• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, May 15, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen Edo: Ku guji siyasar ‘a-mutu-ko-ai-rai’ – Buhari

by DAGA WAKILIN MU
September 18, 2020
in Nijeriya
0
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
SHUGABA Muhammadu Buhari ya shawarci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da jami’an tsaro da su yi aiki tsakanin su da Allah a zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Edo a gobe Asabar.
 
A cikin saƙon da ya aike wa da masu zaɓe da jam’iyyun siyasa da jami’an zaɓe da na tsaro, shugaban ya kuma yi gargaɗi kan abin da ya kira “tunanin siyasa irin na ko-a-mutu-ko-ai-rai.”
 
Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan al’amurran aikin jarida da yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, ya ruwaito Buhari ya na faɗin: “Na yi matuƙar sadaukar da kai na ga tabbatar da zaɓe cikin adalci, to amma tawa sadaukarwar ba ta wadatar ba ita kaɗai idan sauran masu ruwa da tsaki da ke wajen zaɓen ba su bi ƙa’idoji ba.
 
”Ina so in ga an ɗaga darajar dimokiraɗiyya a ƙasar nan a kowane mataki, amma hakan ba zai samu ba idan su ‘yan siyasa sun hau matsayin a-mutu-ko-ai-rai don kawai su samu mulki ko ta halin ƙaƙa.
 
“Tunani irin na  a-mutu-ko-ai-rai a siyasa barazana ne ga zaɓe cikin adalci da kwanciyar hankali domin su ‘yan siyasar sun fi maida hankali ne ga cin zaɓen maimakon su damu da samuwar sakamako cikin adalci wanda zai nuna buƙatar mutane masu zaɓe.”
 
Shugaban ya yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su da su bi doka da oda.
 
Ya shawarci jami’an zaɓe da na tsaro da “su kasance ‘yan baruwan mu don tabbatar da an yi zaɓe cikin kwanciyar hankali kuma cikin adalci. kuma su guji aikata duk wani abu da zai iya ɓata darajar zaɓen.”
 
Ya ce: ”Gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da adalci ya na daga cikin manyan abubuwan da na tsare a dimokiraɗiyyar mu, kuma ina so wannan sadaukarwar ta kasance ɗaya daga cikin gadon da zan bar wa ‘yan baya idan na bar mulki.”
 
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta kammala dukkan shirye-shirye don gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Edo a gobe Asabar. 
 
Haka kuma ya ruwaito cewa ɗan takarar jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, da na jam’iyyar PDP Godwin Obaseki, waɗanda su ne manyan ‘yan takarar da za su gwabza, sun riga sun rattaba hannu a kan wata takardar yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a zaɓen.

Loading

Previous Post

Zaɓen gwamnan Edo gobe: Mun shirya tsaf, cewar INEC

Next Post

Saƙon Shugaban INEC Kan Zaɓen Edo

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Saƙon Shugaban INEC Kan Zaɓen Edo

Saƙon Shugaban INEC Kan Zaɓen Edo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!