• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, July 21, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen Anambra: INEC ta ƙara matakan tsaro

by DAGA WAKILIN MU
November 4, 2021
in Nijeriya
0
INEC ta yi wa masu zaɓe 30,449 rajista a Filato
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta fito da ƙarin matakan tsaro wajen kare kayan aikin ta masu hatsari waɗanda za ta yi amfani da su a zaɓen gwamnan Jihar Anambra don gano kayan jabu.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron da ya yi da masu ruwa da tsaki a zaɓen a Awka, babban birnin jihar.

Yakubu ya yi gargaɗin cewa hukumar za ta ɗauki matakin shari’a a kan duk wanda ya aikata laifin maguɗi a zaɓen, ciki har da duk wani ma’aikacin zaɓe da aka kama da hannu a ciki.

Ya ce, “Ina so in tabbatar wa da dukkan masu zaɓe a Anambra cewa a wajen tsara kayan zaɓen masu hatsari, hukumar ta saka ƙarin wasu alamomin tsaro waɗanda ba a gani da ido, ciki har da kalolin sirri mabambanta.

“Haka kuma an tsara kayan aikin ne bisa kowace ƙaramar hukuma da rumfar zaɓe.

“Saboda haka bari in gargaɗi duk wani wanda zai yi ƙoƙarin yi wa tsarin zagon ƙasa cewa mun tanadi isassun matakan rigakafi don gano kayan bogi.

“Zaɓin wanda zai zama sabon gwamnan Anambra ya na hannun masu zaɓe kuma tilas ne zaɓin su ya yi galaba.”

Shugaban ya kuma tunatar da jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da magoya bayan su cewa har yanzu sayen ƙuri’a laifi ne a dokar ƙasar nan.”

Ya nanata cewa har yanzu dokar hana amfani da wayar hannu ko wata na’urar ɗaukar hoto a rumfar zaɓe ta na aiki.

Ya ce, “Hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, waɗanda membobin Kwamitin Tuntuɓar Hukumomi kan Tsaro a Zaɓe ne, wato ‘Inter-Agency Consultative Committee on Election Security’, za su tura ma’aikatan su domin kama masu karya doka tare da gurfanar da su a kotu.”

Ya yi kira ga shugabannin jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su da su roƙi magoya bayan su da su kauce wa furta munanan kalaman ko yin wani abu da zai kawo tsaiko kafin zaɓen da lokacin da ake yin sa da kuma bayan sa.

Ya ce, “A yayin da mu ke aiki tare da hukumomin tsaro, mun kuma yi abubuwa masu daman haske don tabbatar da an yi zaɓen nan cikin nasara.

“Don Allah ta hanyar kalaman mu da ayyukan mu mu mara wa shirin wannan zaɓe cikin lumana da inganci goyon baya.”

Yakubu ya yi la’akari da cewa an rarraba kayan zaɓe marasa hatsari a dukkan yankunan ƙananan hukumoni 21 na jihar.

Ya ce, “Za a kai waɗannan kaya zuwa yankunan rajista ko unguwanni a ranar Juma’a don a samu buɗe rumfunan zaɓe da ƙarfe 8.30 na safe a ranar zaɓe, wato Asabar.”

Yakubu ya ce Anambra za ta kafa tarihi a matsayin jihar farko a Nijeriya da aka yi zaɓen gwamna inda hukumar ta yi amfani da tsarin tantance mai zaɓe ta hanyar komfuta, wato ‘Biometric Voter Accreditation System’ (BVAS).

Ya ce, “Ina farin cikin shaida maku cewa dukkan na’urorin BVAS da ake buƙata don yin zaɓen a ranar Asabar an tsara su an kawo su Anambra.

“Ma’aikatan zaɓe kuma an horas da su kan yadda ake amfani da na’urar, sannan mu na da isassun ma’aikatan kula da na’urori da za su gyara duk wata mishkila da ka taso.”

Yakubu ya yi kira ga sababbin masu zaɓe waɗanda aka yi wa rajista ko waɗanda su ka buƙaci a ba su katittikan zaɓe na dindindin, wato ‘Permanent Voter Cards’ (PVCs), kuma waɗanda ba su karɓa ba da su hanzarta su karɓa.

Ya ce, “Ina farin cikin sanar da ku cewa an buga katittikan zaɓen kuma an kai su kowace ƙaramar hukuma don masu zaɓe su karɓa.

“Haka kuma mun tuntuɓi masu zaɓen ta hanyar tes da imel, mun sanar da su ainihin inda za su karɓi katittikan su.”

Yakubu ya tabbatar wa da dukkan masu ruwa da tsaki cewa hukumar sa ta shigo da na’urorin musamman da za su taimaka wajen agaza wa naƙasassu a wajen zaɓen.

“Sun kuwa haɗa da littafin ‘Braille Ballot Guide’ da gilashi mai ƙara girman rubutu saboda masu matsalar gani, kai har ma da fasta-fasta na ilimantar da ma’aikata waɗanda ba su gani sosai.

Babban Kwamishinan Hukumar Zaɓe mai kula da wannan zaɓen, Mista Festus Okoye, shi ma ya yi tsokaci inda ya ba jama’a tabbacin cewa INEC za ta gudanar da zaɓe fisabilillahi, babu son kai, kuma karɓaɓɓe ga kowa.

Okoye ya yi nuni da cewa ai INEC ta gudanar da zaɓuɓɓukan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo a cikin mawuyacin hali na annobar korona (COVID-19).

Ya ce zaɓen gwamnan Anambra, duk da yanayin sa na musamman, zai ƙara jarraba ƙarfin kafuwar mulkin dimokiraɗiyyar Nijeriya ne tare da hukumomi da ƙungiyoyin dimokiraɗiyya ɗin.

Loading

Tags: AwkaFestus OkoyeHukumar Zabe ta Kasa (INEC)Independent National Electoral CommissionINECmatakan tsaroPermanent Voter CardsProfessor Mahmood Yakubuzaben gwamnan Jihar Anambra
Previous Post

Cewar Farfesa Yakubu: INEC ta shirya wa zaɓen gwamnan Anambra na ranar Asabar

Next Post

An zaɓi jagororin Kannywood, Ahmed Sarari da Sani Mu’azu, a matsayin ‘yan kwamitin gudanarwa na ƙungiyar kare haƙƙin manishaɗanta ta Nijeriya

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Dakta Ahmed Sarari da Alhaji Sani Mu'azu

An zaɓi jagororin Kannywood, Ahmed Sarari da Sani Mu'azu, a matsayin 'yan kwamitin gudanarwa na ƙungiyar kare haƙƙin manishaɗanta ta Nijeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!