MINISTAN Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi wa Hukumar Finafinai ta Nijeriya (Nigerian Film Corporation, NFC) garambawul ta yadda za ta riƙa samun ribar kuɗi.
Ministan ya yi wannan bayanin ne a yau Litinin a Abuja lokacin da ya ƙaddamar da kwamitin aiwatar da garambawul da maida hukumar mai cin riba.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta bada aikin ga wani mashawarci ɗan kwangila wanda ya ƙware a tsara haɓaka harkar kasuwanci domin ya yi cikakken bincike kan hukumar tare da fito da hanyar da ta dace a bi a yi mata kwaskwarimar da za ta zama mai samun riba.
Mohammed ya ce NFC, wadda an kafa ta ne domin ta tsara, ta tallata kuma ta tattara aikin haɓaka masana’antar shirya finafinai ta Nijeriya, ta kasa cimma burukan da aka ta domin su.
Ya lura da cewar tun da aka kafa ta, hukumar ta fuskanci ƙalubale masu yawa waɗanda su ka haɗa da kasawar ta wajen shirya finafinai da za a sayar a samu riba.
Ministan ya ce dokar da ta kafa NFC ta takure ayyukan ta, ta yadda ba za ta iya shiga hadahadar kasuwancin finafinai da ake yi a masana’antar ba.
Ya ƙara da cewa Cibiyar Shirya Fim ta Ƙasa, wato National Film Institute (NFI), wadda wani ɓangare ne a hukumar ta NFC, ba a ba ta ƙarfin da za ta yi amfani da ɗimbin ilimin ta da kayan aikin ta ba wajen shiga harkar kasuwancin finafinai dumu-dumu don samun kuɗin shiga.
Mohammed ya ce tsarin aikin gwamnati da aka ɗora NFC a kai ya na tattare da wasu dabaibayi da rashin kuɗi da matsalolin gudanar da aiki.
Ya ce: “Idan aka kalli yadda aka tsari hukumar a yanzu sosai za a ga cewar ma’aikata sun yi yawa a NFC kuma ya kamata a sake mata tsari wanda zai dace da aikin da aka ɗora mata.
“Kayan aikin da NFC ta ke da su duk sun tsufa sun lalace, wasu ma tun a zamanin Turawa ake da su.”
Ministan ya ce yi wa hukumar garambawul zai taimaka wajen ƙoƙarin da gwamnati ke yi na gyaran masana’antar finafinai, wato Nollywood, kuma zai sa Nijeriya ta zama hedikwatar harkokin nishaɗi a Afrika.
A yayin da ya ke ambato alƙaluman Gidauniyar Lamuni ta Duniya, wato International Monetary Fund (IMF), Lai Mohammed ya ce Nollywood ita ce masana’anta ta biyu mafi girma wajen ɗaukar mutane aiki a Nijeriya, kuma ta bada gudunmawar naira biliyan 893 ga aljihun kuɗaɗen shiga (GDP) a cikin 2015.
Bugu da ƙari, ministan ya yi la’akari da cewa Nollywood za ta iya wuce haka ma idan aka gyara NFC aka ba ta kayan aikin da ta ke buƙata da kuma ingantaccen yanayin aiki.
Ya ce ban da samar da dukiya da aikin yi, haɓaka industirin finafinai zai taimaka wajen gina kyakkyawar zamantakewa da rage raɗaɗin rayuwa.
Tun da fari, sai da Janar Manaja na Hukumar Kamfanonin Gwamnati (BPE), Mista Alex Okoh, ya yi bayanin cewa idan aka yi la’akari da ɗimbin ƙarfin da masana’antar finafinai ta ke da shi wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasar nan, akwai buƙatar gwamnati ta saka hannu a cikin lamarin sosai.
Okoh ya ce gwamnatin za ta yi wa NFC gyaran fuska ne saboda ta jagoranci tafiyar da za a yi don a haɓaka masana’antar.
Sai dai kuma ya yi nuni da cewa garambawul ɗin ba ya nufin za a sayar da wannan muhimmiyar hukumar ne, kawai maida ita ta kasuwanci kaɗai za a yi.
Ya ce: “Bayanin shi ne a wannan aikin na garambawul, ba za a ɗauke haƙƙin mallakar hukumar daga hannun gwamnati ba, kuma ba za a sayar da hannayen jarin hukumar ba.
“Kawai dai za a tabbatar da ƙarin darajar hukumar ne a yadda ta ke, da kuma yadda za a maida ita mai neman ribar kuɗi.”
Ya ce kwamitin aiwatarwar, wanda ministan ke jagoranta, zai duba kuma ya amince da shawarwarin da gungun waɗanda aka ba aikin yi wa hukumar gyaran fuska za su kawo.
Sauran membobin kwamitin aiwatarwar wanda ministan ya ƙaddamar su ne shi Okoh, da Sakataren Dindindin ta ma’aikatar, Misis Grace Gekpe, da Manajan Daraktan NFC ɗin, Chidia Maduekwe. Sannan Daraktan Yaɗa Labarai na BPE, Dikko Mohammed, zai kasance Sakataren kwamitin.
Ita dai Hukumar Fim ta Nijeriya (NFC), an kafa ta ne a ƙarƙashin Doka mai lamba 61 ta 1979 kuma dukkan ta mallakin Gwambatin Tarayya ce ɗari bisa ɗari, sannan babban ofishin ta ya na Jos, Jihar Filato.
An kafa ta ne domin ta riƙa rarraba finafinan faɗakarwa a kan al’amurra daban-daban na rayuwar ‘yan Nijeriya, kama daga kan rayuwar yau da kullum da al’adu da tattalin arziki zuwa siyasa, kuma ta samar da ayyukan shirya fim ga Gwamnatin Tarayya.
Bugu da ƙari, aikin hukumar ne ta horas da matasa ‘yan Nijeriya masu hazaƙa kan dabarun shirya fim, ta gudanar da bincike kan finafinan Nijeriya, kuma ta bayar da tagomashi ta fuskar kuɗi da kayan aiki ga masana’antar finafinai ta Nijeriya da su masu shirya finafinan.
Haka kuma aikin NFC ne ta sa ido tare da tsara yadda ake fim ta ƙwararrun hanyoyi.