• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 24, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen Anambra: Abin da ya sa murnar Soludo ta koma ciki

by DAGA WAKILIN MU
July 17, 2021
in Nijeriya
0
Zaɓen Anambra: Abin da ya sa murnar Soludo ta koma ciki
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DUK da yake tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Farfesa Charles Soludo, ya yi murnar cin zaɓen share fagen takarar gwamnan Jihar Anambra, murnar sa ta koma ciki domin kuwa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ba ya cikin ‘yan takarar.

A jerin sunayen ‘yan takara da INEC ta fitar ranar Juma’a, sunan Chukwuma Michael Umeoji aka gani a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APGA, maimakon Soludo da ya shiga murna.

A jadawalin sunayen, hukumar ta rubuta kalmomin “umarnin kotu” a matsayin dalilin ta na sanya sunan Umeoji.

Haka kuma jam’iyyar PDP ba ta da ɗan takara a jerin sunayen da aka fitar saboda umarnin kotu kamar yadda jadawalin ya ce.

A cewar INEC, an tsara cewar za a gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Anambra ne a ranar 6 ga Nuwamba, 2021.

Babban Kwamishina kuma shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Faɗakar da Masu Zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, ya faɗa a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a cewa, “Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi taro a jiya Alhamis, 15 ga Yuli, 2021 kuma daga cikin abubuwan da ta tattauna, ta duba jerin sunaye da bayanan ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa daban-daban su ka fitar don shiga zaɓen gwamnan Jihar Anambra wanda aka tsara za a gudanar a ranar 6 ga Nuwamba, 2021.

“Hukumar ta kuma duba tare da yin la’akari da hukunce-hukunce da umarnin kotu da aka kawo mata dangane da zaɓuɓɓukan share fage na jam’iyyun siyasa da sauran abubuwan da aka yi kafin zaɓen.

“Bisa ga tanadin da sashe na 31(3) na Dokar Zaɓe ta 2010 (wadda aka gyara) ya yi, za a wallafa bayanan rayuwar ‘yan takarar a allon sanarwar hukumar da ke Awka, a Jihar Anambra, yayin da kuma sunayen ‘yan takarar da jinsin su da jam’iyyar su da cancantar su, da kuma matsayi da kalaman hukumar ga su a nan an maƙala su. 

“Hukumar za ta ci gaba da yin aiki da Kundin Tsarin Mulki da doka kuma za ta ci gaba da bin hukunce-hukunce da umarnin kotuna da aka kawo mata.”

Loading

Tags: Anambra guber electionElectoral ActFestus OkoyeIndependent Electoral CommissionINECProf Charles SoludoProf Mamoud Yakubu
Previous Post

‘Yan Nijeriya 542,576 sun kammala matakin farko na rajista cikin mako 2 — Yakubu

Next Post

Nabraska ya ziyarci surukin sa, Ɗanjuma Katsina

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Nabraska ya ziyarci surukin sa, Ɗanjuma Katsina

Nabraska ya ziyarci surukin sa, Ɗanjuma Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!