwa 2022, har guda 460,643.

Rahotannin sun nuna cewa daga 2011 zuwa 2019 akwai katin da har yanzu ba a karɓa ba, guda 230,007.

Sai kuma waɗanda aka yi wa rajista amma ba su karɓa ba daga 2021 zuwa 2022 har guda 230,636.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye, ya jaddada cewa INEC za ta yi amfani da na’urar tantance mai rajistar katin zaɓe, wato BVAS a dukkan rumfunan zaɓen ƙasar nan guda 176,846.

Sannan ya ce tuni INEC ta fara aikin yadda za ta ɗauki ma’aikatan wucin-gadi fiye da milyan 1.4 waɗanda za a bai wa horon aiki da na’urar BVAS a lokacin zaɓukan shugaban ƙasa, na ‘yan majalisar tarayya, gwamnoni da na majalisar dokoki ta jihohi.

Loading

Tags: BVASINECkatin zaɓeLegasmahmood yakubuna'uraZaɓen 2023
Previous Post

Babban buri na game da ‘ya ta, Surayya – jaruma Hadizan Saima

Next Post

Alan Waƙa ya zargi Rarara da yi masa ingiza-mai-kantu-ruwa

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa)

Alan Waƙa ya zargi Rarara da yi masa ingiza-mai-kantu-ruwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!