A yayin da mu ke kan gangara zuwa ranar da za a yi zaɓen gwamna na Jihar Edo, a bayyane ta ke cewa yanzu kowa ya maida hankalin sa kan yadda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta gudanar da zaɓen cikin lumana da adalci kuma ta hanya mai inganci.
Ba ni da haufi ko kaɗan cewa ma’aikatan mu za su ba maraɗa kunya. Mun yi irin wannan aikin cikin nasara a da, kuma za mu sake yin irin sa yanzu ɗin ma. Hukumar ta na bayyana gamsuwar ta da irin sadaukar da kai ba tare da gajiyawa ba da ma’aikatan mu ke yi a ko da yaushe, sau da yawa ma har a lokacin da ba na aikin su ba, don tabbatar da mun sauke nauyin da aka ɗora mana. Shugabannin hukumar za su ci gaba da ƙoƙari wajen inganta haƙƙoƙin ma’aikatan mu don ƙara masu ƙwarin gwiwa a cikin halin da ta ke da shi.
Zan yi amfani da wannan dama in yi kira a gare ku da ku ci gaba da jajircewa tare da yin tsayin daka kan aƙidojin hukumar. ‘Yan Nijeriya da ƙasashen waje sun sa ido su ga yadda za ku sauke nauyin mu. Sun zura mana ido. Ya na da muhimmanci duk mu tsare gaskiya a aikin mu. Tilas ne mu tabbatar da cewa ba mu bada fifiko ga wata jam’iyya ko ɗan takara a kan wani ba. Tilas ne mu tsaya a matsayin alƙalai ‘yan ba-ruwan mu, kuma mu tsare Ƙa’idojin Aiki da Rantsuwar Rashin Nuna Wariya waɗanda duk mun yi amanna da su.
Domin kuwa, a ƙarshe, zai kasance dukkan mu mun bada gudunmuwa ga ɗorewar mulkin dimokiraɗiyya da ingantaccen tsarin gudanar da zaɓe wanda duk ‘yan Nijeriya za su iya amincewa da shi.
Na gode da dukkan ƙoƙarin ku.
Farfesa Mahmood Yakubu,
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC)