HAƊAƊƊIYAR Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta samar wa matasan Kannywood guraben horo na musamman daga wata makaranta da ke Legas mai suna ‘Terra Academy for the Arts’ (TAFTA).
Kakakin ƙungiyar na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, shi ne ya sanar da hakan a yau Alhamis, cikin wata sanarwa inda ya ce: “Bayan da aka cimma wata yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin uwar ƙungiyar masana’antar fim ta Kannywood, wato MOPPAN, da ƙungiyar ‘Terra Academy’, an cimma cewar ‘ya’yan masana’antar Kannywood masu shekaru 16 zuwa 35 ne za su mori garaɓasar koyon ayyukan fim kyauta.”
A bisa hakan, Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Muhammad Saurari, ya ce, “Koyarwar ta ƙunshi fannoni kamar haka:
Scriptwriting, Sound Design, Light Design,
Animation da kuma yadda za a yi amfani da abin da aka koya wajen dogoro da kai.”
‘Terra Academy for the Arts’ sun samu haɗin gwiwa da taimakon ‘Mastercard Foundation’.
Wannan koyarwar dai za ta ɗauki tsawon mako 6 zuwa 8.
Kan haka, MOPPAN ta yi kira ga masu sha’awar samun ilimin harkar fim mai inganci kuma kyauta da su yi rajista kai-tsaye ta yanar gizo a wannan adireshin:
https://terraacademyforarts.com/tafta-registration-form/