• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen Ondo: Mun gama shiri – shugaban INEC

by DAGA WAKILIN MU
September 23, 2020
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmud Yakubu

Farfesa Mahmud Yakubu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
BAYAN nasarar da ya samu wajen shirya zaɓen gwamnan Jihar Edo a ranar Asabar da ta gabata, Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bada tabbacin cewa sun shirya tsaf domin gudanar da zaɓen gwamna da za a yi a ranar 10 ga Oktoba a Jihar Ondo.
 
Yakubu ya faɗi haka ne a Akure, babban birnin Jihar Ondon, a ranar Laraba, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.
 
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewar shugaban ya je Akure ne don ziyarar kwana uku saboda duba shirye-shiryen da ofishin hukumar ke yi don gudanar da zaɓen, ya kuma gana da masu ruwa da tsaki a zaɓen.
 
Farfesa Yakubu, wanda ya ce ya je jihar ne domin ya sadu da ma’aikatan hukumar da ke jihar, ya ƙara da cewa duk da matsalar gobara da aka samu a ofishin INEC na jihar, hukumar ta gama duk wani shiri saboda zaɓen. 
 
Ya ce: “Mun riga mun murmure. Sai dai abin baƙin ciki shi ne mun yi asarar injinan karanta katin zaɓe masu aiki da ƙwaƙwalwa har guda 5,000 amma mun murmure ta hanyar sake samo injinan da ake buƙata daga Jihar Oyo da ke maƙwabtaka da nan, kuma an kawo su nan.
 
“Sun iso, an yi cajin su kuma an yi masu saiti, an shirya su domin zaɓen da za a yi a ranar 10 ga Oktoba a Jihar Ondo.
 
“Abu muhimmi shi ne za mu yi amfani da komfutocin ‘Z-pads’ wajen tura sakamakon zaɓen kai-tsaye a ranar zaɓen, kuma mun ɗauko waɗannan ‘Z-pads’ ɗin daga Edo zuwa Jihar Ondo saboda zaɓen.
 
“Saboda haka, irin shirye-shiryen da mu ka yi a Edo, su ne kuma mu ka yi a Ondo, saboda haka mun shirya wa zaɓen.”
 
Yakubu ya ce zai haɗu da majalisar sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro da jami’an hukumar a Yankunan Ƙananan Hukumomi 18  da ke jihar musamman saboda zaɓen.
 
Ya ce, “Wannan ita ce ziyarar farko da na kawo. Za mu sake dawowa bayan mako ɗaya don babban taro da za mu yi da masu ruwa da tsaki da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.”
 
INEC dai ta yi asarar komfutocin karanta katin zaɓe guda 5,141 da za a yi amfani da su a zaɓen na ranar 10 ga Oktoba a Jihar Ondo lokacin da wuta ta tashi da dare a ofishin hukumar a Akure.

Loading

Previous Post

Makon Kurame: Minista Sadiya ta sha alwashin mara wa naƙasassu baya

Next Post

Yau shekara 21: Tunawa da Garban Bichi da Shata

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Daga hagu: Ibrahim Sheme tare da Alhaji Garba Bichi a cikin Satumba, 1998 ... shekara ɗaya kafin rasuwar dattijon

Yau shekara 21: Tunawa da Garban Bichi da Shata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!