HAJIYA Binta Ƙofar Soro ta yi fice a finafinan Hausa. A yanzu haka ta na ɗaya daga cikin fitattun mata jarumai da su ke fitowa a matsayin iyaye a fim. Idan aka ɗebe Ladidi Fagge, Ladi Mutu-Ka-Raba da Hadizan Saima, babu wata da aka fi yawan gani a matsayin uwa a wannan zamanin bayan ita.
Jarumar ta ƙware kan aikin ta, kuma a yanzu haka ta na ɗaya daga cikin furodusoshin da su ke haskawa a Jihar Katsina. Wakilin mujallar Fim ya tattauna da Hajiya Binta kwanan baya, inda ta feɗe masa biri har wutsiya game da yadda ta fara harkar fim, da nasarorin da ta samu, da sauran su.
FIM: Da farko za mu fara da jin tarihin ki a taƙaice.
BINTA ƘOFAR SORO: Suna na Hajiya Binta Ƙofar Soro, wadda aka fi sani da Ayiya. An haife ni a garin Katsina a unguwar Ƙofar Soro. Na yi makarantar firamare a Katsina, na yi sakandire a Soba, Zariya, sannan na tafi (School of) Health Technology, Kankiya, a Jihar Katsina.
FIM: Ya aka yi ki ka tsinci kan ki a harkar fim?
BINTA ƘOFAR SORO: To gaskiya na fara harkar fim ɗin Hausa lokacin da mu ka rabu da miji na ina jawarci a unguwar Fagge, a Kano. A lokacin na fara harkar. Bayan da miji na ya maida ni sai kuma na daina harkar fim kwata-kwata. Bayan Allah ya yi masa rasuwa sai na dawo na ci gaba da harkar, har yanzu kuma ina yi saboda na san fim bai da illa, sana’a ce ta neman abinci, wadda mu ke yi mu nemi kuɗi mu yi sutura kuma mu rufa wa kan mu asiri.
FIM: Kin kai kamar shekara nawa da fara harkar fim?
BINTA ƘOFAR SORO: Gaskiya na daɗe da farawa na daina. Aƙalla ba a kasara ba, ko yanzu da dawowa ta zan kai shekara goma.
FIM: Ya zuwa yanzu kin yi fim kamar guda nawa?
BINTA ƘOFAR SORO: Gaskiya ba zan iya lissafa su ba, amma dai na san su na da yawa; aƙalla za su kai kamar guda dubu ɗaya.
FIM: Hajiya, ko za ki ya faɗa mana wasu daga cikin finafinan da ki ka yi?
BINTA ƘOFAR SORO: A gaskiya su na da yawa. Na fito a fim ɗin ‘Ɗakin Amarya’, ‘Indon Ƙauye’, ‘Baya Da Ƙura’, ‘Da Kishiyar Gida’, ‘Umarni’, ‘Aboki Na’, ‘Halin Duniya’, ‘Ɗaurin Zato’, ‘Mata Ko ’Ya’, ‘Ƙadangarun Bariki’, da sauran su.
FIM: Wanne fim ki ka fi so a cikin finafinan da ki ka yi?
BINTA ƘOFAR SORO: To gaskiya duk fim ɗin da na yi ina son shi saboda ni dai ɗin ce a cikin sa. Kuma ni na yi aktin ɗin da kai na, ina son duk finafinan da na yi.
FIM: A wanne fim ki ka fi shan wahala?
BINTA ƘOFAR SORO: Fim ɗin da na fi shan wuya ba kamar fim ɗin ‘Umarni’ da kuma ‘Waye Gaba’. Na sha wahala sosai gaskiya, domin fim ɗin ‘Waye Gaba’ har faɗuwa na yi na ji ciwo.
FIM: Wane ƙalubale ki ka taɓa fuskanta?
BINTA ƘOFAR SORO: Ƙalubale ai duk mai sana’ar fim ɗin Hausa dole ya fuskance shi. Dole su ce mana karuwai, kuma ana kiran mu da ’yan iska, duk mun ji, mun san wasu na ce mana haka. Amma mu Allah ya san mu na yi ne da zuciya ɗaya, kuma domin faɗakarwa, kuma sana’a ce da za mu nemi abinci, don ya fi a ce ana ganin mu a wani ‘guest house’, ko an gan mu a gidan wane ko motar wane, ko kuma wani wuri wanda bai dace ba, amma mu dai mun san sana’a ce mu ke yi. Amma a garin mu Katsina, da ya ke abin bai yi yawa ba, da an ga ’yar fim – in dai mace ce – to an ga karuwa! Ba ruwan su da su yi bincike.
FIM: Waɗanne nasarori ki ka samu dangane da harkar fim?
BINTA ƘOFAR SORO: Alhamdu lilahi! Maganar gaskiya a da gida na ɗaya a garin Katsina, amma yanzu ko ba komai ina da gida tara, ina da filaye da motoci na hawa da kuma na haya. Na gode wa Allah.
FIM: Ko za ki iya barin ɗiyar ki ta yi harkar fim?
BINTA ƘOFAR SORO: Ƙwarai da gaske, ina iya barin ta saboda na san sana’a ce. Ba zan hana ta ba. Wallahi idan yanzu ɗiya ta za ta yi fim zan ba ta goyon baya da gudunmawa tunda na san fim ba iskanci ba ne. Kuma a cikin ’ya’ya na ma akwai Mufida wadda ina sanya ta finafinai wasu lokutan.

FIM: Katsina jiha ce da aka fara harkar fim da wasan kwaikwayo tun da daɗewa, amma yanzu sun zama koma-baya. Menene ya jawo maku haka?
BINTA ƘOFAR SORO: Rashin haɗin kai ya jawo mana haka da kuma jin zafin junan mu da baƙin ciki da hassada da mu ke fama da shi mu ’yan Katsina.
FIM: Ko ku na da niyyar gyarawa don kawo cigaba?
BINTA ƘOFAR SORO: Ina matuƙar bakin ƙoƙari na, kuma duk masu harkar fim a Katsina sun sani. Ina yin fim da kuɗi na tunda aƙalla ba a kasara ba daga azumin bara zuwa azumin bana na yi fim za su kai shida; da kuɗi na na ke gayyato ’yan wasa daga wasu jihohin su zo Katsina su yi mani fim da kuɗi na.
FIM: Yanzu shekarar ki nawa?
BINTA ƘOFAR SORO: A yanzu haka shekaru na arba’in da huɗu a duniya.
FIM: Ko ki na da niyyar yin aure yanzu?
BINTA ƘOFAR SORO: In auri wa? An mutu an bar ni da ’ya’ya biyar marayu, ni ce cin su, ni ce shan su, kuma ni ce makarantar su, wa zai yarda ya aure ni? Ai babu mai auren ka da ’ya’ya. Ai duk wanda ya lallaɓo ya ce zai aure ni, ya zo ne don ya samu wani abu cikin dukiya ta!
FIM: Me ki ka fi tsana a wannan harka ta fim?
BINTA ƘOFAR SORO: Gaskiya abin da ya fi ci min tuwo a ƙwarya, kuma na fi tsanar shi, shi ne wasu masu fakewa da sunan cewa ’yan fim ne su je su na shaye-shaye, wasu kuma su na yin maɗigo da sunan ’yan fim. Ina jin haushin wannan abin, kuma abin da na fi tsana kenan.
FIM: Wane kira ki ke da shi ga ’yan’uwan ki ’yan fim?
BINTA ƘOFAR SORO: To, kira na gare su don Allah idan an zo wajen su su daina wulaƙanta mutane. Domin mu na samun tsegumin haka. Don Allah su dinga gaisawa da mutane, saboda shi masoyi ba a sayen shi da kuɗi, kuma idan bai san ka bai zuwa inda ka ke, kuma sana’ar mu sana’a ce mai masoya. Ya kamata mu ci gaba da haƙuri.