• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Makon Kurame: Minista Sadiya ta sha alwashin mara wa naƙasassu baya

by DAGA WAKILIN MU
September 23, 2020
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Hajiya Sadiya Umar Farouq

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa ma’aikatar ta za ta ci gaba da mara wa dukkan naƙasassu da kurame baya don a saka su cikin duk wani shiri, a kare haƙƙin su kuma a ba su damar shiga dukkan al’amurran cigaban al’umma.
 
Hajiya Sadiya ta yi wannan maganar ne a Abuja a ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2020 a wajen bikin zagayowar Makon Kurame na Duniya da kuma Ranar Magana Da Hannu ta Duniya.
 
Ta ƙara da cewa ma’aikatar ta ta kasance kan-gaba wajen ganin an kafa Hukumar Kula da Naƙasassu ta Ƙasa don tallafa wa muradun dukkan mutanen da ke fama da wata naƙasa a Nijeriya.
 
Ta ce: “Ɗaya daga cikin dalilan ware  Ranar Magana Da Hannu ta Duniya shi ne domin a haɓaka yanayin maganar da kuma al’adun kurame a dukkan faɗin duniya.
 
“Ina tabbatar maku da cewa Gwamnatin Tarayya, ta hanyar wannan ma’aikata, ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an kula da dukkan mutane masu wata naƙasa a Nijeriya a harkar gudanar da mulki ta hanyar kawar da duk wani tarnaƙi wanda kafin yanzu ya zame masu ƙargen ƙafa a wajen cigaban su.” 
 
Tun da farko, sai da Sakatare-Janar na Babbar Ƙungiyar Kurame ta Nijeriya, Chidi Topaz Oluije, ya gode wa ministar saboda yadda ta aiwatar da Ranar Kuramen a Nijeriya domin kuwa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce akwai kimanin mutum miliyan goma da ke fama da kurunta a Nijeriya.
 
Ya ce: “A cewar WHO, akwai kurame miliyan goma a Nijeriya. Wannan ya nuna cewar Magana da Hannu babban muhimmin abu ne a gare mu wajen samun damar cuɗanyar duniyar kurame da ta masu ji tare da shiga cikin harkokin siyasa, kiwon lafiya da duk wani sashe na ƙasar nan.”
 
Bikin dai ya samo asali ne daga Ƙudiri mai lamba A/RES/72/161 na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda aka rattaba a cikin 2017 kuma aka ware ranar 23 ga Satumba ta kowace shekara a matsayin Ranar Magana da Hannu ta Duniya.
 
Jigon ranar ta bana dai shi ne ‘Jaddada Haƙƙin Ɗan’adam na Kurame’ (wato a Turance ‘Reaffirming Deaf People’s Human Rights’).
 
Dukkan masu ruwa da tsaki a wannan al’amari za su ci gaba da ayyukan bikin daga ranar 26 zuwa 30 ga Satumba, 2020 a birnin Kano.

Loading

Previous Post

Hukumar Finafinai za ta fara neman riba, inji minista

Next Post

Zaɓen Ondo: Mun gama shiri – shugaban INEC

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Farfesa Mahmud Yakubu

Zaɓen Ondo: Mun gama shiri - shugaban INEC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!