• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za a bi dukkan ƙa’ida a tuhumar almundahanar kuɗi da ake yi wa kamfanin Binance, inji Gwamnatin Tarayya

by WAKILIN MU
June 5, 2024
in Nijeriya
0
Za a bi dukkan ƙa’ida a tuhumar almundahanar kuɗi da ake yi wa kamfanin Binance, inji Gwamnatin Tarayya

Hatimin kamfanin Binance

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YAYIN da ake sa ido kan shari’ar nan da ake yi da wani kamfanin hada-hadar kuɗaɗen kirifto mai suna Binance, da wani daga cikin jagororin kamfanin wanda ya karya doka wajen hadahadar, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce za a bi dukkan matakan doka da oda da aka saba da su a Nijeriya a shari’ar.

A cikin wata sanarwa da Rabi’u Ibrahim, mataimakin sa na musamman kan yaɗa labarai ya fitar a ranar Laraba, Idris ya bayyana cewa ana bin dukkan ƙa’idojin doka wajen gudanar da shari’ar.

Ya ce, “A kowace gaba, ana bin doka da oda, kuma masu gabatar da ƙara su na da yakinin samun nasara a shari’ar, ganin irin ƙwararan shaidu da hujjoji da aka tattara.

“Binance zai sami damar kare kan sa a kotu game da waɗannan manyan tuhume-tuhume na almundahanar kuɗi da ya tafka a Jamhuriyyar Tarayyar Nijeriya. Za a ci gaba da sauraren ƙarar a ranar 20 ga Yuni, 2024.”

Idris ya bayyana cewa an bai wa Binance, wanda ke kare kan sa a shari’ar, duk wata dama da duk wata kulawar da ta dace, sakamakon samun kula ta ofishin jakadanci da diflomasiyya da aka saba da su, ya ƙara da cewa alƙalin da ke shari’ar ya bayar da gamsasshen bayanin cewa an hana beli ne ga jami’in kamfanin saboda akwai yiwuwar ya tsere, ganin cewa wanda ake tuhumar su tare ya gudu, kuma yanzu haka ‘Yan Sandan Ƙasa da Ƙasa (Interpol) suna neman sa.

Idan za a iya tunawa dai, Binance ya samu ribar sama da dala biliyan 20 a Nijeriya a cikin 2023 kadai, wanda wannan kuɗin ya zarce kasafin kuɗin da gwamnatin tarayya ta yi wa harkokin kiwon lafiya da ilimi, kuma ya haifar da badaƙalar da ta faru a kasuwar canji tare da matsalar tsadar rayuwa.

Bugu da ƙari, Binance ba shi da rajista a Nijeriya kuma bai taɓa biyan haraji ba, sannan ya yi ta harkokin sa ba tare da an sa masa ido ba, kawai ya na cin karen sa ba babbaka da bin ƙa’idojin hana aikata laifuffukan kuɗi.

Idris ya ce abu ne mai muhimmanci a kalli Binance a matsayin wani kamfani wanda jami’an sa aka ɗaure su ko aka ci su tara ko aka yi masu wani hukuncin ko kuma aka dakatar da su a Amurka, Turai, da Asiya, a cikin ‘yan shekarun nan.

Ya ce, “Changpeng Zhao, hamshaƙin biloniyan nan kuma tsohon shugaban kamfanin Binance, wanda tare da shi aka kamfanin, a halin yanzu ya na zaman gidan waƙafi na tsawon watanni huɗu a Amurka, bayan da aka same shi da laifin almundahanar kuɗaɗe, yayin da Binance ya fito fili ya amince da rawar da ya taka wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci, cin hanci da rashawa, daƙile takunkumi, da kuma taimaka wa da tallafa wa ƙungiyoyi masu lalata da ƙananan yara.

“Hukumomin doka da oda sun yi imanin cewa ayyukan Binance a Nijeriya wani ɓangare ne na rawar da kamfanin ke takawa a ƙasashen duniya. A nan ne kotuna, kamar yadda ake yi a sauran wurare, za su yi wa kamfanin da shugabannin sa hisabin da ya dace da su.”

Loading

Tags: almundahanaBinanceMohammed Idristuhuma
Previous Post

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta fara raba takardar shiga gasar rubutu 

Next Post

Bankin Masana’antu zai yi wa ‘yan Kannywood bita a Kano gobe

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Bankin Masana’antu zai yi wa ‘yan Kannywood bita a Kano gobe

Bankin Masana'antu zai yi wa 'yan Kannywood bita a Kano gobe

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!